TARKON MAQIYA

247 4 0
                                    

GODIYA!

ina godiya ga Allah ubangijin talikai wanda yabani ikon rubuta wannan littafi.

Ina kuma qara godaya gareshi dayabani basira,inaneman tai makonsa, ina Neman gafararsa kuma ina Neman tsarinsa daga sharrance sharrance zucuyoyinmu da miyagun da bi,ummi.

GABATARWA!

wannan littafi banyishi dancin zarafin wani ko wataba; wannan littafi qageggene.

Matar 'yar kimanin shekaru arba in da biyar; wacce ke kwance akan gadon asibiti;saboda tsabar wahala kallo daya zakai mata kaganta kamar wacce tayi shekaru sittin aduniya,sakamakon fatar jikinta da tafara tattarewa;amma kallo daya zakaimata kasan cewa kyakykyawarar mace ce,alokacin quruciyarta.

Ba abinda kakeji sai qaran fanka tana juyawa,a dai dai lokacin da maaikaciyar jiyar ta doso dan karamin dakin mai dauke da gadaje biyu,wanda daya daga ciki matar ke kwance akai, shigowarta tayi dai dai da lokacin da matar ta farka daga bacci,tayi ajiyar zuciya;tafara tinanin abinda yakawota nan!ta tina ashefa motace ta doketa dazu!.Ahankali tafara qoqarin bude idan dunanta;tare da yunqurin tashi;amma sai taji kamar an daddaure mata hannu gashi yayimata nauyi kamar dutse, a dai dai lokacin ma aikaciyar jiyar taturo kofar tashigo;taqaraso inda take;. "Sannu iya;ashe kin tashi yajikin?"taya zurfi acikin tinani ta tsinci wata murya nayimata sannu,zuciyarta cike da nadama;duniya kenan!"wai yanzu ni akecewa iya!? wasu zafafan hawayene suka fara sauqa akan fuskarta,taji ansake cewa "haquri zakiya iya da Allah ma yasa da kwa nanki". Duk surutunnan da takeyi da rarrashi bana fahimtar abinda take fada,hankalina ba anan yakeba;banama ta ciwan dake jikina;ga ninta ya tayarmin da tsohon ciwan dake zuciyata,wanda yazamemin (dafi),gashi wanda zan samu maganin ta hanyarsa na rasahi,naroqi Allah ya yayemin sai naga abin kamar qaruwa yake,idan nai qoqarin kau dashi;zai tarwatsamin zuciya.

Natina tsohon mijina da 'yata da mahaifana."Yanzu humaira itama ai tagirma tazama budurwa kamar wannan?ko mustafa tayi aure?ko 'ya 'yansa nawa yanzu?".

Inacikin yiwa kaina wa 'yannan tambayoyin;naji anturo qofa anyi sallama;dogon saurayin fari ya qaraso hannunsa dauke da ledoji guda biyu,daga ganin yanayinsa kasan arude yake;cike da zumudi yace;"da ma aikaciyar jiyar; tafarka ko?" tabashi amsa da cewa "eh" yaqarasa dab da ita yace "sannu baiwar Allah ya sauqin jikin?".Nidai ina jinsa ban iyacewa ko maiba.Bayan 'yan wasu yan awanni da ya dauka yace da ma aikaciyar jiyar zaije gida bayan sallar magriba zai dawo.

Sadiq ne yayi sallama yashiga falo bakowa,part dinsa ya wuce kaitsaye;toilet ya shiga ya doro alwala; sannan yafito domin tafiya masallaci a palon suka hadu da hajiyarsa tana qoqarin shimfida sallaya "Hajiya maryam tace;" yau she ka shigo gidan?" tana qoqarin tada sallah yace "yanzu Hajiya" yana sauri sauri saboda har anshiga masallaci.

Bayan sadiq yadawo daga ma sallaci ne yatarar da hajiyarsa na lazimi,kai tsaye kitchen ya wuce saboda baya jurewa yunwa, amma me zaifaru sai yaji yakasa cin abincin hankalinsa yana can gun matar da yabige,har sai da hajiyarsa tagama lazimi ta qaraso inda yake tanacewa "yau kuwa lafiya! kai da baka kaiwa magriba?". " wallahi hajiya tsau tsayine yafada kaina yau"gaban hajiya maryamne ya fadi!,"ya akayi badai daga wajan aikin bane?"."Ba a wajan aikibane;a kan hanyata ta dawowa daga aikine,wata dattijuwa tazo zata tsallaka titi;tsau tsayi dai na bigeta da mota".hajiya maryam tace;"Yanzu tana ina?"."Tana can hospital yanzu nake shirin komawa ",yana fada yana qoqarin mikewa,hajiya tace; " "Allah yakiyaye gaba;amma karage tuqin gan ganci"." Hajiya ba hakabane ina ganin matar bata gani sosai,kuma da tsau tsayi.
Tare suka tafi da hajiyarsa.
Ina kwance naji anturo qofa;anyi sallama.Wannan farin saurayinne na dazu shida wata 'yar gajeriyar mata,wacce nake ganin bazatafi kamar niba,sai dai ita dayake tana cikin jindadi da kwanciyar hankali;sai ace ahaifama na haifeta.
Maga nar matarce ta katsemin tunanina."Sannu baiwar Allah; yajikin?".Cikin raunin murya qasa qasa;nace "da sauqi". Sun danjima matar tana bani haquri;akan abinda ya faru;lokacin na tabbatar wannan farin saurayin shine wanda yakadeni,kuma ina zaton wannan matar mahaifiyarsace.Bayan tsahon lakaci da suka dauka sukaimin sallama sukatafi, hajiya maryam tace zata kawo 'yar aikinta ta zauna har lokacin daza asallameni
Humaira tai sallama taqarasa palo,;mamanta tana zaune tana kallo ta amsa sallamar, humaira ta nemi guri ta zauna kusa da mama tare da fadin "gaskiya yau agajiye nake mama", mamannata tace " da alama yau Kinada aiki da yawa?"."Bawani aiki mama;wata tsohuwa aka kawo tayi hatsari".Bataji rauni dayawaba ko?". Ba rauni so sai sai dai ahannunta qashinta ya goce se goshinta da yasamu rauni"."To Allah ya kiyaye gaba,Allah yasa 'yan uwanta akusa suke, kamatayi ace yaje yasanar agidan redi,o "ai yaje yafada.

"Yau bazan dawo gida dawuriba;zan wuce nakai baiwar Allah, nan gida".Hajiya maryam tace;" tasanar daku inda iyalinta sukene?" "wallahi hajiya taqi fada;amma ni ayadda na fahimceta irin almajirannanne masu kwana a;qar qashin gada;sun baro iyalansu aqauye suntaho birni neman kudi". Hajiya maryam tace;" To;Allah ya kyauta koma dai wacece ita;kayi qoqari kasan mahallinta kamiqata ga 'yan uwanta". "InshaAllahu". Yayiwa hajiya sallama;hajiya maryam tabi dannata da addu,ar" Allah yatsare Allah yakiyaye adawo lafiya".
Dakyar sadiq da taimakon ma aikaciyar jiyar nan dattijuwar nan tayad sukaita mahallinta,taso ace ita kadai tatafi.

Qarfe 6:00 pm dai dai muka isa unguwar da nake; wani layi muka shiga acikin unguwar ta kwanarjaba kana shiga layin ba abinda zakafara cin karo dashi sai tarin shara da kwatoci, bakuma wani gida dazaka kalla kace akwai wadata;amma aduk dahaka gidammu yafi kowani gida fuskar rashi alayin,katangar gaban gidan ta rushe ana hango filin cikin gidan me dauke da dakuna uku wanda acikinsu guda dayane yarage muke zaune aciki ragowar duk sun rushe, bandaki kuwa se matattun zannuwa mukasa muka kare.
Mukai sallama muka shiga; "Wa alaikumussalam" uwani tamaida sallama; tana qoqarin fitowa daga daki;tare da fadin cewa "muryar wa nakeji kamar ta jimmai ?" "Nice uwani muka qarasa cikin daki najanyo wata matacci tabarma nashimfidawa yaran da suka kawoni, bayan an gaggaisa uwni tacigaba da cewa; " jimmai kekuwa ina kika shiga yau tsahon kwana uku; balabari gashi ni balafiyar qafaba bare na fita nemanki,ina tatinani nace;to ko kin hadu da iyalinnakine;ko kuma an sake saceki dinne;haka dai kullin cikin tinani"."Bako daya uwani hatsarinayi". "A garin yaya?".naje tsallaka titine tsau tsayi yafada kaina"."Mashin ne ko mota?"."Mota ce:wannan shine wanda yabigeni yakaini asibiti yayi ta da wainiya dani".Sadiq yamiqe yace;"to mu zamu koma zandawo ranar litinin yazaro kudi meyawa yabawa jimmai,itama abokiyar zamannata uwani yabata;humairama tabata dubu biyu tabawa uwani dari biyar, sukai ta godiya.
Uwani tace;"ai ni da nazata iyalankine harnafara yimiki murna;to Allah dai ya bayyana miki naki".Nace;"amin".Nai shiru nawani tsahon lokaci ina ta tinani da zancan zuci;nace Allah sarki mustafa;Ashe maganar tafito fili jinayi antabani,tare da fadin cewa;"jimmai; dankine mustafa?"."Nayi wani dan mur mushi mai dauke da nadama;"Nace;ba danabane ni ai bani da da namiji se mace,tsohon mijinane"."Amma kina bani mamaki jimmai!kefa kikacemin 'ya'yanki biyar hudu maza mace daya,yanzu kuma kince 'yarki dayace;gaskiya jimmai akwai wani sirri da kike boyewa game da labarinki,Ammani ba,abinda na boyemiki game da tarihin rayuwata tindaga quruciyata har kawo yanzu ,ai badan komai zaki gayaminba saboda koda mutuwa zata riski daya daga cikimmu kinga zan iya neman 'yan uwanki zaki iya neman nawa,saboda hakama na sanarmiki da ko ni wacece dakuma yadda danayi dake,in dai har kin yadda dani;kuma kina zaune tsakani da Allah dani;yakamata ki sanar dani labarinki.
"Na gode uwani;naji dadin abinda kika fadamin kuma InshaAllahu zan Sanar dake gaskiyar labarina,amma naso ace yaran nan da suka kawoni suna nan su San waceceni,kuma sukoyi darasi daga labarin rayuwata".Uwani tace; "ai wannan mai sauqine;tinda zasu dawo ranar litinin". Bayan Sadiq ya koma gida yake bayyanawa mahaifiyarsa a irin yanayin da yasamu mahillin jimmai,ya tausaya mata sosai;hajiya maryam ma tanuna tausayawa ga jimmai.Sadiq yacigaba da cewa; " hajiya ina tinanin matarnan akwai matsalar da tarabata da iyalanta".hajiya maryam tace; "kana nufin kace ba asalin gidantabane?" "haka nake nufi;dan naji abokiyar zamanta da muka shiga tanacewa wai ko ta hadu da iyalantane,kinga kuwa ai akwai alamar tambaya?,zanso nasan labarinta nikuma na dau alqawarin bincikomata iyalanta.Hajiya tabawa Sadiq goyon baya tace;kuma tare zasuje in zai koma.
Abangaren humaira data koma gida take gayawa mamanta yadda suka sami mahallin jummai tanuna matuqar tausayawa ga matar,mamanta ta ce tinda tace;zasu koma ranar litinin da maimotar daya kadeta zata tallafamata dawasu abubuwan.
Yau litinin yaune Sadiq da humaira harma da mahaifiyarsa suka koma gidan jimmai dan duba lafiyarta Sadiq zuciyarsa cike da zumudin Sanin tarihin rayuwar jimmai.
Sun hallara gaba dayansu;acikin madai daicin da kin Daba komai acikinsa se kullin tsummokaran kayansu,bayan sun gaggaisane sukaiwa jimmai sannu da jiki,jimmai tace; " jiki Alhamdulillah ". bayan shiru nawani dan lokaci,shi Sadiq yanata tinanin yadda zai tinkari wannan dattijuwa akan tarihin rayuwarta,yana kuma jinnauyi daganin girmanta;yana cikin wannan yanayine yaji sautin muryar jimmai tanacewa; " saddiq nasan kayi qoqarin Sanin Inda iyalina suke tun a,asibiti wanda aqarshe nace muku anannake da iyalina, tabbas bani dawani mahallin da yawuce wannan ayanzu, kuma bani dakowa ayanzu bani da kowa se uwani,Amma ayau zangayamuku koni wace;menene dalilin da yarabani da asalina,jimmai taishiru nadan wani lokaci ;fuskarta kunshe da damu;wasu zafafan hawaye suka fara sauqa akan fuskarta,tasa gefenzaninta tagoge,tai wata 'yar dariya ta yaqe.Hankalin kowa yana qanta;tafara kamarhaka

ina neman sha wararku.
dakuma gyararrakin ku, domin samun qarfin gwaiwa.


TARKON MAQIYAWhere stories live. Discover now