TARKON MAQIYA

28 2 0
                                    

Yau kai yayi zafi;a yaune muke zana jarrabawar kammala makaranta,hall din yayi tsit bakajin motsin kowa,kowa ya dukufa.
        Sannu sannu;kwanaki suna qara matsowa,yau Allah yanufe
mu da kammalawa munrabu da
zulaihat cikin kuka da kewar juna, dama sauran qawayemmu.
            Ta bangaren yaya ibrahim
da yaya mustafa ko wannansu ya
kammala karatunsa harma sun sami aiki.
        Yaumun shirya kai ziyara gidan kakanninmu, ya mustafane ze kaimu ni da umma
,jakara muka fara zuwa bayan sallar azahar muka wuce qoqi.
       Baban abbana  ko da yaushe kaje zaka sameshi da mu
tane a kofar gida.
Duk muka durkusa gaba dayam
mu dan gaida Alhaji,umma ce;
tafara gaidashi "Alhaji ina yini,ya girma"? "lfy Alhamdulillah, wacece ne"?.Yatambaya kasancewar bagani yake sosaiba.
Ya mustafa ya karba, "to dama yaza,ayi ka gane ko suwaye kai daba gani kakeba". "Alhaji yace; "ai baganine bana yiba,so nake naji amaryata tai magana". Umma dai ta tashi tabarmu a,nan wajan Alhaji. "Ya mustafa yace; "wannan ai ba amaryar ka bace, kai tsufa dayawa se yara". " Me yaran zasu nunamin,kobaha
kaba amaryata"?. Nace; "hakane
Alhaji".Haka muka cigaba da hira
da alhaji tare da wasan kaka da jika,daga bisani muka shiga cikin
gida.
           Tindaga lokacin da mukaje qoqi,na lura ya mustafa yana sake shishshigemin. Ranar wata lahadi ina zaune ni kadai a palo
Ina kwance akan doguwar kujera ina karatun littafi,hafsace tai sallama " Assalamu alaikum". "wa,alaikumussalam". Na amsa
mata ina me fuskantar bakin kofa, da murmushinta tashigo hafsa kenan ba daga nanba akwai yawan murmushi tana qarasowa inda nake ta fisge littafin dake hannuna,cikin sauri
na tashi daga kwanciyar da nayi,
nace; "Dan Allah hafsa bani Karki
rufemin shafin da nake karantawa"?.tace, "narantse baza
n bayarba tinda bakisan amfanin
saba nace;  "ke ai kinsani". Tace; "sosaima;nikuwa na sani tinda nasan menene so nakuma
iya soyayya, shiyasama kikaga ba
na bata lokacina wajan karance
karancen littattafan soyayya,sabo
da ba;abinda ban iyaba indai aharkar soyayyace". Takaicine ya
kamani da maganganun hafsa nakai hannu nace; "da Allah ni bani littafina baki san ko maiba
se shirme, cemiki akayi darasin
soyayya ake dauka kawai a cikin
karatun littafin? Ai;duk wani qa
lubale na rayuwar mutane, akwaishi a cikin littafi hatta irin
rayuwarki in dai kina karantawa
watarana zaki iya cin karo da ita,
danhaka se ai qoqari afara karan
tawa". hafsa ta tabe baki tare da fadin cewa; "ko;gaskiya ne yaka
mata,manyan daliban littafi", rufe bakin hafsa kenan ya, mustafa yashigo palo, hafsa da murmushinta tace; da ya, mustafa, "ya mustafa ina wuni".
shikuwa gogannaka da yatashi se
ya amsamata ciki ciki, ganin haf
sa ne ya hanashi zama a palo, kai
tsaye dakinsu ya wuce.
            Hafsa ta danyi shiru yana
yin fuskarta ya canja daga murmushi zuwa alamar ta kura,
tadan ja wata doguwar ajiyar zu
ciya, nasan ba komaine yasata canja yanayintaba se abinda ya, mustafa ya yimata,ni kaina bana
jin dadin abinda yake mata in ta
zo gidanmu,kunyace ta rufeni,
magana nake amma hafsa kamar
bada ita nakeba, bata tankamin
nace;  "hafsa meke faruwa, muna
hira kuma kinja baki kin tsuke"
Tace; "hmmmm; tai qasa da mur
yarta, " tace: "Aisha bansan abin
da naiwa ya;mustafa ba in yagan
ni se yayi ta shamin kunu". Nace;
" lallai ma hafsa kamar bakisan
halin ya,mustafa ba nimafa haka
yakemin kin san muskilin mutun
ne". Tace; "ba wani nan kedai kawai kice kina kareshi". Nace; " to shi kenan baki yardaba kenan"?.Tace; "ni dai kawai abar
maganar kar yajiyomu, tacigaba
da cewa;ni fa turoni akayi gunki". Nace; "ni kuma? waya tu
roki guna"?. Tace; "wani bawan Allah ne". Nace; "Allah yasa muji
alkhairi". Tace; "ai alkhairin nema, am  gaskiya maganar nan
ba a nan zamiyitaba  mukoma da
ki; saboda ya;mustafa". Nace; "to
me ya;mustafan zemiki, shi da yake cikin dakima,ke kincika tso
ro, dole dai tasa muka koma daki.
            Tace; "Aisha kin san wa ya turoni kuwa"?. Nace;  "se kin  fada". Tace; munyi babban kamu
Ai,nagayamiki wani abokin Abdulne tinda ya ganki ya kasa
samun su kuni, yana nan yafada
cikin soyayyarki, bakiga yadda ya rameba yadade yana da muna
akan nazo na gabatar dashi agunki,tsoran halinki ya hanani
zuwa,wallahi bakiga yadda yake
sonkiba, tinda tafara maganar na
canja fuskata daga walwala.Nace;
hafsa ki denaimin irin wannan,
kin san dai ko ina da lokacin sa mari, bazan kula wannan 'yan is
kan samarinba, danhaka ki nannade saqonki ki koma dashi,
amsar da zan bayar ba me dadi bace, munyi haka dake abaya na gayamiki ki dena sani a cikin shirgin irin wannan samarin, ki
gaya masa kada yasake ya tinka
ro gidammu. to,haka dai bamu
kwashe da dadiba dani da hafsa,
muna yawan samun sabani da hafsa ayanzu, sabanin ada can lokacin ba mukai hakaba, hakan
nafaruwa ne sakamakon halin
mu da ya banbanta, fiye da a can
baya, yawancin halayen da batayi
A yanzu tanayi, saboda mu,ama
larta da gurba tattun qawaye da samarin banza, innai mata fada
akansu tace ni har yanzu ban wa
yeba. Hafsa akwai saurin fusata amma, nan da nan take saurin sauqowa, kafin tabar gidammu
ta sauqo daga fushin da tayi, bayan munci abinci tace; zata tafi
na rakata,alokacinne take gayamin
cewar mama ta biyamata umra
daga nan zasu wuce dubai, na ta
yata murna sosai.
                  bayan wata daya hafsa tazo yimana sallama, aranar daza su tafi nashirya zuwa gidansu hafsa dan yimusu rakiya
               To;haka dai rayuwa tacigaba da tafiya, daga ban garen ya, mustafa kuwa kullin wani sabon abune yake bullowa
daga gareshi, akaina yana tattalina motsi daya innayi idan
sa akaina, hatta aikin gida idan inayi kamar wanke wanke ko share share indai yana gida ranar weekend, se yasamin hannu ya tayani, umma harta gaji da yawan magana akan ya dena samin hannu, wai zan san garce, kuma ai shi namijine aikin
matane, shikuwa, ya; mustafa se yace mata; "umma nifa wa dannan aiyukan sanda ina maka
ranta ni nake yi da kaina", umma
tai murmushi tace; " hakan yayi
kyau". Nace; umma kinga matar
sa ta huta, Allah dai ya kawoma
na tagari, ina fada ina dariya, nice; ta hannun damar ka ya; mustafa, amarya na gefe babbar
aminiyarka qanwarka na gefe,
ko ba hakaba yayana"?. Yace; "ha
Kane; umma dai tana daga gefe tana ta murmushi; haka dai muke rayuwa a gidanmu cikin farinciki da walwala.



           














TARKON MAQIYAWhere stories live. Discover now