*🎍🎪🎍(WANI SALO)🎍🎪🎍*
~-------------------------------------~
*Written-by✍🏻*
*Sa'adat alkali D/tsafe*
*(9-10)*...Dan dazon 'yan jarida ne kuwane nason isa gurin da aka tanada na musamman dan tattaunawa da mai girma Emran Yusuf usman,
*Gatattaunawar kamar haka!!*
~_______________________________________~'''dan jarida'''= yalla6ai mune maka barka da zuwa wannan gari namu da fatar ka iso cikin koshin lpy??
*Emran*=lpy..
'''dan jarida'''=masha allah,haka akeso tohm ba tareda 6ata lkci ba dik mutanin dake cikin elahirin birnin zariya sunawa yalla6ai barka da zuwa tareda miqa din bin godiyar su matuqa da ziyar daya kawo musu tare da abin alkhari allah yasaka masa da alkhairi yaqara arziki da budi..
*Emarn ameen*..... afatar bakin shi kadai yatsaya komi jinka bazaka ce kaji abinda yace ba,
'''dan jarida'''= ko yalla6ai nada aure?
kasim dake gefe baisan lkcn da dariya tazo mishi ba yayi qoqrin gintse ta...tareda kallon fuskar emran da lkc daya ta canza,,shi yana mamakin emran anya kuwa lpyr sa qlu? ace mutun da anmasa zancin aure ko mata kamar wanda aka zaga" tsaya wa yayi dan saurarin me" emran zai ce?
*Emran*..is.ok = kawai yace yamiqi yanufe qofa ai nan danan Bodyguards dinshi suka rufa mishi baya 'yan jaridar dake waje suka hau kaukawa daukar sa photo sukuma bodyguards dinshi nata qoqarin tureso dan yasamu gurinda xai wuce da qyar suka isa gurin motocin so akayi saurin bude masa cike da isa ya shiga ya zauna akayi saurin rofe qofa amma dik da haka sai da suka kewaye motocin su,, kasim ma da qyar yasamu yashiga gidan gaban motar da emran yake ciki, saboda mutane ko sallama basuyi da shugaban gidan marayu ba haka suka fice daga gidan,
allah yahuce zuciyar na mijin mazaje shalelen mamy, kuma" dan gatan daddy, Baban su.....au🙊 yayan su khaleefa da afrah nake son nace😜 a gsky dan jiradanan ya iya shiga hurumin da banasa ba koda yake baisan abinda ake ciki bane dan allah yalla6ai amishi afuwa...👏🏻 hannu ya dagawa kasim alamar surutun ya isheshi,
Ranka yadade amun afuwa kafin mu isa masauki mudan mubiya gidan su aisha *matar da kasim zai aura,,, nakira ta yanzu tafito kafin mu isa nadan bata saqo plss..('''kasan cewar matar da kasim zai aura 'yar zariya ce lkcn da yazo xariya gurin wani aiki,suka hadu da ita gashi har mgn tayi nisa ankusa biki kuma wai emran ne best friend din ango babbar mgn koya za'ayi wannan shagali? gamu dai gani''') jin dayayi yayi shiru ne yasa yacewa Driver ba gida zasu tafi ba sai sun dan biya wani guri yashiga mishi kwatancin gidan su aisha...
.....da fitar ta gidan su teema, layin gidansu wata qawarta tanufa dumin takai mata kudin anko saboda tadame ta da kira kullum kiranta take akan tayi maza takawo kudin ankon ta wai dan kada yaqare bata samu ba gashi itace bast friend dinta tohm shine,yau tafito daniyar takai kudin,tace bari tabiya gidan su teema domin tarakata..sai gashi taje ta iske wani kayan haushi,mtss tadan ja wani siririn tasaki,kafi ta kara wayarta akunne". Hello! aysha kina gida? da gacan 6angarin tace, ehh! toh ganinan tafe zankawo kudin ankon" OK, nima ganinan zanfito bakin get yanzunnan kasim yakirani wai zaizo yakawo min saqo na fitoh kafin suqaraso wai dan sauri suke,ok ba damuwa nima na kusan karasowa sai mugaysa da angon ko? gskym kam ya kamata, inji Aysha...
Horn=ake mata ba kyakyauta wa inda dik ancika mata kunne, ai agigice ta tsinke wayar tareda juyuwa bayan ta taga shin wani da qiqine wannan da yake bidar kurman tar da ita wannan dan banzan horn haka? motoci tagani wanda bataga qarshin su ba securitys taga sunfito atare dayan yace" kewace erin dabbace kinaji anameki horn kin wani tsaya wa mutane akan hanya sai kace titin na ubanki ne kinsan wanda ya biyo hanyar nan kuwa? mtssss... dan allah kauce nan wllh ko mubugar dake anan kuma in an bige ki,, an bige Banz.....bai ida mgnr sa ba zee tayi saurin katse shi, dan duk inda ranta yake ya gama 6aci jita ke koma waye suka tare da shi wllh yau saita mugun shuka musu rashin mutunci, ayau dinnan, tace kayi kadan wllh da kai da dik wanda kake taqama da shi, kuma,, kaine, banza,jaki,dabba,jahili,wawa,wanda baisan abinda yake ba,hannu ya daga daniyar marinta dayan security yayi saurin riqe masa hannu,ai nan take zee taqara harzuka,kutt" melecy, naratse maka da allah daka mareni sai kayi danasani marar iyaka dakai da har wanda ya tsaya maka,kai din banza...horn sukaji da sauri daya yaje yana sanar da kasim abinda ake ciki yace yaje yaxo da yarinyar koda ya koma yasanar da ita yalla6ai nakiran ta binshi tayi batayi musu ba dan daman hanya take nema dan shi ma bazata qyale shi ba...gless din mota kasim yadan saukar..gogan naka shi ko nabaya riqe da laptop dinshi yana daddana wa..isar ta keda wuya...ai bata bari ma kasim yayi mgn ba tace, kai malam daman kai kadaure wa wa'ancan banzayin mutane gindi dan suci zarafin bayin allah toh wllh yau da ya kuskura ya mareni wallah sai ya raina kansa dan sai na mugun wulaqanta shi da har abada bazai manta dani ba, dole sai ta gefin danake tafiya zaku wuce dik filinnan bai ishe ku ba, dan kawai kunada kudi shiya sa kuke abinda kuka ga dama toh ni wllh bazan dauka ba, dik maganar da ake bai ma san abida ake ba dan dik hankalin sa naga aikin da yake cikin laptop dinsa" kasancewar zee ba cikin tashin hankali take mgn ba ahankali take amma kai da gajin mgnrt kasan ahasale take yin ta, tsayuwar yaji tayi yawa yadan dago kansa yadan tsinkayi wata agefin motar su, ahankali cikin wata erin murya mai sanyi, yace kasim meye haka? kai da kace saqo kawai zaka bada muwuce,zaka wani tsaidàmu a hanya/ shifa emran ya aza, ayshar ce ke tsaye gefin mota,kasim da yayi zurfi cikin tinanin, wannan kyakyawar halitta yau da yayi ido hudu d ita,, aranshe yake cewa allah kasa wannan ba gamo mukai da aljana ba, danshi wllh har ga allah bai ta6a ganin kyakyawar halitta my kyau ko a film ba erin wannan, dan dik mgnr da zee take kwata2 ba wacce yaji,yatafi duniyar tunani"sai da yaji emran yayi mgn sannan hankalin sa ya dawo jikin sa, am!=am!! ba ita bace bamuma qaraso gidan ba, tohm Idan taimako take nema kasallame ta mana=muwuce inada abinyi "kana 'batan lkc,,dik da cike da aji yayi mgnr,tsaf zee tajishi ranta taji ya masifar 6aci,amma wannan dan mugun rainin wayo ne ma, ni zaywa kallon almajira ? dan wulaqanci" meyake ji akansa~ dik abinda ke yawo cikin kansa nawa. yafi nasa *(kai gsky emran ya mugun bani dariya,😄)*kai tsaye tadan daga murya yanda zai jiyo ta" tace= kai ne kayi kalan wanda daza'a baiwa taimako ni nafi qarfin taimako daga gurin ku wllh,bakuda abinda zaku iya bani aduk fadin duniyar nan..nan gaba kasan erin maccin da zakawa magana, ni" *{zainab lawal jabir}* nafi qarfunka da duk wani abu da kake taqama da shi...wani dogon tsaki taja da saida emran ya jishi har cikin kansa,,kafin tawuce tabar gurin hanyar gidasu. tanufa dan batajin zata iya isa gidan su aysha ayanda takejin ranta na masifar quna...
[TOH FAH!!! ] (BAZAN IYA KALLON FUSKAR EMRAN\BA WACCE TAKE TATTARE DA BACIN RAI) DAN HAKA NI DAI NAYI NAN💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

YOU ARE READING
WANI SALO
Bukan FiksyenLabari ne dake qushe da wani matashin mutun mai tarin dukiya, kyau, kudi, daukaka a fadin duniya yasame ta allah yabashi, sai dai kash Magana tana matuqar masa wuya wanda idan ma takama sai dai yayi a rubuce Miskili ne na bugawa a JARIDA, kwatsam y...