HANNAH 11-12💘💘💘💘💘

118 5 2
                                    

Written by
Mrs hilwa

Story by
Mrs hilwa

Edited by
Mrs hilwa

Page
11-12

26-12-20  12:07@m

Bangaren Ahmad kuwa kaman yanda sukayi magana da INTISAR haka akayi kuwa,sukaje date ,bayan magrib ya kawota wani katafaren gida da tace nan ne gidansu ya ajeta, shi ya fito ya bude mata car door din ta fito cikin material gown da wani veil just cover,tayi kyau abunta,nan ma Ahmad 100k ya bata,ta karba tana masa godiya, dan guntun murmushi yayi wanda ya kara fitowa da kyawun face dinsa yace no hug nothing nothing, intisar tayi hugging nasa tare da manna masa sumbata a gefen kumatunsa, nan sukayi saida safe,ahmad ya fice abunsa

Saida INTISAR ta tabbatar Ahmad yayi nisa da ita,kana tayi dialing number a wayanta tace kaga dan Allah zo ka daukeni, bata jira feedback dinsa ba ta kashe wayan,bayan 20minute sai ga wani zabgegen mutun akan babur, kallo daya idan ka masa bazakaso ka kara ba saboda bayada ma'ana koda one second,haka intisar ta dale babur din suka fice abunsu

Ahmad ya koma gida yana tunanin irin rayuwar da zaiyi da INTISAR saboda shi yanzu har ga Allah ganin yake ya samu mace ,irin wacce yakeso,wacce zata nuna masa tsantsan so,wacce zata bashi kulawa,wacce zata dauki dawainiyarsa tamkar uwar da danta, ahmad kam ba'a cewa komai saboda ya kamu da son INTISAR sosai, ahaka dai Ahmad ya bata daren nasa yana tunanin irin rayuwar da yakesan suyi da intisar 😒😒😒😒😒😒😒😒😒😒

Kamal ne zaune a office dinsa sai juyi yake akan kujeransa,wani dan guntun tsaki yaja kana ya tsaya chak tamkar wanda ya tuna da wani abu,idanuwansa ya lumshe ahankali tare da furzo iska mai zafi daga bakinsa,ahmad ne ya shigo bakinsa dauke da sallama ,kamal ya amsa masa yana masa wani irin kallo na ban mamaki,murya cen kasa yace uhmm wannan farin ciki da ya bayyana akan face dinka yau early in the morning, kanan wani ango ,how far?

Ahmad ya zauna daidai sanda kamal yake karasa zancen nasa,kana yace guy kaide bari kawai,Allah intisar is behind this,guy INTISAR ta hadu,kaga na farko,ga kyau ,ga dirin jiki,she's from a wealthy family, nd above all she's educated, and kasan ba kudin nakeso ba saboda nima inada su,kawai kasan yaran masu kudin nan akwai daukan sense,da dressing wallahi,

Daidai lokacin da suke firan hannah ta shigo,hannunta dauke da file fuskanta yau tas itama dauke da fara'a, yau kam kallo daya idan ka mata zakaso ka kara na biyu saboda yau tayi kyau iya kyau,ado taci cikin arabian dress dinta black mai ratsen white,tayi rolling da veil dinta,tayi kyau sosai,sai kamshi take abunta,bakinta dauke da sallama ta karaso ciki,dukansu kallanta suke ko kyabtawa babu,haka ta shigo tana smiling abunta,

kan dayan kujeran da ke kallan Ahmad ta zauna,kana tace katse shurun da ,lafiya kukeman irin wannan kallan haka?ahmad yaja wani dogon numfashi yace uhmmm bakomai babe,kamal yace nidai kinsan bazan maki karya ba Allah baki tabaman kyau irin yanda kikaman yau ba,hannah tace uhmm nagode,so what's up?

Kamal yace lafiya lau wallahi,gani nan wannan guy din yana bani labarin babe dinda muka hadu da ita,hannah ta kara gyara zama tace uhmmm tau wannan karon kuma meya faru? don't tell me bata maka ba,ahmad yace ayyi inaga kawai ku shirya biki yana nan zuwa,hannah tace toh Allah yasa saboda gaskia mun matsu, kamal yace stop dreaming hannah kema kinsan mutunenki da aure not now,ahmad yace baka yadda ba kenan,anyway back to business

Nan zancen ya sauya zuwa ga business plans dinsu na wannan week din duka,take kowa yasan inda zai kama,haka suka yini ranar kamal sai satar kallan hanna yake, ahmad kuwa shima ba karamin kyau ta masa ba yau,

Zaune suke a fallo suna fira,hannah tana bawa zee irin yanda kamal da Ahmad suka sata gaba suna kallo,zee tayi murmushi tace dama nagayamaki kawai ki dinta daukar classic wanka babe bawai all the time office dress ba,hanna tace uhmm zancen ki hakane wallahi,naga alamu sosai,saboda through out yau kam duk wanda yaganni sai ya maganta, zee tace all credit goes to mrs zee,dan haka i deserve a very special treat

Ahmad ne kwance sai juyi yake akan gadonsa,INTISAR da HANNAH ke masa gizo, ya kass runtsawa ga baki daya, haka ya tashi zaune ya dauko wayansa tare da dannawa INTISAR kira,nan ta daga suka shiga firan masoya, ahaka dai har bacci ya daukesa, jin shurunsa yasa INTISAR kashe wayanta itama tayi kwanciyarta

Da safe ma tunda ya tashi suke waya da INTISAR har ya shigo office,duk wanda ya gaida shi saidai ya daga masa hannu kawai ,haka ya karasa office dinsa ya zauna yacigaba da wayan tasa,duk wanda ya shigo haka yake samunsa,kuma ahmad ya gagara kashe wayan,hannah ce ta shigo itama,ta dawo gefensa ta tsaya ta bude masa file dinda ta shigo dashi yayi signing amma yasa hannu ya rufeshi yana bani hararanta, hakan bai hana hanna kara bude masa file din ba haka ya kara rufesa haka suka dinga yi har suka maida abun kaman wasan yara

Daga karshe dole ya saka INTISAR mute yace haba haba haba hanna bakya ganin ina waya ne?hanna ta tabe baki tace ina gani mana toh dan kana waya sai ka aje aikin office din ,ita batasan ka fito aiki bane?Ahmad yace naji jeki idan nagama zan maki signing i will call you Allah, hanna tace toh naji,haka tayi tafiyanta,ahmad ya rufe file din yacigaba da wayansa

Bayan 30minute ta dawo tayi masa tsaye still wayan yake,takaici ya hana hanna cigaba da tsayi jin irin zafafan kalaman da yake gayawa INTISAR hakan ba karamin bakan tawa hanna rai yayi ba,amma haka ta danne ta nuna masa halin ko inkula, nan take tsaye har tsawon wani lokaci,jin yanda zuciyarta ta fara mata zugi da zafi tamkar zata fito yasa hanna juyawa ta fice cikin bacin rai,

Hankalin Ahmad kuwa ko alama baya kan hanna,yayi nisa a duniyar masoya,haka ya bata wannan yinin duka ba tare da yayi aikin komai a office ba😟😟😟😟😟😟😟😟😟😟😟

SHIN HAKAN NA NUFIN HANANH SON MASO WANINE TAKEYI KO KUMA YA TAKE NE?

share
Comments
Likes
Vote

Mrs hilwa💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌💌copy💌💌💌💌💌

HANNAHWhere stories live. Discover now