*🎍🎪🎍(WANI SALO)🎍🎪🎍*
~-------------------------------------~
*Written-by✍🏻*
*Sa'adat alkali D/tsafe*{{ _wannan shafin na sadaukar dashi ga duk wani masoyin_ *🎪WANI SALO*🎍}}
~________________________~*(11-12)*...mutuwar zaune kasim yayi, yayin jin furucin zee da yanda take magana babu ko dar" a idanun ta,,iyakar gskyr ta take mgn sosai tabashi mamaki wani gefin kuma ba qaramin burge shi tayi ba...yanda ta tsaya tafadi iya son ranta kuma ga dukkan alama ita ba 'yar kowa bace amma hakan ta tsaya tayi qoqarin fadawa tsadaddin mutun kamar emran mgn mai matuqar fizgar jiki, gsky wannan yarinyar ta da bance…
wai wayowa kasim yayi, yawa emran magna,, ya daga mishi hannu alamar bai son jin komy, idonshi kadai idan ka kallah zakasan cewa,ran maza a6aci yake,basu ko tsaya, biyawa takan gidan su, aysha ba kasim yacewa Drievr su wuce masauki kawai… _daya daga cikin gidajin emran dake cikin garin zariya_ haka motocin suka jera suka fice daga unguwar batare da sunje inda zasu tafi ba, sake wai wayar sa kasim yayi, yaga yanda zufa keta tsatsafowa akan fuskar emran, dik da ko erin sanyin, AC.. dake ratsawa acikin motar, hannu yasa yaqara sanyin..AC wai koda emran zaiji sauqin zufan dake fita ajikin sa, yana mamakin emran yanda lokaci guda yake erin wannan zufan, dik da yasan hakan bai rasa nasaba da abuda yarinyar nan tafada mishi" randa yake da emran bai ta6a ganin sa cikin 6acin rai ba erin yau.. da wannan tunanin na kasim suka iso masauki..
Khaleed! Khaeed!! Khaaaaaleed!!!= wai kana inane? aguje yarugo da gudu ya iso gaban ta yana haki' saboda tsorata dayayi da kiran da auntyn sa ke masa, aunty lpy? ya tabye ta, tace ina mama? yace taje gidan su anwar,mamar sa ce akace ta haihu, kai kadai ne kenan agida? kana inane naketa kiran ka kaman shiru wllh aunty ina ban daki zanyi wanka, koda kika kirani, ok' toh je kagama kashir ya kazo na aike ka gidan su aysha, tana fada tana cire mayafin ta, tare da cewa,kash" wllh duk nagaji, aunty ina kikaje halan? zakaje kayi abinda nace kazo in aike ko yaya? zakazo katsare ni da tambaya sai kace aike na kayi,,afuwan" my aunty bari naje nayi sauri na fito"tace daya yafima ,,
kiching ta nufa ta zubo abunci taci,,taji wayarta dake tsakar gida kan wata 'yar kujera tana ringing tafito da saure ashanty tagani kan screen din wayar ta, sai da taga kiran aisha sanan tatina da maganar zuwa gidan su dan eta harga allah harta manta da abinda yafaru tsakanin ta da mutanin da tahadu dasu kan hanyar zuwa gidan su aisha- _allah sarki zee kokadan ba tada riqo batada sanyawa rai abu idan akayi abu, nan gurin yawuce agunta idan kamata tarama kenan" amma matuqar bata rama ba toh fa ranar bamai gane kanta har sai tafa rama...
Z)='''amarya ta ango har angon yatafi ne?'''
A}}~_ya ban ganki ba, kema? kasim ma bayzo ba sai kirana da yayi way nabari har zuwa anjima da dare zai zo uzuri ne ya hanashi, kema say najiki shiru shine nakira naji ko lpy??_
Z)='''eyyah wllh kin ga har na kusa isa ga gidan nahadu dawasu 'yan rainin hankali…tashiga bata labarin dik yanda sukayi dasu kasim taqare da cewa,allah yakoma hadani dasu ko ahanya ne,,'''
A}}~ *_dariya sosai aysha keyi tace amma guy nan ya mugun miki wulaqanci da har zai miki kallon kalar almajira tabb" gsky ya debo da zafi" abinda kikai masa kin min dai2 dakika tsaya kika mai da mishi raddi,dadi na dake kenan wllh zee bakya barin bashi,toh yanzu sai yaushe xaki kawo kudin??_*
Z)= '''yanxu xan aiko khaleed yakawo miki dan gsky ban iya dawowa kuma ma mama bata nan yanxu ni zandaura abincin dare kuma gashi wllh dik agajiye nake,'''
A}}~ _shi yasa nace kiyi qoqari ki fitar da gwani amma kinqi sai anyi mgn kice wai namaji baya gaban ki toh kenan wakike so yaxan gaban ki wllh kinatsu kifitar da miji yafimiki tin kafin abba yabadake sadaka…😜_
Z)~'''kinfara ko? anqi afitar da gwani din, kuma da kike zancin sadaka tin kafin abban yayi sadaka dani ay sai kizo kiyi,ingani malama karfa kidaman da wani zancin gwani,, ba gwani ba gwano" bantshi ba, keda kinka tashi ba gashi zakiyi ba, kitashi kitafi har abuja, ayni wllh ko zanyi aure ina garin nan ba inda zanje, bazanyi nisa da mama na ba da yaya na…😘'''
A}}= _he he he wllh,harkin ban dariya,toh angaya miki daman kowa ason ransa yake barin gida,? dik inda allah ya qaddara gidan ki yake dannan in yayi nisan birnin sin, sai kinje,ko baki so,kamar yanda kinka gani yafaru akyna wllh ko amarki banyi tinanin zanyi aure a abuja ba, sai gashi, zanyi aure gidan da banta6a tsammani shigar sa ba, kasim kece wai mamar abokin sa tace zata hada muna dinner ta musamman a gidan ta bayan muntare da kwana daya, kullum Colin bani lbrn abokin sa yake,amma" banta ganinsa ba, keko a waya mugaisa dashi banta6a ba,, dana tmby kasim nace kanata bani lbrn abokin ka har yanxu ko awaya bamu ta6a mgn ba, yace wai kurmane baya mgn sosai,, nanuna tausayi sa,sosai danni na aza kurman kwarai yake nufi,,sosay yayi dariya ta wai bafa kurma wanda bayaji ba yake nufi, mgn ne bata da meshi ba,, nace tohm allah ya kyauta,,yace ay zangasa da zaran anfara biki nace allah yakai mu…_
Z}}= '''hmm aysha kenan,amarya"ga khaleed nan zanturo naga ya shrya dan naga yau fira kikeji naga alama baxaki barni ko abinci naci ba harsai mama tadawo ban daura komy ba shin yanzu saura ma kwana nawa bikin'''
A}}= _ok"sai yazo,, kin manta yau saura kwana 10 jibi zamu fita rabon minti kifadawa su raliya fa- bye_
Z)~''' allah yakai mu insha allah xanfada musu,'''
bayan sun gama, wayara kudi tabawa khaleed tace yayi sauri yadawo kafin marece tayi,,su,, su raliya ko sun kai kudin anko? oho- tashi tayi tafara dura abinci dare, kafin ta zauna cin abinci…*_wai ina emran be?_*
…ya kamata emran kafitar da wannan abin aranka, yarinyar nan fa, da wuya fa, ka qara ganin ta, dik kabi ka canza lkc guda abinda bai kai ya kawo ba zaka wani dame kanka haba emran
ayi mana boking din jirgi yau dinnan zamu koma gida, bazan kwana agarinan ba, kokadan wannan yarinyar bata gabana,tin bayan second 5 da barin mu a unguwa na mantata, akanka ne dik nashiga cikin wannan hali danake ciki tin bayan da kasanar dani ba wacce zaka aura bace, take gefin mota ba kuke mgn, kasim"akanta! katsayar dani, akan ta!! ka 6atan lkc, bayan kasan komy nawa a, tsare yake,, wllh da ba dan, kai abokina bane da kowa ne ne shi, allah sai yahu da fushina, nan gaba kai ma,kakiyaye,dan banaso…
_yaune karo nafarko da naga emran yayi mgn mai tsawo har haka,_
sakin baki kasim yayi yana kallon shi, lallai lamarin emran my girma ne kasan mgnr ma da muke nan ya kwashe komy yasanar da shi, kafin yanumfasa, yace emran wai kai wani erin mutune? shikenan tinda abun byma dadi ba allah yabaka hqr,, bari nakira amana boking din jirgin,million nawa za'a turawa hsptl din?
''' million7 yace ataqai ce'''
hakan kuwa akayi,su kasim suka tattara suka koma abuja batare da sun kwana a garin zariya ba dik da kasim kwarai yaso yaga Aysha, amma bayan kwana biyu zai dawo yaji dame2 suke buqata,,
BAYAN KWANA BIYAR
shirye2 biki sun kan kama tako ina bangarin ango da amarya.

YOU ARE READING
WANI SALO
SachbücherLabari ne dake qushe da wani matashin mutun mai tarin dukiya, kyau, kudi, daukaka a fadin duniya yasame ta allah yabashi, sai dai kash Magana tana matuqar masa wuya wanda idan ma takama sai dai yayi a rubuce Miskili ne na bugawa a JARIDA, kwatsam y...