FADILAH KO SAMHA p 2

125 2 0
                                    

FADILA KO SAMHA

writing by
Oum... now and old

P 2

Dedicated to Ummu hairan





Washe gari Salim da sai goma ya tashi dan dama ya saba tashi da a wannan lokacin bayan yayi sallah wanka ya fara yi kafin yayi brush ya sauko kasa yayi break sama ya koma ya chanza kaya wata zuwa manyan kaya wani farin yadi ya saka Wanda ya matukar daukan Sa musamman da ya dawo dan karamin glass din Sa ya zama mukullin motar Sa ya duka falo ya fito ya samu iyayen NASA suna tattauna har kasa ya duka ya gaidasu da fara'a suka amsa dan Allah ya Sa musu San dan nasu sosae Abba nehh y kalleshi tare da fadin Salim ina fatan baka manta da magana ta ta jiya ba dan gsky abin yana da muhimman ci sosae kuma idan kayi min hakan zanyi farin ciki dana


Duk da baya son abin amma yaji maganar mahaifin nasa har tsakiyar kansa nan dai ya sadda kai yace ban manta ba Abba insha Allah zan dawo da wuri ma

Abba yace to maza tashi kaje Allah ya maka albarka kada lokaci ya kure ma

Ya amsa da amin ammi ma tace a dawo lpy yace Allah yasa

Kai tsaye ya nufi wata mota kirar landkruser wadda tasha wanki sai kyalli take dan daba al'adan gidan ce kullum da safe sai mai wankin mota ya wanke motocin gidan baki daya amma banda lokacin sanyi

Shiga yayi tare da kunna karatun alkur'ani sannan ya kunna ac kadan ya mai gadi ya bude masa get a tsanake ya fice daga gidan yana sauraran kira'ar sheikh suday's

A katon wani mall naga ya tsaya tare da danna Horn ba jimawa aka wangale masa kofar mai gadin nehh ya fara miko gaisuwa har kasa ya tsuguna Salim ya tsaya suka gaisa kamar ba uban gida da yaro ba har raha sukeyi sannan ya karasa parking space ya aje motan fitowa yayi ya nufi cikin mall din duk inda ya wuce gaisuwa ake kawo masa wasu siyi musabaha wasu kam saidai ya amsa dan kin had a hannu suke dashi mutane da yawa suna mamakin Sa shi baya nuna wani banbanci tsakanin Sa da ma'aikatan Sa say tari tare suke cin abinchi da wasu ma'aikatan NASA sannan bayason ana duka masa wasu sukan ce tunda Allah uban giji ya baka dole a duka ma alhaji Salim nikuma nace ai ba tsurku zaku tsaya yi ba kuma Ku tashi Ku nema Allah ya baku


Har ya kusa kai office din sa nehh ya tuna zai karbi sako agun manager dinsa na gun dan haka sai ya dawo ya nufi bangaren Sa dan a ka idar Salim indai bai zauna a. Office dinsa ba to baya Aiken kowada kansa yake komai nasa



Yana cikin tafiya a nutse sai fara'a yakeyi da murmushi GA ma'aikatan Sa bai kula da ita BA sai ji yayi ya bangaje ta da Sauri ya riko hannun ta ganin tana neman faduwa gaba daya abinda takes an siya ya zube a kasa duka ya tarwatse





Da Sauri ya saki hannun ta yana kokarin tsuguna wa ya kwashe mata kayan daya zube aikuwa nan ma'aikatan gurin suka taso d sauri dan su kwashe kayan yana ganin su ya dakatat dasu tare da fadin baku kukayi mata laifi ba nine dan haka Ku bari na kwashe mata duka ehemm kowa ya koma inda kuma ngd kalawa



Gaba daya gurin ba wanda bai yi mutuwar tsaye ba kuma duk wanda ke gurin da mai siya da mai siyarwa yasan Salim KUMA yasan matsayinsa agun dan haka kowa mamakin sannan abin yakeyi itako yarinyar da ya buge gaba daya ta shagala da kallon Sa ta saki baki kawai tana kallon Sa yana kwashe kayan a hankali har ya gama tashi yayi ya mika mata kayan ta karba tare da fadin am sorry ban kula ba kiyi hkr

Sororo tayi tana kallon sa bata ma San mai yake cewa ba labbansa kawai take kallo da suke motsawa a hankali a hankali kamar ba mgn yake ba ji tayi gaba daya jikin ta yayi sanyi tsigar jikin ta ta tashi

Hannu yasa a Dan kusa da idan ta tare da fadin madam mgn nake tayi fahh

Firgigit tayi ta dawo hayyacinta tare da fadin ohh ba komai bro ai ba abinda ma ya faru am sunana SAMHA kuma ina nan garin Kano nehh ta fadi hakan tare da mika masa hannu

Kallon hannun ta yayi kafin ya aklleta kawai ya yi tafiyar sa mutuwar tsaye tayi agun dan bata taba tunanin haka daga garesa ba yarda take mutuwar San gayen nan amma ya dizga ta a gaban jama'a a ranta tace lalle ma Salim zaka gane kuran ka da zaka shigo hannu bakasan wace SAMHA MUKHTAR ba ne ka tambaya za'a baka lbr ban taba Neman Abu na rasa ba kada kai tayi ta nufi gurin da zata biya kudi bayan ta gama biya nehh ta fice a gaban motar ta ta tsaya ta zaro wayar ta number Salim ta kurawa idanu kawai tana tunanin ta kirashi nehh ko ya kiransa tayi kawai Ring biyu ya daga tare da rangada sallama da daddadar muryan sa amsa sallaman tayi tare da yin shuru a hankali ya furta waye

Banxa tayi masa saiji tayi kit ya katse wayan wani kululun bakin ciki nehh yazo mata wuya dan bakin ciki kawai saita shige motar ta ta kifa kai a kan sitiyari ta jima a haka kafin ta dauko wata kwalbar magani ta bude ta kwankwade duka sannan ta buka ta a waje ta fashe sake kifah kanta tayi akan stiyari ta jima kafin ta fara gani kadan kadan a haka ta ja motar zuwa unguwa ALU AVENUE dake nan cikin nasarawa g r a Allah nehh ya kaita gida lpy kawai amma dai ba wani ganin gaban ta take ba sosae tana zuwa tayi aka bude mata tayi parking amma ta kasa fitowa a cikin motar wasu mata dake gefe suna ganin haka suka taso da sauri suka bude motar suka kamota suka shiga da ita ciki a katon gadon ta sika shimfide ta tana kwanciya bacci ya dauketa suko sika koma inda motar ta take duk wani Abu data siyo saida suka kai mata dakin da dan shi kadai nehh aikin su a gidan idan ta shiga irin sannan yanayin su kaita bangaren ta shine kawai aikin su

Bayan sun shigar da komai ciki nehh suka Rifo mata kofah sai a lokacin na samu damar karewa SAMHA kallo doguwace mai yar kiba cikin ta a shade yake kamar bata taba cin komai ba tana da manyan Boob's masu daukan hankalin da namiji bakin ta dan karamine a tsuke mai dauke da dogon hancinta kamar Biro duk da idan ta a rufe yake bazai hanaka gno manyan idanun ta ba amma ba chan na itama fara ce sosae dan fatar ta har barazanar fitar da jini takeyi matsalar SAMHA daya tana shaye shayen zamani kuma tana da abokai maza da yawa da suke jin dadin su.............



WANNAN KENAN

VOTE
more comment more type

Plz shared

FADEELAH KO SAMHAWhere stories live. Discover now