03

267 23 0
                                    

❄️❄️ *DUNIYA BIYU!!*❄️❄️

©Jeedderh Lawals

Free page 3

BAYAN SHEKARU BIYU!

"Anty Mommy, don Allah, don Annabi, ki taimaka mana!. Yau tun da safe aka ce za'a kore mu daga asibiti idan bamu biya kuɗin magani da na gado ba, bamu da yadda zamu yi. Ki rufa mana asiri don Girman Allah!!".

Ameenatu a rikice take, yadda ta baro jikin Yayarta Murjanatu, a gadon asibiti a kwance, kamar ba zata rayu ba, ya matuƙar gigitata. Wataƙila dalilin daya sanya kenan ta tsinci kanta duƙe, a gaban wadda taci alwashin ko zata mutu, ba zata taɓa roƙar wani abu a wajenta ba. Ko kuwa tsabar ƙagauta ne da neman mataimaki da rashin sanin abin yi?.

Hajiya Uwani da take hakimce akan wata kujera ta alfarma, a cikin haɗaɗɗen falonta wanda yafi kama da na wata hamshaƙiyar matar gwamna, ko ma ta shugaban ƙasa. Kodayake, a halin da ake ciki mijinta neman kujerar sanata yake yi, don haka babu mamaki idan aka haɗa gidan dana hamshaƙan mutane.

Duk da halin da take ciki, hakan bai hanata jinjina kai cikin tu'ajjibi ba. Gidan ya canza matuƙa daga yanda ta sani, a ƙarshen zuwan da tayi, haɗuwa da faɗin gidan bata kai haka ba, duk kuwa da cewa ko a wancan lokacin samun haɗuwa da tsaruwar gida irin wannan abu ne mai wahala. Balle a yanzu. Shekaru uku kenan rabon data taka ƙafarta cikin gidan, sai kuwa wannan satin daya kama. Shekaru uku kwanaki ne masu yawa. Abubuwa canzawa suke yi. Mutane canzawa suke yi. Haka zalika gidaje da garuruwa ke canzawa.

Murya cike da ƙasaita tace, "me kuma ake buƙata ne yanzu? Ba jiya muka je aka biya kuɗin maganin ba?".

Ta girgiza kai a hankali, murya a can ƙasa, cike da saddakarwa, tace "waɗannan ai kuɗin waɗancan magungunan aka biya dasu. Kuma za'a mata awon ciki, sannan...".

Bata kai ga ƙarasawa ba ta katseta, "to naji. Anjima zan zo asibitin in gani".
Tace "amma Anty Mommy...!".

Zuwa yanzu ƴar fara'ar da take ƙaƙalowa ta yaƙe ta kau daga kan fuskarta. Cikin alamun faɗa-faɗa da nuna gajiyawa tace, "wai ba na faɗa miki kije zan zo bane? Haba don Allah don Annabi! Wai da wanne ake so mutum yaji ne a wannan duniyar? Da hidimar iyalinshi ko ta wasu? Nace zan zo, tunda na faɗi haka da bakina ba sai a kyaleni ba kuma? Haba!".

Jikinta ya riga ya gama bata babu alamun cin nasara a nan, hankalinta ya kasu kashi-kashi, tunanin yadda zata yi. Cikin ɗaukewar hankali ta gyaɗa kai, babu amfanin ci gaba da magiya da roƙo a kunnen da basu shiga.
Tace "to Anty Mommy, mun gode, Allah ya ƙara girma".
Bata kara cewa komi ba, ta kakkaɓe zaninta ta tashi.

Wani irin dumm! take ji a cikin kanta, wata irin amsa kuwwa mai ɗimauta mutum. Damuwa ce, tunani ne, fargaba ce, tsoro ne, babu kalar abinda bata ji a lokacin.

A cikin wannan halin ta fita daga babban falon nasu inda ta wuce ta garejin motoci wajen da suke ajiye motocinsu. A ƙalla motoci sun kai guda biyar, manya na alfarma, ajiye a wajen, wasu ma a cikin tamfal alamun an jima ba'a taɓa su ba. Sai dai hankalinta ko kaɗan baya kan su, gabaɗaya hankalinta yana kan Yayarta dake kwance akan gadon asibiti. Tunanin yadda zata yi ta ceto ta daga agar mutuwa take yi.

Sati biyu kenan da aka kwantar da ita a gadon asibiti. Matsananciyar cutar gyambon ciki (chronic ulcer) ne ya kwantar da ita. Daga farko asibitin gwamnati aka kaita. Bayan sunyi iyakar bakin ƙoƙarinsu, suka faɗa musu abin yafi ƙarfinsu, suka haɗa su da wani likita a asibitin kuɗi, suka koma can. Abin ya ɗan lafa, sai dai tsananin tsadar magunguna da gado, abin yafi ƙarfinsu. Tun suna kame-kame da sayar da ɗan abinda ya rage musu, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci komi ya tafi. Ƴar sana'ar da take yi, ta haɗe kan jarin gabaɗaya ana sayen magunguna, suma suka tafi.
Waɗanda suke tunanin zasu taimaka musu kuma, sun ƙi kawo musu agajin daya kamata.

DUNIYA BIYU!!! Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt