Chapter 22

735 54 8
                                    

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by  Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story

CHAPTER 22

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
"Akwai wata budurwa a wani kauye mai suna Kurya. Kauyen ya sami sunan ne dalilin wani shahararren kasurgumin barawo da ke da wannan suna, don kwarjininsa da tambaya har masu kada masa take ke gare shi, in zai je wurin fashi." Shuru wurin yayi ba abinda suke saurare face labarin da Sarah ta fara basu. Tun da rana ta fadi, Jinah da Nafisa ke ta rokonta akan ta basu labari kamar wasu kananan yara. Allah yayi masu son jin labarai, ba kamar Nafisa da ba zata iya ganin littafi bata karantashi ba, har ma tafi karfi a na tatsuniyoyi irin su na Shehu Jaha, Magana jari da makamantansu.

Daga karshe dai sun shawo kan Sarah har ta amince zata basu amma sai bayan anci abincin dare. Bayan an kammala komai, babbar tabarma suka shimfida a tsakar gida, kowa ya zauna banda Dauda da kowa yake tunanin ya tafi kauyensu tun kafin farfadowar Jinah sakamakon wata wasika da ya aje masu.
Sarah ta cigaba da labarinta :
-A tsakanin Kurya da wani kauye Tafi-da-Kwarinka akwai wani surkukin daji, to a wannan dajin Kurya ke zuwa ya tare duk wani mai wucewa ta nan ya yi masa fashi. Kurya dai katon gaske ne, gabjeje, baki-kirin kamar gawayi, da gashin baki, da jajayen idanuwa, ga shi da kwarjini da komai karfin halinka da jarumtarka in kun yi arba sai gabanka ya fadi.
To, wayewar gari duk sai ka ji an ce ya yi fashi, kuma ya kan zo da jakkai ne ya labta masu kayan da ya yi fashin, ya kora ya tafi cikin dokar daji inda ya kafa bukkokinsa, ya yi dangar kara ya kewaye ya jibge su a nan, kuma ya yi runbuna da ya kan zuba hakoran mutanen da ya kashe, watau ko mutum nawa ya kashe a ranar sai ya bi su da dai-dai ya cire hakori guda na kowanne ya kai rumbu ya jefa, da haka sai da ya yi rumbu guda guda cike da hakoran mutane. Wannan mutum sai ya zama abin hirji da neman tsari a wurin matafiya; kai ta kai intaha dai ya kashe hanyar, in kaga wani ya biyo, to bako ne cikin rashin sani.
Ana cikin wannan halin ne, sai mutanen da ke kauyukan, nan biyu suka rinka kaura, sai dagatan kauyukan byu abin ya dame su, don sun ga mutanensu sun kusa kauracewa su bar kauyukan, sai su ka hadu suka yi shawara, suka zartar da cewar, kada kowa ya yi tafiya, sai cikin ayari dauke da makamai, tun da sarkin yawa dai ya fi sarkin karfi, ko Kurya zai bullo dai, sa gabza da shi, kuma suka ce duk wanda ya yi dalilin Kurya ya zo hannu za'a bashi lada mai-yawa, kuma a dauke ma sa biyan haraji, in kuma mace ce, to mijinta ko iyayenta sun huta da biyan kudin kasa muddin ransu.
Wata rana sai samarin wannan kauyen suka tafi yawon tsarince a Tafi-da-kwarinka, sai wani saurayi daga cikin samarin ya sami wata budurwa a kauyen, akawala kyakkyawa, sai ya ce, yana sonta, sai ta ce, ita ma tana sonsa, ya tambayeta sunanta, ta ce masa sunata Ayashe, ta tambayeshi nashi sunan, ya ce mata Mazgau. Ayashe ta yi dariya, ta ce, wannan suna naka bai dace da kai ba, don ga alama dai sunan ya cancanta da masu karfi ne, to, amma kamar nan taka, wa za ka iya mazgewa? Hala dai sunan kakanni ne wannan. Mazgau ya amsa mata ya ce, "I" na yarda, tunda an ce alamar karfi tana ga mai kiba, toamma ba a dukkan lokaci ba, wani sai ki gan shi, ki raina, amma in wuri ya yi wuri sai ya baki mamaki, ya yi maki ba zata." Mazgau ya yi sallama da budurwarsa, ya tambayeta randa za ta zo kauyensu Kurya, ta ce masa za ta rinka zuwa a duk ran kasuwar kauyensu, don cin kasuwa, in ta kwana ta ci kasuwar, ta juyo, suka yi sallama ya tafi.
Ayashe ta rike alkawarin da ta yi masa, a duk ranar kasuwar kauyensu Mazgau, sai ta je masa tsarince, to a duk lokacin da ta je, in suna tadi na hirar saurayi da budurwa, sai ta kan ce masa, Shin me ya sa ne kai baka cika zuwa kauyenmu ba, sai ni ke zuwa naku, ko don barawon nan ne dan fashi da ke tare mutane? Mazgau ya amsa mata cikin ruba ya ce, "Shi din me, ya ma isa, ji kika yi an ce maza mata ne? Ayashe ta yi murmushi ta ce masa, haba ai ko a matan ma suna kadai suka tara, amma ai akwai munam mata, akwai mataye, akwai kuma mata, kai har ma da mateku. Ashe baka da labarin wata matar ta f namiji jarunta ba ? Don kuwa ta kowace hanya ya bi, ta damashi ta shanye a nan, sai Mazgau ya ce don Allah rufe mana baki, namijin banza ba ? In dai ban da baki, da me mata suka fi maza ? Ayashe takan ce to a bar wa ranar gwaji wann sani, sai randa ta zo.
Ayashe ta ci gaba da zuwa tsarance wurin Mazgau, har dai ta gaji, shi da rana daya bai taba zuwa mata can kauyen nasu ba, tun dai daga ranar da suka sadu, ashe dai shi a ransa tsoron gamuwa da dan-fashin nan ya ke yi, kuri ne kawai ya ke yi wa Ayashe ta ce masa, ko Kurya ke hana shi zuwa kauyensu ganinta.
To, ana haka, har sai Ayashe ta soma shan jinin jikinta ta ce, ko baya sonta ne, shi ya sa baya zuwa, rannan data je sai ta sake tambayarsa dalilin da ke hana shi zuwa, sai ya kawo mata wadansu dalilai marasa karfi ya ce, su ne suka hana masa samun sukunin zuwa, daga nan sai Ayashe ta ce, haba Mazgau, ku maza dai kun raina hankalin mata, alhali kuwa ba ku san bakan mukan yi maku ba, don mu ga iya gudun ruwanku, kai dai kawai matsoraci ne, Kurya ke hana maka zuwa kauyenmu, ni kuwa in fada maka yau, ni fa ba matar matsoraci ce ba, daga yau in baka je ba, ni ma na daina zuwa maka. Mazgau ya murtuke fuska, ya ce haba ki dubi duk tuli na ki ce da ni matsoraci ? Yo, duk duniya akwai wanda nike tsoro, in barnda wanda ya haliccemu.
To, yau in za ki koma har gida zan kai ki, in kuma dawo komai dare, kuma ta nan wajen sarkakiyar itatuwan kukkokin, inda yake labewa, ta nan za mu bi mu shige. Ayashe ta ce masa, to, in dai kai namiji ne sosai, sai ka bari sai dare ya yi tsaka, kana mu bi, mu tafi...

 JINAH (Matar Aljani)Onde histórias criam vida. Descubra agora