Talla!!!

1K 33 0
                                    

Ameenah (BAYAN RAI!) tace, "Allah ne Ya hadani da Marwan a cikin duniyar da ban taba tunanin zan je ba, ya kuma sake hadani da AbdulMaleek a wata duniyar da haskenta ya dusashe sauran duniyoyi!".
Nafeesah (NI DA ABOKIN BABANA!), tace "anya akwai abinda ya kai duniyar dana tsinci kaina a ciki ni da Ibraheem-Galadanchi kuwa?".
Mubassheerah (DR. SHEERAH), tace "ban taba tunanin akwai farincikin daya riski wanda na tsinci kaina a ciki ba sai dana hadu da Al-Mustapha a duniyar da ba tawa ko tashi ba! Gashi yanzu ina cikin duniyar da babu komi a cikinta face farinciki, jindadi da alfahari!".
Na'ilah (A ZATONA!) tace, "ban taba tsammanin duniyar da Bilal ya kaini tana wanzuwa ba sai dana shigeta, na tabbata ban taba ba, kuma ba zan kara shiga makamanciyarta ba!
Bahijja (WANI GIDA!), tace, "haduwata da Abbas a duniyar da bamu yi zato ba ko tsammani, wannan nasan kaddara ce da ikon Allah kawai!
Ameenah tace, "ko kun san irin duniyar da Baqeer-Lamido yake kokarin turani kuwa?!"......

Duniya ce da bata taba ganin kwatankwacinta ba. Duniya ce da mutane biyu kadai suke rayuwa a cikinta; masu kudi da talaka. Basarake da bawa. Duniyar da masu kudi da iko ke mulkarta, talaka kuma yake a karkashin takalminsu suna taka shi yadda suke so. Duniya ce da kudinka ne kadai suke tsirar da kai, duniyar da bata la'akari da uwa, d'a, uba, 'yan'uwa, ko iyaye matukar ba ka da kudi.
Yaki ne tsakanin duniyoyi biyu, inda ake gabzawa tsakanin kyawun hali da kyawun suffa, tarbiya da rashinta, kudi da rashinsu.
Wannan duniyar tsananin kishi, bakinciki, hassada da tsabar son matsayi, ya hana mazauna cikinta zama lafiya. Kowa so yake ya kai matakin da yake so ya kai ta ko wane hali, koda hakan zai karkatar dashi daga kan hanya mai kyau kuwa!!

Shin a cikin littafan da aka jero, wadannene baku karanta ba? To ku sani, wannan duk sharar fage ne akan wannan da yake tafe! Ku shigo cikin wannan duniya da baku taba ganin kamarta ba domin ganin yadda wannan fafatawa zata kasance.

__________________________________________________________

Yan'uwanta ne su, amma basu taba daukarta a matsayin haka ba. Watakila shi yasa itama bata jin su a ranta kamar yadda yakamata sauran 'yan uwa suji. Take nesa dasu tun karfinta, take gudun duk wani abu da zai zaunar dasu a karkashin inuwa daya koda na yan dakiku ne. Ta kasance a duniyarta ba tare data shiga tasu ba!.

Sai kuma ga Lamido-Baqeer ya afko cikin tata duniyar kamar daga sama! Ya kuma yi kememe, ya hanata zama a tata duniyar, ita kuma ba zata iya da duniyarshi ba, ya kenan?!!

Ga Affan Jika a gefe guda. Mutumin da tun ba tasan meye tsana ba, yake gwada mata ita. Wanda ya tsaneta da abinda duniyarta take dashi. Shin dama bakin daya furta tsana, zai iya dawowa ya furta so daga baya?!!! Ba zata iya yarda da hakan ba...

Duk wadanan kananun alhaki ne akan guguwar data tunkarota mai suna Fauziyya Hilaludden Jika!! Bata taba ganin zallar tsabar kiyayya da tsana a tattare da wani mahaluki ba kamar yadda taga wadda Fauza take mata. Me ta mata? Kawai don Allah bai kaddaro kasancewarta a cikin duniyarsu ba? Ko kuwa don mutumin da take kira nata tun yarinta ya ki ta, ya kuma kaurace mata saboda ita, (Ameenar)? Shin ita bata san kaddarar Allah bane? Ko kuwa bata san cewa soyayya ba'a yi mata shigar sauri ba? Ta manta cewa ba'a tursasa namiji ne? Namiji ma kamar Baqeer AbdulKareem Turawa??!

Wani irin selfless mutum ne shi, da kafin ya duba kanshi sau daya ya duba halin da wadanda suke kewaye dashi suke ciki sau goma. Bai taba dora bukatunshi akan na wasu ba, sai dai ya dora na wasu akan nashi.. Sai dai sau daya, just once in his life, ya nuna son kan, he just want to be selfish! Amma hakan ya zamar mishi jan aiki. Duk saboda me? Kawai saboda duniyarsu shi da cikar burinshi ta bambanta!!!

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

"Baka ganine? Duniyata da taka ba daya bace... Ni da kai kamar misalin dare da rana ne, ba zamu taba zama a waje daya ba! Dole idan yini yazo dare ya tafi!!". Ta fada mishi cikin sanyin jiki da sarewar gwiwa.

Yayinda ya tare ta da karfin gwiwarshi, "Dare da rana suna haduwa waje daya Ameenah, baki taba ganin faduwar rana bane? Muma kamar su, zamu iya haduwa waje daya mu rayu, mu bada haske da kala masu kyau da zasu dauki hankalin duk wani wanda zai kallemu!!!"

■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■


Labarin DUNIYA BIYU zai fara zo muku a ranar litinin, uku ga watan agusta 3/8/2020 akan naira dari uku kacal! (300).

Zaku tura kudin ta 0002862363
Hauwa'u Shafi'u Lawal
Jaiz Bank

Sai ku tura shaidar biyan ta lambobin wayar dake kasa,

Domin neman karin bayani, ko kuma tura katin waya, sai a tuntubi
09030312094, ko kuma,
07038687240

Me zaku jira? Maza ku garzaya, kada ku bari a baku labari!!!!!

DUNIYA BIYU!!! Where stories live. Discover now