PAGE 4

9 0 0
                                    

🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚

   *AWANNI CASA'IN...*

🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚

         
*Short story*

*Based on borno true life story*
                     
   *By*
        
  Abdul alh musa {10k}
             And.    
  Khamal balah {no love}

_*HADUWAR KUNGIYOYIN BIYU TA ONLINE WRITER*_

*PEN WRITER'S ASSOCIATION*
      
    *AND*

*✍STRONG PEN WRITERS ASSO.🖋🖊*
    _aiki da nazari domin farin cikin makaranta(readers)_

*THE STRONGEST WEAPON'S*

*BISMILLAHLA_HILLARH MANURRAHIM*

    04


Tagumi *yusuf" yayi Abin tausayi yana tinanin shikenam yanxu yanda suka hallaka min kaka ta daya tak, danake tin k'aho da ita nima hakan ne zai faru da ni kenam?.

    *"Tsamo yayi tamkar marayan dan tsako, Abin tausayi kafadar sa Salma ta dafa ta ce, *"Yusufa"* Bamuda Wata mafita wa 'yannam mutanen Basa tsoron *"Allah"*, sannam basuda tausayi Sunacikin tadin wani *"murtuke_ken k'aton gardi ne, da bindiga a wuyan Sa yana zuwa ya nuna *"Salma"* ya ce ke ta shi muje Dora hanu akai tayi tace na banuna Ta fashe da kuka..!.
   
   
  *Kallon "Yusufa" ta yi ta ce Ba lallai na dawoba idan bandawoba karkudamu Allah na tare da ku tana hawaye tana Share kayan ta, gaba D'aya sauran Matan gurin kowacce tayi shiru bamai ko motsi, "Yusufa" ya bita da kallo har sukadai na ganin ta, tafiya suke "Salma" na biye dashi Abaya Jikin ta tayi sanyi..! wani bangare Suka iso Shiru kukan tsun_tsaye kawai kake ji  gurin, na musamman ne gune mai k'yan gaske "Salma" gani  Tayi ya tsaya ita ma ta dakata ya ce ki tsaya anam gurin Tsayawa tayi jikinta yanata b'ari..!

   A bun tausayi, jim kaɗan Suna tsaye Gogan naka yanata na muxuxai..! "Salma" Tayi shiru, "Wasu mutanene A Wata mota, jif Iso war su kenam,''Salma'' ta fara A'du'o'in ta A cikin zuciyat ta.

Bud'e k'ofa sukayi,Mutumin daya kawo *"Salma"*, Ya turota gaba Tana Tana isowa Suna Hada ido Dasu ta fadi k'asa tace Dan Allah karku chutar dani Kurabu dani, Daka Mata tsaya yayi Tayi shiru Aka mik'o masa Wata jaka cike DA kudade.

  "Kallonta yayi yace wannam bazatayi Ba A maida ita Jan motar sukayi Shikuma ya Mai do da "Salma" ta na isowa A ka maidata, "Yufufa" ne yafara zuwa kusa da ita kallon idanun ta yayi yaga sunyi jazir..! Ya yi murmushi yace Allah yayi bazasu rabamu dake Ba, tayi murmushi.

  Ta ce "Yusufah", Kenam Allah yayi da sauran numfashi na, Niyyar saida nima akayi "Yusufa" ya ce Subahanallahi..! Ta kwashe labarin Abunda ya faru ta fada musu, Washe Gari Da misalin k'arfe 12:35na Rana, Awannam lokacin mutanen Dasu ke tsare su basuda yawa sosai Har sun shiya guduwa daga Wajen Am ma abun yagagara, Sukacigaba da zama Anam Har "Salma" Da "Yusufa", sukazama sun Saba Dasu, Duk da haka basu fahimci "Yusufa" namiji bane Suna cikin wannam yanayin Wani Suka hango Da kayan kakin Soja a daure shi Jini ne kawai yake malala A fuskar sa, Dakagan shi yanada jikin jarumta, sannam yanada matsa kaicin jiki, Hanunsa Dama tsun shi a mummurde, Jefa shi akayi kan "Yusufa", Ya na motsi kadan sama_sama, juyashi Yusufa yayi, Tsumma ya samu ya Nata famar goge masa jinin fuskar Sa, Daga bisani Ya bude Idon Sa ya kalli Yusufa, Ya bude baki yace Na gode.

Mamaki ya Kama shi, Haka sukacigaba daku DA shi, har jikin sa ya war_ware cire hijabin dake jikin, *YUSUFA*, Yayi Sojannam yayi mamaki ya ce, Kai jami'in sirrine, *Yusufa* ya girgiza Kai ya ce A'a yallabai Tun dauko mudasukayi a garin (MAZARGA), nayi shigen Mata Dan na tsire daga Hanun mugayen muta nen Nam, Girgiza Kai sojan Nam yayi Ya ce yaya Sunam ka?.

Yace sunana Yusufah, yayi murmushi yace karkudamu Zan San yadda xa'a yi naga kun kubuta ahanun Azzalamunnam, Hakk'i ne daya rataya A wuya na.

  Wasu fasatattan 'yan ta'adda ne suka kamo so jannam DA k'arfin tsiya,Suka daddau re shi, Suka rufe mar fuska Suna dakan shi suna fadin Shegu K'afuran Banxa sai munga bayan Ku, Lilis suka mar Cikin Rana suka tube shi Daga shi sai Dan k'aramin Wanda.

  Shugaban sune Ya A jiye kujera Ya dauko Wata k'aramar wuka ya na tsaga wa sojannam jiki Yanata kururuwa shikuma Dariya Yake Kawai, *Salma* suna daganesa kuka kawai suke Haka aka ringa Azabtar DA shi A Rana Gayunwa Ga k'ishin ruwa.

Sakawa yayi Aka k'irawo Salma, Ta na zuwa ta durk'usa Ya ce Maganar Auren Kunnam An fasa Ba yanxuba sakamakon Rasa dakarun mu DA mukayi Dadama wajen Gwabxawa Yasa K'afa Ya k'ara nitsawa sojannam wuk'a a cinyar sa "Salma" rufe Idanun ta tayi Ta fa she dakuka Kallonta Sojannam Yayi Yace Kubani Ruwa Zan mutu.

"Ta shi Salma Tayi Ta dibo Ruwa Ta na yunk'urin Karkata Ruwa ya shi Daga nesa Wani ya taho Zai Dakatar Da ita Ido Kawai Ya masa Yadakata Ya ce Rabuda Ita Koda Tabashi Ma mutuwa zaiyi.

  Tana k'arisowa kusa DA shi Ta tallafa mar Tabashi Dan kadam Ta hanashi ya sake cewa ruwa Ta sake Bashi Ahaka harya k'oshi.

Ta kalleshi ta ce wannam wace kalar Rayuwa ce, Haka An maida mutum Bashida Wata Daraja Kashe Mu a ke Kamar Kiyashi Haba Wannam Da Mai Yayi Kama?.

  Wanine Ya taho Yayiwa Maigidan Nasu Rada a kunne Yayi Yatashi Ya Kama zazzaga wuta a sama Yanata huci, Ya ce A garin yaya hakan ta faru To zamu Rik'e wannam sojan Amatsayin Tarkon mu Idan Har suka kashe mana Namu Muma bazamu bar shi A rayeba.

Ya ta ho yasamasa bindiga ya tofa masa yawu Yace Munanam Dakai Dagayau Ba sassauci Karku Ragawa kowa Mata Guda Hudu A ka Ciro suna Kaku Yasaka Bindiga ya kashe su DA ya a yan daya Abun Tausayi Sakesu Sukayi Yace idan Sunaga Dadama Sugudu, Tattara su Akayi A kaje Aka yadda su, Abin Tausayi.

Ya ce to DA ga yau Duk Wanda yakega Zai gudu to ga hanya, Harara shi *Salma* tayi Ta girgixa Kai tana kuka ta KO ma cikin 'yan uwanta.

Gefe, Daya kuma *Yusufa" ne Ya na zaune ya na rera 'yan wa k'ok'in sa, Ya na cewa Wayyoni ! Wayyoni !! Ina zamu sakan mu duniyar Nam cike take da zalinci Allah ga mu Gare ka, Muna ta wassali da sunayen ka, Ka kawo mana dauki, Wayyoni ! Wayyoni !! Wayyoni !!!, gaba d'aya babu imani a tattare dasu, Idanun sa nata zubar Hawaye haka yaci gaba DA rero baitocin Wa'ken sa, "Salma" kuwa tayi Ta gumi, Yayi shiru yace *Salma* kidaina tagumi kiduba duk yawan munnam Ahankali Suke Kashemu Muma Ba laillai bane Mu Tsira daga Hanun mak'iya Allah DA adinin musulin Ba.

K'arar harbi sukaji Tau_Tau Har sau Uku Ji kake Kabbara na ta shi, Gayyar zaratan Samari ne Ke shigowa Sunata Rungumar Juna.

Yuk'ura sojan Nam Yayi Ya rarrafo Ya jingina Jikin Shigin Da aka tsare su Salma, Ya kalle su Yana murmushi yace Insha Allah Ankusan Zuwa Tabbas Karkuda mu kunji?.

Taruwa Sukayi Kowa fuskar su A rufe Wani Comanda ne Ya musu Huduba, Daga bisani yace Kowanne Daga cikin mu yazauna cikin shiri Tabbas Abokan k'arawan mu sunakan Haryar su ta tinkarar mu, Take gurin ya rude da kabbara, na 'yan mintoci sannam yace muntura mutanen mu guda 100 Dari amma babu Dan Aike har yanxu kowa ya zauna cikin shirin sa.

Dajin wannam batun sojannam yayi murmushi.







AWANNI CESA'INWhere stories live. Discover now