HANNAH 23-24💔💔💔💔

109 6 0
                                    

Written by

Mrs hilwa

Story by

Mrs hilwa

Edited by
Mrs hilwa

Page
23-24💕💕💕💕💕💕💕

Bayan kamal ya gama waya da Ahmad yana kwance akan doguwar sofa ya dannawa hanna kira,bayan sun gaisa,kamal ya gayamata yanda sukayi da Ahmad,murmushi tayi tace uhmmm agidan shi kuma?kamal yace eh wallahi ,tace alright no problem, sai ya kenan?kamal yace kiyi wanka,zanzo na dauke ki, hannah tace alright ba matsala bane sai kazo

Zee na zaune,hanna ta sanar da ita,zee tace hmmm jeki kawai bazan samu daman zuwa ba,hannah tace no problem

Misalin karfe hudu na yamma kamal yazo daukan hannah, taci adon atamfa riga da sket,kayan sun mata kyau sosai,mayafinta,wrist watch,earings,flat shoes da mini handbag dinta all in black ne,ba wani dogon makeup tayi ba amma tayi kyau sosai sai kamshi take

Haka suka isa harabar gidan Ahmad,inda kamal ya saka kaftan light blue ya saka komai black shima yayi kyau sosai irin nasa,knocking sukayi busu wani dauki dogon lokaci ba ahmad ya bude masu,shigowa sukayi suna gaisawa da junansu ,fallo suka zauna Ahmad yace kunyi kyau sosai,kamal yace ayyi kyau na mata ne ya karasa maganan yana kallan hannah dake galla masa harara,yayi dariya yace maida wukar hajia

Nan sukaci gaba da firansu sai dariya suke,hannah tace i need a glass of juice,ahmad yace gidan ba bakonki bane hajia serve yourself, ta mike tsaye tana fadin but am your guest anyway bara naje,haka ta nufi hanyar kitchen

Tana tura kofan kitchen din ta hango intisar a tsaye tana aiki ta bada baya,hakan yasa gaban hannah ya fadi ba shiri, take farin cikin da ke kan fuskanta ta dauke,karasawa tayi ciki tana gallawa intisar harara wacce batasanma da shigowar mutun ba

Jin kamshin turaren da ya daki hancinta yasata juyowa ba shiri,ganin hannah a tsaye yasa intisar sakin wani kayataccen murmushi kana tace sannu da shigowa,hannah ta danja wani guntun tsaki ta karasa gun fridge din ba tare da ta cewa intisar komai ba

Bude fridge din tayi tana kara masa kallo sanadiyar kayan lemun da yake dauke dasu different types,ganin kota kanta hannah batayi ba yasa tace mekike so ne?hannah ta kara mata wani kallo na wulakanci kana tace kicigaba da aikinki gidan ba bakona bane,hakan yasa intisar yin cirko cirko tamkar wata barauniya

Bayan hannah ta dauko lemun da ya mata,ta dora shi akan fridge,ta nufi kusa da durowar da intisar take tsaye ta bude ta dauko glass cup,tana daukowa ta maida dubanta gefen intisar taga citta danya da tafarnuwa,ta girgiza kanta kana tace indai ahmad zakiyiwa girki kada ki saka citta da tafarnuwa bayaso he's allergic to them,bata jira feedback dinta ba ta dauki juice dinta ta fice cikin isa da iko

Hakan ba karamin mamaki ya bawa intisar ba,dubanta ta maida kan citta da tafarnuwa din murya cen kasa tace kaji wani sabon iskanci wai hausa nacewa "Rashin jini rashin tsagawa"baki ta tabe tacigaba da aikin da tasa gaba

"Ni mrs hilwa dake gefe nace wannan ko duk duniya zatayiwa girki ayyi ya isa ace ta gama yanzu😒😒😒😒😒😏"

Fitowar hanna yasa su ahmad maida dubansu kanta, ganin yanda ranta ya wani bace, cikin kulawa kamal yace babe lafiya kuwa?cikin zafin nama tace............😡😡😡😡😡😡😡😡😡😡

Sai mun hadu a page na gaba danjin yanda za'a kaya tsakanin su

Vote
Comments
Share
Likes

Mrs hilwa copy✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍

HANNAHWhere stories live. Discover now