DARAJAR MACE

195 19 0
                                    

💞Page 3💞
Koda Baffa ya dawo yaga mama bai mata magana ba kai tsaye falonshi ya shiga Ammi tabi bayansa kasancewar ita ne da girki,sannu da zuwa baffansu ta fada tana miqa masa ruwa akofi amsa yayi tare da cewa yauwa Amminsu ya fama Alhamdulillah ta fada tana zuba masa abinci bayan ya gama sukaci gaba da hira kamar babu wata matsala anan ammi ta riqa tausarshi domin niyyar shi yaje ya kori mama ta koma inda ta fito domin yasan ba daqaiyyawa taje ba.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Halima kina inane kawu ya fada cikin wani bacin randa baisan na minene ba domin tunda garin Allah ya waye yake jin damuwa akan maganar auren zeenatu da Ahmadu haka kawai yaji zuciyarsa bata qaunar auren don haka ya shirya zuwa kano domin ya samu sule kan maganar fasa auren ko yaji dadi,gani malam cewar inna halima tana mamakin sauyin na kawu domin jiya qalau sukai hirarsu kuma uwa uba bashi da daga murya komai batamasan da zakayi,daukko min kudin nan yau kano zani kan maganar auren yarannan ta tsinkayi muryar kawu,to ta amsa tana shiga daki.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞Kawu kawu mama taji muryar salim da mu'azzam dan wajenta suna fadi cikin murna, murmushi ta saki angaida malam haka aikinsa yake kamar yankan wuqa kai amma a gaisheda uwani,fitowa tayi daga daki lokacin tuni yaran sun kewayeshi yana zaune kasan bishiyar mangoro dake tsakar gidan kan tabarma tuni Ammi ta kawo masa ruwa bayannan ta zauna suna gaisawa saiga mama ta qaraso,sannu da zuwa Baffa kaine tafe ta tsugunna tana gaidashi.
Baffane ya shigo dama bawani nisa yayi ba kasancewar yau lahdi ba kasuwa,qarasawa yayi ya zauna kusa da kawun suka gaisa cikin zuciyarsa yana tunanin zuwan kawun bayan sunyi waya jiya game da gonarda aka saida amma kuma baifada masa ba.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
qarfe 8:00 na dare bayan sun gama cin abinci kawu ya gyara zama yana fuskarta Baffan,sule nasan zakayi mamakin zuwana to amma ba abun mamaki bane idan kaji dalilin zuwana duk danasan zakaji babu dadi,sule amatsayina na uba awajenka Ina so kayimiin wata alfarma ya fada yana kallon yanayin Baffan baijira amsarsa ba yaciga,alfarmar kuwa ita ce fasa auren zeenatu da Ahmadu,kawu lafiya Baffa ya fada cikin firgici,lafiya sule haka kawai na wayi gari da qin auren nan nan ya faiyyacewa Baffa yadda yakeji game da aurennan,take Baffa ya gano matsalar wato harira ce ta zage ta fadawa kawu qarya da gaskiya amma ai bai bata damar zuwa gidansa ba saidai idan wani abu tamasa zuciyarsa ta sanar dashi tabbas biri yayi kama da mutum yanda maman take cikin murna to amma yaushe ta koyi yawan malamai,karka manta tayi ikrarin fasa auren nan ba sau daya ba sau biyu ba don haka zata iya komai yasakeji zuciyarsa tana sanardashi.
Kayi shiru sule cewar kawu daya zuba masa ido yana jiran amsa ko ya samu nauyinda ke qirjinsa ya fada, murmushi baffa yayi cikin ransa afili kuwa cewa yayi to bakomai ya janye idan junin harira san kudi watarana sai takai kanta mahallaka suna zaune zai zuba musu ido ita da"yarta yaga gudun ruwansu,kawu yaji dadi anan ya bashi shawarar hada Ahmadun da khairiyya tuni Baffa yayi na'am yasan mamamshi bazata bashi kunya ba don haka ma bazai fada ma kowa ba sai dai suji andaura harshi kansa Ahmadun.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Khairiyya yace zaune adakinsu tana irga kwanakin da ya rage masoyinta ya zama mijin"yar uwarta duk da yake ma ya Ahmad baisan tanayi ba atunaninta,muryar Baffa taji yana cewa Ina kike zeenatu ya fada yana daga labulan dakin,zeenatu firgit ta miqe daga kangado afirgice waya suke da kamal tuni ta boye qasan filo,nazo ne na sanardake ki turo yaron da yake sonki nan da kwana biyu ayi magana ya juya ya fice,wani ihu zeena tasa take ta Kira Kamal ta fada masa shima yayi murna sosai yamata albishir kan cewa gobe zai turo.
Mama albishirinki Baffa ya amince zai auramin kamal harma munyi waya yace gobe zai turo ta fada tare da rungume maman, murmushin samun nasara tayi,ah to mai na fada miki aidama nace saidai in bana raye za'ai auranki da wancan tsintaccen marar asali.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Tuni Kamal ya turo anyi magana antsaida rana wata daya da sati biyu,Ammi dama tasan an fasa da Ahmad khairiyya ce abin ya bata mamaki sai kuma Ahmad amma Baffa yace ya cigaba da shiri karya fasa abinda ya daure masa kai kenan.
Baffa da bashi da niyyar sanar da Ammi qudurinsa daga baya ya sake shawara ya sanar mata tayi murna sosai saidai yace karta fadawa khairiyya.
Ya bawa kowaccensu kudi suyi shirye shirye dadai qarfin amatsayina namai rufin asiri mama ta raina sauqinta daya Kamal ya bawa zeena kudi duk zuwanda zaiyi kuma bata kashewa tunda komai Kamal yana mata sutura kayan kwalliyarta dsauransu aboye ba tare da sanin Baffa ba,yanxuma kudin suka dauko suka qirga 500,000 ne domin Kamal baya qaramar kyauta suka hada dana wajen Baffa 150,000 sukai sayayya Baffa ya musu kayan fitar biki dasu da yaransu har Jamila dake gidan mijinta, Ammi kam daidai qarfinta tayi komai Koda khairiyya ta tambayeta kayan waye cewa tayi na zeenatu ne Baffa yasata sayowa haka take shirya"yartata cikin dabara take gyareta duk da ta tsargu da magungunan datake sha domin ta taba dauka ta duba hadin Amare ne gashi ita ba Amarya ba koma minene zataji.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Yau biki saura sati zeenatu da khairiyya sunyi fresh dasu kana ganinsu kaga Amare domin sunyi gadon kyau yayangidansu akwai kyau .
Yau ake kawo lefen zeena jakakkuna"yan ubansu goma sha biyu komai yaji sai sam barka mama sai murna take su uwanine"yan karbar kaya maza ne suka kawo lefen komai yaji Kamal ya kashe kudi harda sarqar zinare aciki,mama sai yadawa Ammi magana take ko takanta Ammi bata bi ba.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Abokina yane naga kayi tagumi ko akwai wani abune cewar lukman abokin Ahmad tare sukai BUK,ba komai kasan Baffa ya fasa maganar aurena da zeena kuma yace Ina shiri narasa kan abun ne,hhhh Ahmad kenan Ina ga khairiyya zai aura maka tunda zeenatu da uwarta sunqi, khairiyya kuma cewar Ahmad eh khairiyya ko bakasonta ne yarinyar tayi akwai hankali ga tarbiyya kai kanka kasani saidai ka bawa wani labari fatana Allah yasa ita ce,Ahmad shiru yayi yana addu'ar hakan ya tabbata domin shi yasan mai yakeji game da khairinsa.

#swrter😍

DARAJAR MACEWhere stories live. Discover now