001

473 17 4
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *TSAKAR GIDA!!!🏚*

*—•«Start on: 1/1/2021»•—*

*_FROM D WRITER OF👇🏻_*

*_WAHALA DA GATA seasons 1 & 2._*
            *_RUBINA♦️!!!_*
_{Rayuwata su ke son d'auka}._
    *_'YAR BALLAJJA'U!._*
            *_AND NOW👇🏻_*
     *_TSAKAR GIDA!!!._*

    *_BEE SMART✍🏻_*

*WATTPAD: @Smart_Feenert*
_Joining My Wattpad Link:👇🏻_
       https://my.w.tt/qyn8iY2cHcb

*_{🌳EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌳}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation 
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

All dis buk isn't hv an editing.

001

A cikin Garin St. Louis, na jihar Missouri dake cikin K'asar America, wato United State (USA), tun a safiyar Yau ake gudanar da wani daddad'an iska mai had'e da sanyi-sanyi irin wanda ke saurin narkar da zuciyar masoya, kasancewar wannan k'asar ta na d'ai daga cikin k'asashen da Allah ya hore ma tarin Ni'ima mai albarka da kuma yilwantar arzikin da ya k'ara d'aga darajarta a fad'in duniyar nan.
A wani wargajen babban Titi ne wanda aka matuk'ar k'awata shi da Itace kala-kala tare da furanni masu matuk'ar d'aukar hankali da kuma burgewa, wanda idan har ka tsaya ka kalle wannan tsararren Titi'n da had'ad'd'in motocin da ke ta famar zirga-zirga a samansa wad'an da ba a rasa ba, kai da kanka zaka tabbatar da cewa, ba k'aramin ci gaba aka samu a wannan hamshak'iyar k'asar ba, wanda kuma gefe guda idan ka duba a gefe-gefen titin inda aka ware ma masu ra'ayin tafiya da k'afafuwansu ba tare da sun haw abin hawa ba, zaka lura da cewa mafi yawancinsu masoya ne, masoya kuma na hak'ik'a wad'an da suke matuk'ar k'aunar junansu, domin da zarar ka kalle fuskokinsu gaba d'ai zaka tabbatar da cewa cike suke da wani shauk'i na wata azababbiyar Soyayya wa junansu.

             Wata Jahilar mota ce k'irar New rolls-royce phantom, wadda ta zamana bak'a ce dulum kamar yanda glass d'inta yake da tinted da baka'isa ka iya tsinkanyo abin da ke cikinta ba,
       Kai tsaye wajen wani makeken parkin space d'in wata hamshak'iyar super market ta nufa wanda ya yi nasarar dawo da hankalin mutane da dama a wajen da sai famar zumud'in ganin fuskar mamallakin wannan jahilar motar suke
         Sai da aka kusan shahe wajen 5 to 6 minutes kamar mai wannan had'ad'd'iyar motar ba zaya fito ba, sai can kamar abin assiri suka ga zulowar wata had'ad'd'iyar k'afa ta fara fitowa kafin mamallakin wannan k'afar ta ida fito da gaba d'ai gangar jikinta waje
          "Woww!." Ita ce kalmar da ke ta famar haifafa a wajen dandazon mutanen da ke wannan wajen, kamar masu kiran sallah ta sanadiyyar tozali da wata matashiyar budurwa wadda shekarunta ba zasu haurawa 18 ba, dik da kasancewarta Bak'a, sai dai ba sosai ba,  irin black American nan ce wadda idan ma baka san asalin hasken fata ba, zaka iya kiranta da farar mace,
        Matse take cikin shigar da ta yi bala'in kama jikinta, da wani jahilin trouser black mai zanen Heart maroon color a jikinsa, sai kuma wata 'yar guntuwar riga maroon color mai guntun hannu, wadda iyakacinta cibi ne wanda a jikin rigar aka yi wani dank'areren rubutu bak'i mai taken suna da Love cycle, sai kuma tulin gashin kanta da tayi roll d'inshi da ribon bak'i sai dai kusan gaba d'ai gashin goshinta cike yake da wata kwantacciyar suma da saje wad'anda su kayi bala'in k'ara ma fuskarta kyawo dik da kasancewar fuskarta ba wata make up ce mai yawa a gareta ba, sai kuma tsintsinyar hannunta da ke sanye da wata matsiyaciyar tsarkar Diamond wadda da zarar ka yi tozali da ita tare da sark'ar dake sanye a kyakkyawan wuyanta mai matuk'ar d'aukar hankali, da kuma 'yan-kunnenta da zobban dake sark'ahe a faratunan hannayenta, kai da kanka zaka tabbatar da cewa atare aka k'erosu, sai bak'ak'en takalumma dake sanye a k'afafuwanta, masu shegen tsinin tsiya har na Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un, da suka matuk'ar kama had'ad'd'in k'afafuwanta,
        B'angaren siffar jiki kuwa, kamar ita ta yi kanta domin ko Nick Minaj bata isa ta kamo k'afarta ba.
        Tafiya take a hankali kamar mai tausayin k'asa, sai faffad'an k'ugunta dake ta famar sallamawa mutanen dake wajen, wad'anda da ka kallensu zaka ga dukansu ba wanda yake cikin hayyacinsa
                K'ofar super market d'in ta zo zata shiga, sai dai shi wanda ke kan k'ofar da ya gama lalurar da ta kawoshi a super market d'in ya fito k'ofa kenan ya hangota wanda hakan ya hanashi motsawa daga wajen ya yi tsaye sakaka kamar tunkiyar sake, wanda sai da ya ji alamun an game kanukan makullayya waje guda an buga, wanda hakan ya sa hankalinshi dawo wa jikinshi tare da rufe wangalallen bakinshi dake bud'e tun d'azu kamar wani k'asungumin Sauna, sannan ya bata hanya ta wuce tare da bud'e mata k'ofar shiga cikin Mall d'in yana k'ok'arin washe mata baki, sai dai aza k'afarta kad'ai ke da wuya a saman welcom din shiga Mall d'in aka yi rashin sa'a k'afarta ta gwabce ta taka wani gefe wanda tyls ne zallarshi, sai jin ta yi b'awan Ayaba ta ja ta zurrrrrrr zata fad'i k'asa inda cikin mugun tashin hankali dandazon mutanen da ke cikin Mall d'in su ka  rugo da niyyar su samu nasarar cafketa inda wani had'ad'd'en gaye dake k'ok'arin fita daga super market d'in ya yi hanzarin kaiwa wajenta zai rumgumota, ta samu tayi k'arfin halin k'aucewa daga wajenshi inda Allah ya bata nasarar rik'e wata doguwar roba dake aje a gefe, sai dai anyi ba ayi ba inda wannan robar kuma ta shiga k'ok'arin biyota babu k'ak'k'autawa wanda nan take wani Balarabe dake tsaye a wajen tare da Matarshi da kuma Yaronsu da shi ne wanda ya ci Ayabar ya yada b'awarta ba tare da su ma'aikatan shop d'in sun halkanta ba, nan take ya juya mata bayanshi ta fad'i saman bayanshi tare da rik'eshi gam kamar chiewgum tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya wanda sai da hankalinta ya fara dawowa dai-dai ne da ta tuna a saman bayan wani ne take, ta yi hanzarin mik'ewa tsaye ta saisaita tsayuwarta tare da yi ma wannan Balaraben godiya tana sauke ajiyar zuciya inda shi ma da shi da matarshi da kowa dake wajen suka shiga yi mata "sannu tana amsa masu da godiya inda Manager wannan wajen da Ma'aikatan wajen, su ka zo suna bata hak'uri tare da gaggawar tsaftace wajen, wanda halin rashin damuwar da ta nuna a wajen ba k'aramin kwarjini da d'aukaka ya k'ara mata a wannan wajen ba, juyawar da zata yi bayanta kad'ai ke da wuya idanuwanta suka yi mata tozali da wani had'ad'd'en kuma kyakkyawan Saurayi ajin farko na bugawa a jarida wanda kana ganinshi ko ba'a baka labari ba ka san cewa Mulki da Izza tare da huta ba k'aramin zaunawa su kayi a jikinshi ba, shi ma fari ne sol kamar ba'indiye, sannan gashin kanshi kad'ai abin kallo ne ta yanda aka nakkasa Dollars suka zamo bayi a wajen gyaranshi, wanda ba abin da ke tashi a cikinshi sai k'amshi da k'yallin dake fita a wajen dik da daddad'an k'amshin dake tashi a cikin Mall d'in bai hana fitar na shi ba,
      Sanye yake cikin wasu tsadaddin Suit, maroon color, wanda rigar cikinsu kuma black ce, sanye da wasu tsadaddin takalman da   suka matuk'ar da ce da suit d'inshi, wad'an da su ma suka amsa sunan kalarsu da black, wanda agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunshi kad'ai abin kallo ne balantana zobban dake d'ahe a faratan hannuwanshi wanda da  ganinsu, su ma zaka iya ambatarsu da suna Diamond's, domin shi kad'ai ne sunan da zaka iya kira ya dace da su
          Tsaye kawai yake gefe fuskarkarshi a murtuk'e babu alamun wasa ko 'yar kad'an a tattare da ita, sai P.A d'inshi da ke biye da shi rik'e da wani had'ad'd'en Basket mai tambarin Mall d'in a jiki, yana nuna mashi dik abin da yake buk'ata yana d'auka yana sakawa a cikin,
        Kamar an tursasashi dole ya kalle bayanshi kawai sai had'a ido hud'u suka yi a tare ita da shi wanda sai da ko wannensu ya ji wani irin bak'on yanayi ya ziyarce k'asan kwakwalwarshi tare da fad'awa cikin wani irin mawuyacin yanayin da ba wanda ya tab'a tsintar kanshi a ciki, sai dai dik da hakan ba wanda ya iya nuna alamun hakan a cikinsu domin ko wannensu  fama yake da wata mahaukwacciyar Izzah da isah na ganin cewa shi d'in wani ne, inda shi wannan had'ad'd'en saurayin ya tab'e d'an k'aramin bakinshi cikin wani salo na burgewa, sabida ganin irin kallon da take binshi da shi kafin ya maida fuskarshi gefe yana ci gaba da yin abin da ya kawoshi cikin mall d'in, inda ita kuma ta murgud'a mashi bakinta gefe tare da watsa mashi wata nakkasasshiyar harararta ta gefen ido, sannan ta shiga neman abin da ya kawota, wanda mutanen dake wannan wajen suka koma 'yan kallo ganin bombin d'in da ke kok'arin tashi da su a wajen,
           Cike da wani gagarumin munafurci P.A ya ce "Yallab'ai waccen yarinyar wlhy na ga kamar kai take murgud'awa b........!" Wani wawan kallo ne da ya wurgo mashi kai tsaye ya saka shi had'iyar munafurcinshi wanda kai tsaye ya canza akalar maganarshi da cewa "Tuba nake yallab'ai.!"
         Wani d'an k'aramin tsaki ya ja ciki-ciki ya ce "Stupid girl.!"
     Yana gama shopping d'inshi  bayan ya biya kud'in abin da ya d'auka, a fusace ya bar Super Market d'in,
        A hanzarce wannan budurwar da fiddo wata tsadaddiyar wayarta daga cikin aljihun wandonta k'irar Samsun Age, ta lalabo wata number daga cikin dialing call d'inta, ta kira, wanda nan take aka amsa kiran, kai tsaye ta ce da wanda ta kira d'in "Ku zama cikin shiri, ya na fitowa yanzu, dik inda ya je ku tabbatar da kunbi bayanshi Sannan daga baya ku kirani ku sanar da ni inda ku ke zan zo na sameku a wajen.!" tana gama fad'in hakan k'it ta yanke kiran inda kai tsaye gallery d'in wayarta ta shiga ta lalabo photon wannan had'ad'd'en Saurayin tana kallonshi cikin wani firgitaccen murmushinta mai wuyar fassarawa ta ce "Mahir! Mahir!! Mahir!!! amma sunanka bai yi kama da na mutane ba dik da kasancewarka mutum.!" Bakinta ta tab'e kai tsaye ta ce "Ko da dai wannan ba shi ne gabana a yanzu ba, abin da ke gabana yanzu dik baifi na ci gaba da saka ido akanka wajen cigaba da bibiyarka ba, har sai na tabbatar da na ga bayanka da kuma bayan azzaluman Family d'inka, tabbas rayuwarka da ta iyalanka tana cike da fargabar had'uwa da Dodon da ku ka dad'e da binnewa a cikin kushewa, musamman idan har ku ka samu labarin ya dawo kuma d'auki da makaman yak'inshi a gareku, dik da na san zaku firgita sosai idan ku ka tashi daga nannauyan baccin da ku ke, ku ka sameshi zaune a TSAKAR GIDA'nku, sai dai albishirin da zan maku anan shine, muddin ina lumfashi fiye da goma a yini, ba zan tab'a dakatar da yunk'urin abin da nake da niyyar aikatawa ba a gareku, har sai na ga na samu nasarar ganin bayanku, kuma na nakkasaku nakkasawar da zaku ji da ma ba a halicceku a cikin duniyar nan ba!, amma mu je zuwa, yanzu aka fara wasar.!"
           Ta na gama fad'in hakan  fuuuuuu ta fice daga cikin super market d'in ta nufi wajen da tayi parking d'in motarta ta shiga, daga nan kuma ta tayas......
*FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE Smart_Feenert*
*#Bee smart*

TSAKAR GIDAWhere stories live. Discover now