09

217 14 0
                                    

❄️❄️ *DUNIYA BIYU!!*❄️❄️

©Jeedderh Lawals

Free page 9


Ranar da aka ɗauki azumi na sha tara, su Ameerah suka dira a Katsinar kamar daga sama, don babu wanda yasan da zancen zuwan nasu.

Saukar safe suka yi, wajajen ƙarfe goma sha ɗaya na safe.
Lokacin Ameenatu ta bararraje, tayi dai-daya a tsakar ɗaki da biredi da kofin shayi a gabanta don bata yin azumi. Tun da safiyar ranar ta waye sai lokacin ta zauna.
Suna tashi ta ɗauki geron da aka jiƙa jiya da dare, ta wanke ta kai niƙa. Tana dawowa kuma ta tace, ta kai store ta ajiye. Shine fa ta ɗora ruwa ta haɗa shayi, ta ɗauki guntun biredi da suka yi saura jiya da dare ita da Huwaila zata ci.

Tana fara ci, aka buɗe kofar ɗakin aka shigo.
Kwata-kwata bata kawo komi a ranta ba. Kafin ta tantance, sai jin sallamar namiji tayi a bakin ɗaki.
Sai data amsa, sannan ta tuna halin da take ciki a lokacin. Ta ɗaga kai da sauri ta kalli bakin ƙofa; Ameerah ce a tsaye tana kallonta tana murmushi. Daga bayanta kuma Yaya Baqeer ne. Suka haɗa ido.

Subhanallahi! Wata irin rikicewa da kunya suka kamata a lokaci guda! Tsabar kiɗimewa sai ta miƙe tsaye, tayi duru-duru, daga ƙarshe dai ta ɗaga ƙafa ta shige banɗaki a sukwane. Tana jiyo sautin dariyar da Ameerah ta dinga ƙyaƙyatawa.

Tana jiyo muryarshi da Hajja suna gaisawa, Hajja data rasa ina-taka-saka, ina-taka-tsare dashi, sai nan-nan take dashi tana jan shi da hira, tashin muryarsu kawai kake ji.
Nan da nan ta kirawo Huwaila, ta bata makullin ɗakin da suka saba sauka, ta umarceta da taje ta gyara, don ma dai lokaci zuwa lokaci ana gyara shi musamman ma saboda baƙin bazata.
Sai da suka jima suna hirar, har Huwaila ta dawo da makullin ɗakin ta ƙarɓi turaren ƙamshi taje ta kunna, sannan ya bar dakin.
Sai daya tafi sannan Ameerah taje tana buga mata ƙofar banɗakin, tace "ai sai ki fito tunda ya tafi".
Sai lokacin ta fita daga banɗakin tana sunne fuska, Ameerah kam na mata dariya.

Ta zauna a gefen gado, gabaɗaya sai taji shayin ma ta ƙoshi dashi. Ameerah ta yaye gyalenta ta jefa kan gado, ta kalleta tana ɗan murmushin tsokana, "har kin ƙoshi da abincin ne kuma?".

Ta kalleta ba tare data ce wani abu ba. Ameerah ta zauna ta ɗauki kofin ta kai baki ta kurɓa, ta ɗan yamutse fuska, Hajja da Ameentu suka bita da kallo baki a ɗage. Tace, "ya ma fara hucewa dai, haka nan zanyi maneji don dama yunwa nake ji, ban karya ba!".

Tayi saurin dira daga kan gadon ta warce biredin dake hannunta, tace "saboda kin fini zane a damtsen hannu ko? Wato ni yunwa ta kashe ni kenan?".

Ameerahr tayi dariya tace, "to ai naga kamar ba ci kike so kiyi bane. Kin wani koma gefe kina sunne kai wai ke nan kunya, a kanki farau?".

Harara ta watsa mata ƙasa-ƙasa cikin wasa, ta raba biredin gida biyu ta miƙa mata rabi, babu musu Ameerahr ta amsa suka fara ci.
Cikin dan kankanin lokaci suka tada shi, Ameerah taja jakar hannunta ta zuge ta ciro apple guda biyu ta mikawa Ameenah daya suka kara da ita. Kafin kuma suka hau hirar yaushe gamo.

Zuwa can da rana, suna shirye-shiryen haɗa abuwuwan kari, ta shiga ɗakin Hajja ta sameta a zaune tana gyaran shinkafar tuwo. A waje ta baro Huwaila da Ameerah suna gyaran waken da za ayi alale anjima da yamma.
Tace, "Hajja tun yanzu za'a kai niƙan waken ko a bari sai anjima?".

Hajja ta ɗaga kai ta kalleta, tace "ai zancen alale ya kau, tuwon shinkafa za'a tuƙa!".
Ta kalleta da mamaki. Hajjar tafi kwana uku tana musu ƙorafin alale take so ta ci, sai yanzu kuma da za ayi zata dawo tace ba zata ci ba?. Tace, "saboda me? Ba kya jin daɗi ne ko wani abu?".

Tace "lafiyata garau. Babban maigida yana gida ina ni ina cin wata alale yau? Tuwon shinkafa za'a tuƙa mishi da miyar alayyafo. Zo kije gidan Maman Imam ki sayo mana kayan miya da alayyafo. Ki dawo ki kira min Isiya yazo yaje bakin kasuwa ya sayo min naman miya da ɗanyen kifi".

DUNIYA BIYU!!! Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang