Wannan labarin qirqira ne banyi shi don cin zarafin wata ko wani ba idan yayi daidai da rayuwar wasu Amin afuwa.
Yayi marisa yasha kafso😜
Kai ku taro shi yasha kafso😜
Gungun yara ne suke bin wani matashi suna masa ihu tare da rera masa waqar marisa.
waiwayowa yayi kai zanci abu takazarku ni kuke tsokana kamar kun samu wani mahaukaci to wallahi muddin na kama yaro sai na daddatsashi dan mecin du.....ya fada tare da kai musu wafta ai tuni suka watse suna dariya.
Tagal tagal yayi kamar zai fadi yaci gaba da tafi yana tambele wata yarinya ya hango"ke zo nan"waigawa tayi lungun ba mutane tuni tsoro ya cikata tasan halinsa sarai bashi da kirki tsaf yadda yake abuge zai mata illa.
Uwarki kike kallo bani kudin da yake hannunki ko na illataki awajennan da wasu shegun idanuwanki kamar na mujiya,taso yi masa gardama tuno marin da ya taba mata ne yasa ba shiri ta miqa masa cikin sauri.
Fisge kudin yayi cikin yanayin maye yace fecee kafin naci uwarki awajennan juyawa tayi ta fada gidansu cikin kuka,shi ma gidansu ya qarasa qanwarsa tana wanki tana ganinsa tashiga taitayinta karya masgeta.
Ke dan uwar data haifeki Ina kayana dana shanya a igiyar nan😡gasu dan baba bushewa sukayi na dauke maka cewar innarsa tana fitowa daga daki.
warcewa yayi to da suka bushe cewa nayi ki daukemin ko saki nayi nifa banason shishshigi mtswsss yaja tsaki yana shiga dakin kamar zai bangajeta.
Inna kiyi haquri dan Allah cewar binta qanwar dan baba cikin tausayawa innar tasu,zuruf dan baba ya fito sai ji kake fassss ya dauke binta da mari dan ubanki mai akayi kike cewa tayi haquri ko ni sa'anki ne dan bu....Allah ya isa na wanda baisan darajar iyayensa ba ta fada tare da fadawa daki tasa sakata.
Kan Uwar ya juyo nasan dama ke kike marata baya wallahi idan na kama yarinyar nan sai na ballata ya fada yana ficewa daga gidan.
Shiru uwar tayi itakam tana ga jarrabawa dan baba ya zame mata zakka Allah dai ya bata ikon cinyewa.#meenah
Vote
Comments
shares
YOU ARE READING
SANADIN MAYE
Short StoryLabarin matashin saurayine da ya maida kayan maye ruwan shan sa,yasa mahaifansa zubar qwallah baya ganin mutuncin kansa balle yaga na wani ya wofintar da martabar da Allah ya masa ta kasancewarsa Dan Adam ya cutar da mutane ya zaluncesu,sakaiyya ta...