Chapter 2

115 7 0
                                    

Firgigit ta farka daga baccin da take,

Ruwa ta gani a jinkin ta.

Ya ganin sa tayi tsaye yana rike da wani karamin bucket.

Sauri tayi ta tashi daga kan gadon da take ta koma kan kafet tana shirin yi masa magana ya dakatar da ita.

Daga hannun sa yayi yace don't say a word!

Idanun sa ta kalla sun jajir don bacin rai.

Useless kawai ya fada yana jefar da bucket din hannunsa.

Kallon ta yayi ta kankame jikinta tana kuka don Allah kayi hakuri ta fada cikin kyarmar murya.

Shut the hell up!

Tun yaushe na fada maki ki kira sale ki fada masa ya je airport ya dauko mu?

Daka kanta tayi hawaye na zuba tace jiya da daddare.

And den sai kawai kika yi kwanciyar ki baki fada masa bako?

Kayi hakuri wlh bacci ne....

Shut up 🤫

Yatsansa yasa yana rufe lips din sa yace

Shut up ok!

Ya fada yana daga murya.

Zama yayi kan wata kujera da ke gefen ta.

Yana zama ya kalle ta

Kinsan tun yaushe nike airport ina jiran sale?

Kadan kanta tayi tana share hawayen da ke zuba daga idanunta.

Look here!

Agogon dakin ya nuna mata yace kalli time

Tana dubawa taga 12:pm

i was in the airport since 7:00am ina jiran sale.

Amma shiru ashe keee ce baki fada masa ba ko?

Kayi hakuri..

Dakata daga yau bake ba fita daga gidan nan ok?

Makaranta kuma daga yau kin daina tunda ke baki da wani amfani sai bacci,

Duka aikin gidan nan daga yau ke zakiyi shi.

Yana gama fada ya fita fuuu!

Ransa a bace.

Ya salam gaba daya Kilishi ta tsorata kwanciya tayi saman kafet din dakin ta.

Kuka sosai take yi kamar ranta zai fita.

Hakika tasan tayi kuskure amma bata dauka har ya kai ga haka ba.

Hatta karatu yanzu ya hana ta.

Tashi tayi ganin ana ta kwankwasa kofar dakin ta,tashi tayi jiki ba karfi taje ta bude.

Ina so ki fito yanzu nan ki fara aikin ki ya fada yana kallon cikin idanun ta

Hop you under stand?

Kada kanta tayi jiki na kyarma ta amsa

Yana fita ta shiga toilet tayi alwala tayi sallah kafin ta shiga wanka.

Tana fitowa da sauri ta saka kayanta material doguwar riga ta saka hula ta fito kitchen ta shiga ta hada ma kanta breakfast 🥞

Don yunwa take ji sosai.

Tana gama cin abincin ta taji wayarta na kara tana dubawa taga Nihal ce ke kiran layin ta.

Kin dagawa tayi don tasan kwanan zancen.

MATA BA BAIWA BA.Where stories live. Discover now