HANNAH 37-38💌💌💌💌

117 6 0
                                    

Written by
Mrs hilwa

Story by
Mrs hilwa

Edited by
M.hanna

Page
37-38

Ahmad amad sai cizon down lips dinsa yake,haka dai kamal ya dawo gefensa ya zauna yana fadin haba guy relax,kayi hakuri,yace haba kamal ya kake tunanin zanyi introducing wannan abun ya nuna intisar a wulakance yace awurin mahaifiyata ,haba dan Allah, intisar a fusace tace wakake kira wannan?ahmad ya juyo ya banka mata wata uwar harara yace menene banbancinki da dabba?dan jahili bazaiyi abunda kikayi ba,kamal yace kinga intisar kudaina please ku bari har ku koma okay?intisar dai bata tankawa kamal ba hasalima juyawa tayi ta basu baya

Mahaifiyar ahmad amad kuwa bayan tabar fallon,kitchen ta dosa, inda ta bawa masu aikin gidan damar fara jera komai akan dinning,nan ta shiga jera chinchin,samosa,meat pie,akan tray,kana ta dauko ,ta cewa dayan mai aikin ta dauko mata drinks da ruwa,tana gab da shigowa fallon tajiyo hayaniyar amad da intisar,bata karasa ba nan ta tsaya saida taji komai,kana ta girgiza kai tace kana wasa da ranka amad,bazan taba lamuncewa ka auri wannan jahilar ba,nan ta shiga tana sallama,shigowarta fallon shine daidai shigowar HANNAH,cikin hanzari ta karaso ta karbi tray dinda ke hannunta, tana fadin haba mum haba mum,wannan ayyi ba aikinki bane

Kinsan banasan kina wahala,mahaifiyarsa tayi murmushi ta rungume hannah ajikinta tana fadin toh diyar mum,ayyi kinsan inda kina kusa kece zakiyi aikin,kamal da amad kuwa kallo suka bisu dashi saboda inda sabo sun saba ganin hakan,amma hakan ba karamin dadi yayiwa Ahmad ba,mummy ta zame hannah jikinta tace kinyi kyau diyar mum,hannah ta juya  ahankali tace Allah koh mumcy?mummy tayi dariya tace ana magana,nan dai suka zauna,kamal yace uhmmm su diyar mummy baki ganmu bane?

Hannah dake rike da hannun mum ta tabe baki tace hmmm kanada aiki malam,ayyi tunda kukabar mamana tayi maku wannan aikin zakuji ajikinku,kamal yace kiyi hakuri,mummy ayyi bakice mu zo ba,mummy tayi murmushi tace kyalesu hannah,ya aikin toh?hannah tace before wannan bara nayi serving naki saboda nasan kinyi aiki,bata bari mummy ta kara koda kalma daya ba,tayi serving dinta ruwa masu sanyi tasha,kana ta karbi cup din hannunta tace mummy aiki alhamd lafiya lau,mummy tace ma sha Allahu, ina fatan amad baya takura ki?hannah tayi saurin girgiza kai tace ko alama mummy

Yanayin yanda ta bawa mummy amsan ya tabbatar mata da akwai wani abu saboda inda before ne tuni zata kaiwa amad duka ko harara amma yau sai taga kota kansa batayi ba,mummy tayi murmushi tace bara na shiga nagani ko sun kammala,mummy tana mikewa hannah ta mike tabi bayan mum,haka suka karasa kitchen din a tare suna dariya

Kamal yayi murmushi ya maida dubansa kan amad wanda ya maida dubansa kan intisar wacce ga baki daya ta maida hankalinta da duniyarta akan waya,tamkar baa fallon take ba,amad ya kira sunanta ahankali, yace intisar?juyowa tayi tana smiling tace baby necklace din nan ta gold din nan zatayi kyau a neck dina wallahi ya ka ganta?wayan takai masa a face wacce ke dauke da hoton wata hadaddiyar zinari mai kyawun gaske,Ahmad kuwa ko kallan screen din baiyi ba kallo kawai ya bita da shi ko kyabtawa babu,ji yake kaman yayi strangling nata

Ganin yanda yanayinsa ya sauya ya bawa kamal dariya amma babu halin yin dariyar saboda har ga Allah yasan intisar ta samu sa'ar ahmad sosai,intisar kuwa ganin yaqi kallan abunda take nuna masa yasa ta banka masa wata harara taci gaba da sha'aninta, ahmad amad ya huro iska mai zafi daga bakinsa ya maida dubansa kan kamal wanda ya kara yin relaxing yana sipping juice dinsa a cup yana kallansu,

Ahmad yace da Kamal kaga abunda na daukowa kaina koh?kamal ya qara gyara zamansa yace wannan labarin naku ne ba nawa bane ayyi da mutane suna nuna maka love sai kayi tamkar baka gani and you ended up with a witch🧟‍♀️🧟‍♀️🧟‍♀️🧟‍♀️🧟‍♀️🧟‍♀️kamal ya karasa statement dinsa yana kallan inda intisar take sai yaga hankalinta ga baki daya baya kansu,sannan yace uhmmm yanzu dai kaga abunda ake cewa WIFE MATERIAL koh?

Ahmad yace a ina?intisar ce wife material?banasan iskanci wallahi,ina material din yake anan?Allah taci albarkacin mum yau da naci ubanta wallahi,wannan ayyi daga nan kowa ya kama gabansa kawai dan bazan daukar mata raini akan mahaifiyata ba,yaja wani dogon tsaki mtswwwwww

Kamal yayi murmushi yace ba ita nake maka magana ba,am talking about HANNAH  itace ake kira wife material complete material kuma saboda abunda tayi yanzu shine ya dace ace intisar tayi ko bakomai this is her first time of meeting her but imagine abunda tayi maka,haba kai ka kuru fah wallahi da ace yaya is around da sai dai kawai taji saukar mari a kan face dinta sai dai kawai kabar gidan,ahmad yace wallahi kaide ka fadi ka kara fadi harni sai nasha slap din,nan dai kamal ya bawa ahmad hakuri sannan fah suka koma wata chapter ta daban

Bangaren mummy da hannah kuwa suna shiga kitchen suka shiga kara gyara komai, mummy dake saka tissue a cikin glass cups tace ni kuwa na tambaye ki hannah?hannah dake tsaye tana jera plate akan tray tace ina jinki mummy,mummy ta tsaya chak daga saka tissue din,ta maida dubanta kan hannah tace wannan da sukazo tare da amad ita kuma wacece?


Hannah kuwa daga sama ta jiyo tambayan kaman bazatayi magana ba,sai tayi murmushi tare da yin dan karamin kyabci wanda ko wanda ke kusa da ita bazaiji ba bakinta kawai ta motsa,ta juyo tace bai gayamaki ba koh mum?kunyarki yakeji,uhmm ayyi itace wacce yakesan ya aura,sunanta intisar, sun zama close sosai mum,kai kedai mum bari amad yana sonta sosai,kowa is wrong ita kuwa she's always right,Allah dai ya kaimu lokacin biki mum,she's the best Allah, ta karasa fadan hakan tana kara jera plate din,mummy da ta saki baki imani yayi mata yawa da jin bayanin hannah

Mummy tayi wata yar dariya mai dauke da alamun tambaya tace kinganki banasan wasa,tell me mana,who is she?hannah ta kuwa ba tare data dago ba tace uhmm Allah mumy ba wasa nake ba,Allah gaskiar kenan she's his wife to be,sannan ya gayamana cewa bazaki taba ce masa aaaah ba,sannan muma munsan kinasan abunda yakeso,

Mummy tayi shuru bata kara cewa hannah komai ba,nan hannah ta dauko tray din dan takai dinning,kitchen tabar mummy a tsaye cike da mamaki da kuma takaici,hannah kuwa bayan ta karasa dinning ta aje tray din tayi murmushi tace AHMAD AMAD kenan,ayyi wallahi tunda kaciman zarafi yau sai na tabbatar mummy ta maka fiye da wanda kaman,intisar the game begins now

Nan tayi setting dinning,har ta karasa dauko komai daga kitchen mummy tana nan tsaye,masu aikin da keta faman aikinsu hannah tayiwa magana sukabar kitchen din,karasawa tayi gin mummy tace lafiya kuwa mummy?mummy tayi murmushi na karfin hali ta shafa gefen fuskar hannah tace Allah yayi maki albarka, kiyi hakuri,zaki samu wanda yafi Ahmad amad,amma koda baya sonki bazan taba bari ya auri wannan marar kunyar ba,bata jira me hannah zatace ba ta fice daga kitchen din ranta bace

Hannah kuwa kallo ta bita dashi,murya cen kasa tace me take nufi da nayi hakuri?ko tasan ina son Ahmad ne?kai ayyi bantaba gayawa kowa ba,so may be wannan tunanin mum ne kawai

Mummy tana fitowa daga kitchen fallo ta dosa tayi tsaye ta kara yiwa Ahmad da intisar kallo, wadanda babu wanda yasan shigowarta,kai ta girgiza tace ko alama baku dace ba,wannan bata dace da tarbiyar da na baka ba,sannan bazan taba haihuwar danda zaifi karfina ba,duka maganganunta ita kadai tayi abunta ba wanda yaji sai hannah dake bayanta tsaye itama zata shiga fallon,mummy tace yawwa amad meet me in my room please, sai lokacin ya dago yana smiling ya nufota, wani kallo yake yiwa hannah ganinta gefe tsaye,mummy kuwa juyowa tayi ta nufi dakinta,ahmad kuwa tsaye yayi gab da hannah, yace haba talk to me mana

Nasan zaki fahimceni,kinsan what i did dazu.....hannah ta katse shi cikin hanzari da kaje kaji kiran mum first yafi wannan surutun da zakaman please, nan tasa kai ta karaso cikin fallon,jiki a sanyaye amad ya nufi dakin mum


Vote
Comments
Share
Like

Mrs hilwa's copy✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍🤜🤜🤜🤜🤜🤜🤜🤜


HANNAHWhere stories live. Discover now