TARKON MAQiYI

32 2 0
                                    

Sakamakon jarabawarmu da muka zana yafito,naci (F.G.C) kazau;itakuma hafsa zata tafi (dala).Amma hafsa taso ace makaranta daya aka kaimu,nima kuma naso ace makaranta daya aka kaimu,se dai ni; bandamuba sosai kamar yadda hafsa ta damu kasancewar ra ayimmu ya ban banta,ni ina San karatu sosai;hafsa kuwa karatun be dametaba tacika saka wasa acikin al amarinta.

Ranar wata Monday da sassafe sega hafsa tayi sallama,umma ta amsa sallamar;bayan sun gama gaisawa da umma hafsa tace "umma ina Aisha?" "Tana wanka;ke yanaga baki shiryaba?" "Ai ni se gobe;se naraka Aisha makaranta" umma tace; hafsa ke nan wannan qawance naku bansan yaya za kuyiba in kunyi aure, to yanzu mamanki tasani?ko ke kika tsara hakan?" Tasani; na gayamata".umma tace; "ai shike nan; amma idan kin koma gida ki shirya karki tsaya wasa".hafsa ta karasa cikin Palo ina daga daki najiyota tana cewa;ke sarkin sininniqi kifito ko fatar zaki canjane?" Ina daga acikin daki nacemata; "dayake nima irinkice ba". Da gudu ta qaraso dakin; " 'yar renin wa yau kina ciki kina kina",nakalleta nace; yanaga baki shiryaba?" taharare tace ke dallacan ai tare zamu kai ki da umma ni sai gobe za a kaini".na washe baki nace Allah da gaske ki.....?"ban gama rufe bakinaba umma tashigo tace hafsa "ai gwara kije ki shrya". Tace to umma".

10:00 am qarfe goma dai dai muka dau hanya;hafsa se famar surutu take nikuwa ina fama da kewar gida. "Aisha saura kuma inkinje makaranta kin hadu da wasu qawayen,ki manta dani". " Ke kike ta qawaye;ni ba wannanne ya kaini ba abinda ya kaini shi zanyi,ke ko irin tinanin gidan nan bakyayi kamar ba gobe za a kaikiba.

Sun kaini makaranta sun ajiyeni nayi kukan rabuwa da umma,hakama hafsa tana kuka tana cewa;itama nan za adawo da ita batasan (dala).Da kyar muka rabu da hafsa;umma taimin fada sosai.Aisha ki kula da karatu sosai karki tsaya wasa kinsan dai halin Alhaji,im baki mai da hankaliba zakiga bacinrai.Mukayi sallama dasu umma,hafsa na dagamin hannu nima ina daga mata,ahaka muka rabu.

Tin ina kewar gida;harnazo na saba na mai da hankalina akan karatu

Ranar hutu tazo kawa se farinciki yake zeje gida,musamman 'yan j.s one munfi kowa farinciki,wata daliba ta taho da gudu; "Aisha kizo anzo daukarki".Da gudu nakarasa inda umma take na maqalqaleta. " Umma tace;duk farincikinne zaki gidanne yasa kika maqalqaleni haka? To sakeni;bakiga yayanki mustafa ba?" "Yana ina?". "Gashi can shi ya kawomu,kin san shima yazo hutu". Na qarasa inda ya;mustafa yake fuskata dauke da fara,a muka gaisa na tambayeshi sauran 'yan uwa yace kowa lafiya

Mun dau hanyar kano;shiru kakeji bawanda ke magana,se can ya mustafa yayi dan murmushi yace, "umma;ammafa Aisha tayi girma dayawa gashi ta qara kyau". "Amma kaga duk da girmannan nata bata daina tsalle tsallen nan nataba". " umma to ai 'yar autace".Muna tafe akan hanya ina tambayar ummata, "umma hafsa ta dawo?" "Aisha hafsa yanzu kam ai ta dade agida tinda akusa take.Ammafa Aisha qawarnan taki ba tasan karatu,saubiyu ana kawota gida wai bata da lafiya washe gari se kiganta tana yawo,akwai wani yaro da yayanki yace yana ganin
su tare,kuma yace yaran bashi da kamun kai,banda sakaci irin na maman hafsa;nawa hafsa take ina ita ina kula wasu samari,zan gayamiki gaskiya idan har hafsa bata canja halayentaba,to tafiyar ku bazatazo dayaba;dan ba zan daukaba naga ita kamar fada baya shiga kunnanta.

Mun isa gida lafiya;se naga gidan ya qara kyau komai an canjashi.Tofa duk inda nayi se naga ya mustafa nabina da kallo,har seda na tsargu ana kallona. Ya mustfa yace; "Aisha kinyi girma da yawa ke dai school din ta karbeki". Nace; "haba dai "ya mustafa kana ganin na rame",ina rufe bakina naji sallamar hafsa,da gudu ta qaraso muka rungume juna muna tsallan murna. "Ammaf hafsa kin qara girma". "Na qara girma ko kika qara girma". Ya mustafa muka jiyo yana cewa; "fada matadai tasan Cesar bani kadai naga girman nataba". Hafsa tace kuma taqara kyau ko yaya?" ya mustafa yace;sosai ma kuwa". Nace mata; "to naji kekuma kin qara fari kinyi qiba". "wace irin kiba kuma;ni da bani da lafiya". "Dabaki da lafiyar ai kinzo gida kin huta har saubiyu". "Waya gayamiki?" ummace; nace; "wallahi hafsa kiji tsoran Allah,nasan halinki pretending kike dan akawoki gida". Ta harareni ta dadamin duka a baya tace; "to muna fuka ai shiru haka kar umma taji".hafsa ta dan bigi ka fadata, race; " Kinsanme?Aisha". Nace "se kin fada".Tace " daga nima ( f.g.c) za a maidani har mama tayarda wai se abba yace idan aka hadamu guri daya bazamiyi karatuba. Aisha amma wannan yayankine ko?" "Me kika gani?" "ganinayi suna kama da Alhaji". "Dan wan Alhajimmune, karatu yake a (A.B.U),Zaria hutu yazo". "Wannan kuwa bawani abu a tsakaninku?,naga se kallanki yake duk inda kikayi se yabiki da kallo". " To dan yana kallona se ki fassarashi da wata munufa". "Ke dai ki fada;imma baki fadaba nangaba gaskiya zatai halinta.

Ni duk a wannan lokacin bansan me hafsa take nifiba,bansan ma anar kallonba nidai kawai idan kafiye kallona nakanji kunya ko kuma naji duk na takura.

Hutu yaqare;munkomo makaranta,na duqufa kan karatu.


TARKON MAQIYAWhere stories live. Discover now