Page 1-2

1K 23 1
                                    

*🎍🎪🎍(WANI SALO*)🎍🎪🎍

   ~------------------------------~

*Written-by*✍🏻
                ~*Sa'adatu alkali D/tsafe*~
          
*(1-2)*...tafe suke ahanya yayin da hadari naqoqarin tasowa 'yan mata ne su ukku sanyi da wata atamfa dik eri daya mayafi ne kowa da kalar nasa saka makon color uku ne keda atamfar  da alama daga biki suke  sauri suke sonyi su isa gida kafin hadarin dake hadowa yazubar da ruwa amma hakan yakasa samu wa sabida iskan dayayi yawa  ga zee ita kuma kokadan bata iya saurin tafiya bata ma san yanda zatayi shi ba tako take tamkar maijin tausayi qasa karka yi zaton hadarin bai daga mata hankali ba tama fisu tsoron ruwa saboda baya bata lpy dayar mai suna raliya kecewa zee dan allah dik yanda xa ayi kicira qafa muyi sauri mu isa gida kinfasan idan ruwan nan yasauka kece aciki dayar mai suna fatima ce tace haba raliya kinfasan ba laifinta bane haka halitta ta take kinfasan lkcn damuna yara zee tasha duka sosai agun maman ta idan ta ayketa tadade bata dawo ba sai daga baya tagane ba ason ranta take dadewa idan ta ayketa ba tafiya dasuri ne bata iyaba..mafita kawai musamu gidan da zamu fake kafin agama ruwa raliya tace wannan ba shawara bace dan bamusan sanda za a gamawa ba kawai muyi addu'a allah yakawo mana mai napep kafin ruwan nan ya sauka" dik maganr dasuke zee najinsu batace musu uffan ba wanda sukuma hakan bai dame su ba tinda sun saba da  halinta wataran in abin yamotsa dik yanda sukaso tayi mgn batayi komy tsokanar dazasu mata idan ko ta tashi surutun ta bazaka ce ita bace haka suke tare tin suna yara cikin ikon allah saiga my napep sun samu kuma sunyi sa a b kowa sukayi saurin tsayar dashi basuko tsaya tmbyar sa nawa zai kaisu ba suka fada gunda zaikasu kawai suka fada mishi haka yasauke su unguwar su suka biyashi kudin sa dayake gidan su raliya na kallon gidan su zee gidan su fatima ne sai kawuce gida biyu kafin kakai gidan  haka sukayi sallama da juna kowa yanufe gida isarsu gida kenan iska yataso sosai saiga ruwa Alhamdulillahi matar dake tsaye a cikin kiching tafura ta lkcn d zainab tayi sallama tashigo gida' zainab meya tsaidaku harkuka bari hadari yahadu haka kinkoma san ruwa sam baya baki lpy? zee tace wllh mama abun hawane yayi wuya aqafa ma muka fara takowa sai da mukayi tfy mai nisa sannan muka samu my napep yakawo mu..tohm ay shikena mungode allah tinda andawo lpy baban ki ma nakeji karya dawo baki nan kin kuma san sarai da surutun khalid baban ku na dawowa zai tmbaye sa ina kike ...tace wllh kuwa mama ai naji dadi dana rigasa dawowa  ina Khalid din halan? tace yanacan daki  home work yake zainab tace shiyasa naji shiru mama bari naqarasa daki nacire kayan nan nayi sallah tace toh.. dakin gama kifito kici abinci dan nasan halinki.  tace ay mama yanxu xanfito naci kar yaya yaqi sayamin waya su fateema dikan su sinada nice kawai"tohm ay yanzu kema zakiyi ko?tin da kingama karatu yayanki kuma yamiki alkawari.. tace hakane Mamana......

official,sa'adat alkali🍬:

-dankararun motoci nahango masu matuqar kyau d girma kokadan baka ganin mutanin dake ciki- motace dai-dai har guda 10 sai budaddin motoce goda hudu danqare da kayan abinci da sutura da kayan amfani ke biye da hadaddun motocin- tafiya suke ahankali tamkar man dake cikin motocin zai qare" dandazon mutane ne tsatsaye motoci dayawa sun parka domin bawa motocin daman wucewa hannu mutane ke tadagawa alamar gaisuwa da jinjina kowa ka kallah fuskarshi kunshi d murmushi kowa nafadin albarkacin bakin sa da alamun yabo suke da wa'anda ke cikin motocin (niko nace sowaye wannan dake cikin motoci idan dai ba shugaban qasa ba toh sarki ne ko wani babban mutun amma dai bari nabisu naga suwaye anci gani🙄 yakori 👂🏻) qaton wani get aka bude yayinda na tsinkayo mutane kinjim aciki da alama jiran bakin ake guri suka samu sukayi parking sannan mutanin dake cikin motocin suka fara fitowa d sauri daga ganin.shigar su zakasan bodyguards ne wata rantsetseyar mota sukawa qawanya but..basu bude ba saida aka kwashe kusan 15: mnt sannan akayi knocking din glass sukayi saurin budewa konan sayda akafi 5:mint sannan aka sako kafa daya waje amma ba a fitoh ba..kai🤦🏻‍♀ gsky jan ajin yayi yawa wai wanene wannan???

~.......~ kafarsa daya yakoma saukar wa kafin mamallakin yafito...tirqashi😳 ido na murza nakoma saukar da idona akan kafafun sa dumin tabbatar wa kai na wannan mutune kuwa  tsalelin saurayi ne idona yasauka akan sa wanda fadar kyansa 6ata muku lkc ne mai karatu dik yanda zan kwatan ta muku kynsa yazar ce hakan nikai na dana gansa😜 nadauka akasar India ne nake ko larabawa bazaka ta6a cewa bahaushe bane cikakki allah yayi halitta anan saurayin bazai wuce 30 years ba farine sosai erin farin nan my sirki d yellow eye brow dinshi bakine sosai da cikar gashi tamkar an mishi gyaran ta idanunshi dauke suke da eye lashes dasuka masu rumfa gwani kyau da tsari pink lips dinshi tamkar yashafa janbaki multi billonaire man *......Emran yusuf usman* kenan matashin mutun maiji da kyau da kudi da izza )

  *** *Waye Emran?* ***

Emaran dane da wani shaharrin mai kudi Alhaji yusuf usman bafulata nine dan adamawa mutun ne da allah yabawa dukiya dakoshi bazai iya qiyasta ta ba allah yayi shi mutun ne  nagari mai tsoron allah mai kyauta da taimakon wanda bashi da shi yanada mata daya Hajiya amina wacce takasan ce  shuwace macice my kyau da kamala da dattako tanada kirki sosai tamkar mijin ta itama akwai ta. da taimakon jama'a musamman talaka suna zaune agarin abuja a unguwar maitama.. sunada yara hudu mata 2 maza 2 aunty hajara ce babba sannan emran.sai khaleefah.sannan auta afrah suntaso cikin tarbiya da son junan su idan kadebe emran kokadan baya sakarwa qannin sa fuska ko auty hajara dake yayar shi baya kulata dik yanda take tsokanar shi emran miskili ne na bugawa a mujallah bayason raini kokadan yanada wuya kaji mgnr sa idan bada mamyn sa ba sai friend dinshi kasim koshi basosai yake kulasa ba eyayin shi namatuqar ji dashi tamkar shi kadai ne dansu dik da haka kuma basa nuna banbaci tsakanin 'ya'yan su shi yake taimakawa mahaifin sa da harko kinsa emarn nada son taimako tin yana qarami da girmama wanda ke gaba da shi  saboda gwargwadon ilimi da tarbiya eyayin su sun basu tako wani 6angare auty hajara tayi aure anan cikin abuja tanada yara biyu twins dik mata.. gashi emaran yadoshi shekara kusan 30 amma kokadan baya zancin ko budurwa bare yayi tinanin aure aranshi gashi khasim na shiriye2 aure amma shi kokadan abin bai dame shi sai yace har yanzu baiga matar dayake so ba kuma bazai ma ganta ba 'yan mata da yawa na masifar sonsa ta 6angari da dama dangi harma da bare amma ko kallo basu isheshi ba mamyn sa tayita fada har tagaji shi gaba daya bayako son ana masa zancin mace bare mgnr aure ranshi yakejin yamatuqar 6aci..emran yayi suna sosai ba afadin Nigeria ba harma da qasashe da dama saboda taimakon sa da arzikin da allah yamusu..kwanci yake da alama wani aiki yake mai muhimman ci acikin laptop dinshi .iPhone 7* ce" gefin shi ke ringing screen din wayarshi ya duba yaga kasim ne bai daga ba sai da yayi mishi kusan 5 miss call sannan ya dauka koshi syda yakusan tsinke wa kafin yadauka baiyi maganaba saida kasim yace maihali baya canja halinsa shiyasa nake addu'a allah yakawo wacce zata canzaka dik ajinnan da miskilancin nan tafitar dashi akanka kitt...kasim yaji yakashe waya murmushi yayi yace emran manya wllh insha allah sai kazo hannu text yatura mishi dan yasan idan zai kwana yana kiran sa bazai dauka ba..{'''gani a zariya fa gidan marayun nan danake gayama na buqatar taimako nasanar dasu zakazo gobe sunyi farin ciki sosy yanxu haka sunyi sanrwa zuwan ka dan allah kadaure kaxo dik da nasan kai mutun ne mai alkawari jinjina ga emran yusuf usman abokina nakai na mijin maci hudu insha allah Lol..😜'''} kasim bayajin dadi kokadan idan by tsokali emran ba😄 yatura mishi kafin yace emran manya kukayi ba  a fadi.."

WANI SALOWhere stories live. Discover now