07

191 18 0
                                    

❄️❄️ *DUNIYA BIYU!!*❄️❄️

©Jeedderh Lawals

Free page 7

Tun a ranar talata din aka fara gudanar da shagulgulan biki.
Bayan sun gama hada kayan, an zuba su a mota an tafi wajen walima, suka wuce can bangaren masu aiki ita da Indo suka kimtsa jikinsu. Gidan shiru, duk an tafi wajen walima sai yan daidaikun mutane wanda yawanci duk yara ne.

Can kurya dakin Anty Mommy inda ita da abokanta suke ta yiwa tsinke. Daga Anty Mommyn har abokanta su hudu dake cikin dakin, sun sha ankon wata bugaggiyar shaddar getzner, kai daga ganin yadda take ta zuba sheki babu tambaya kasan cewa ba karama bace ba.

Duk suka katse hirar da suke yi lokacin data shiga dakin suna kallonta. Ta durkusa ta gaida su, duk suka amsa mata, Anty Mommy tace "ashe fa kun zo, Jenny take fada min zuwanku, hidimar baki yasa na manta in leko ku".

Ameenah ta kada kai tace "ai babu komi. Ya hidima da taro? Allah Ya tabbatar da alkhairi".
Tace "ameen. Ya har yanzu baku tafi wajen walimar ba?".

Tace "ai mun baro kayan da zamu sanya a gida saboda bamu yi zaton zamu jima ba, gashi kuma yamma ta fara yi".

Wata daga cikin kawayen Anty Mommy din tace "zancen banza kenan! Yo me zaki canza a haka? Ku kama hanya kawai ku tafi don a haka ma kinyi kyau abinki, ki dan samu kwalli da janbaki kawai ki zizara, nan zaki ga kin fito fes abinki!".

Wata ma tace "ehh, ku shirya kawai. Dama yanzu Eeshey zata dawo ta dauki jakarta data manta, kin ga sai ku tafi kawai!".

Tana shirin ta daga baki ta musa, don ita har ga Allah bata yi niyar zuwa wajen walimar ba, Anty Mommy ta kada baki tace "to kinji, sai ki kama hanya. Ku jirata a nan bakin kofa don kada tazo tayi ta nemanku".
Koda zata sake yin korafi, bata ga fuskar yi ba, dole ta tashi ta fita daga dakin.

Kofar dakin na rufewa bayan fitarta, Anty Mommy ta juya tana jefawa kawarta Hajiya Salamatu harara, "yanzu don Allah aminiya wannan wane irin zubar da aji ne kika min a gaban yarinyar nan? Don ki jawo mana raini, har ki wani dinga cewa tayi kyau a haka? Gaskiya ni fa bana son haka!".

Sauran abokan nata suka sanya dariya har da sakin ihu. Hajiya Salamatu tace "ke fa matsalata dake kenan, shegen kyashin tsiya. Yabon wani ma ba za ayi a gabanki a zauna lafiya ba? Naga ai ita din kamar ta gida ce, tunda ga kamanninta nan da na Badi har ma da Affan sun fita sosai".

Tace "to daga ganin kamanni sai ki dauketa a matsayin diyata ko me? Sanin kanki ne ba kowa ya kan zama dan gida ba sai wanda ya isa!".
Nan ma suka kara sakin wata shewar har da masu shan hannu.

Sai da suka lafa sannan Hajiya Salamatu tace, "amma fa ni maganar gaskiya yarinyar nan ta burge ni da kuma yanayin tarbiyarta, a yanzu da yarintarta da komi ma tayi halin manya ina ga ta girma? Kinga Abdul yana makaranta yanzu amma ya kusan gamawa, da ba don ba ai da nace ina mishi kamu!".

Anty Mommy ta yamutsa fuska, "don Allah ki jiki da wata irin magana marar dadin ji! Yanzu don Allah don annabi me kika gani a jikin yarinyar wannan? Fari da hancin ne suka rude ki hala? Idan ma su dinne ina ce ga Fauza nan? Me zata gwadawa Fauza bayan shi? A hakan ma bani da shakka ko hau fi akan na kanti ne wallahi. Don haka ki ma ajiye maganar nan a gefe, idan an gama wannan bikin amarya ta tare, zan zo in same ki kawata. Yo gida bai koshi ba an kaiwa na waje?! Ga auta ta nan, son kowa kin wanda ya rasa?".

Hajiya Laila ta gyada kai a hakimce, mace ce mai shegen dagawa da fankama, tace "wallahi zancenki dutse Hajiyata. Gwanda ma dai ayi-ayi, mu zo mu kara shan wani bikin!".
Aikuwa me zasu yi idan ba kara daukar wata shewa da guda ba??.

*

Suna tsaye a bakin kofa ita da Indo da wata yar aiki Juma, wata matashiyar budurwa ta fito daga gidan cikin ankon da za'a sanya na wajen walima. Atamfa ce English, fara wadda aka yi zanen circles ruwan kasa mai cizawa, tayi dinkin riga da zani wadanda suka bi shape din jikinta sosai. Tayi nadin dankwalinta mai burgewa, ta dora gyale ruwan zuma akan kafadarta wanda ta danne da jakarta vincci mai tsayin hannu ita kuma fara. Yanayinta yafi kama da sa'ar Fauza amma ba Badi ba duk da cewa daga gani ta girmi su Ameenatu din.

DUNIYA BIYU!!! Donde viven las historias. Descúbrelo ahora