FADEELAH KO SAMHA
writing by
Oum now and oldSadaukarwa nehh ga maman hairan Allah ya Kara hazaka da basira
P 7&10
A bangaren salim kuwa yana shiga cikin dakin sa bai zarce ko ina ba sai bandaki ruwa ya watsa Sannan ya saka blue din doguwar riga Kara min takalmi ya dauka mara nauyi tare da saukowa kasa domin Samun abinda zaci sakamakon wata yunwa dake damunsa
Dining table ya nu fa Kai tsaye domin samawa kansa abinda zaici yana isa yaja kujera ya zaune tare da bude babban plas din dake kan table din tuwon shinkafa nehh da miyar agushi wadda taji naman rago murmushi yayi Dan a cikin abinci idan akwai abinda yake matukar so to tuwo nehh Dan haka ba bata lokaci ya zauna ya kwashi tuwon nan saida yaji yana kokarin dawo masa sannan ya hkr
Bangaren mom dinsa ya nufah ba domin yasan sadiq ya ruga ya fada mata duk abinda ya faru yanzu kawai shi take jira da sallama ya shiga falon nata zaune take akan 3sis sai dai wannan karan uban tagumi ta rafka dan bata ma san da zuwan tilon da nata ba dan haka sai da ya kuma maimaita sallamar tasa har kusan sau uku
Firgigit tayi tare da mikewa tana fadin a a salim kaine har ka fito kenan ai ban yi tunanin futowarka yanzu ba ma
Dan sosa keya yayi tare da fadin wlh na fito mom harma na ci abinci brk da gida fatan an wuni lpy
Lpy klu saidai kai naga kamar ba lau ba dan ba haka na saba ganin ka ba
Yace ba komai mom kawai dai akan yarinyar nan nehh da dad yace naje na gani nehh
Tace yawwa dama inason mu zauna akan wannan batun ma maza zauna muyi mgn
Zama yayi akan cafet kamar yarda ta bukata batayi mgn ba dan tasan komai zata ce masa bazai komai kan kujera ban salim muddin tana zaune a kujera to tabbas kan cafet nehh gurin xaman sa dan haka ba tayi mgn ba dan hakan ba sabo bane agun ta saima wani dan guntun murmushi da tayi tare da fadin kai dai salim baka da dama idan nace ka zauna ma ba zama zakayi ba dan haka muje ga abinda ya zaunar damu shin yarinyar tama nehh ko kuwa dai dan abinda naji sadiq ya fada min gsky ya daga min hankali
Shuru yayi yana tunani a ransa yake fadin to mai kuma sadiq ya fadama mom kodai ya fada mata nayi wa yar mutane rashin kirki kai bazai fada mata ba sadiq nawa nehh wani abun dai ya fada da ban amma to mai ya fada mata wanda har ya daga mata hankali hk kai allah yasadai abun kirki ya fada mata dan gsky bana son mom ta gano bana son yariyar nan tun yanxu, , , ,
Shurun da mom taji yayi yawa nehh yasata fadin salim da kai fahh nake mgn kayi wani shuru kodai bata ma bane
Dan sosa keya yayi dan har ga allah baya son yaja da dad dinsa dan haka ya dan yi kasa da murya yana fadin munje gidan nasu fahh mom kuma ma na ganta harma mun gaisa amma ban ce mata komai ba gsky a bani lokaci nayi tunani akan ta mom
Sakin baki mom tayi tana fadin kai kaji wani shirmen banza agun ka fa salim wani tunani idan tayi ma kawai tayi ma batun tunani da wani bincike bai ma taso ba tunda kai dai kasan wannan yarinyar yar aminin mahaifin ka ce kuma babban abokinsa nehh a fannin kasuwancin sa kaga ai ba abinda bai sani a kansa ba kuma baza a baka wadda zaka cutu ba amma tunda kace haka kaje na baka nan da zuwa dare idan dad dinka ya dawo sai ka fada masa sakamkon da bakin ka
Bai ce kala na illah mikewa dayayi yana tom mom ngd sosae kuma insha allah zakiji sakamako mai dadi momyna
Murmushi tayi mai nuna alamar tsantsar farin ciki da jin dadi kalaman da dan nata yayi kafin tace tom allah yasa haka son yanxun kuma ina zuwa
Yace mom kin manta da hanan yaufahh xata sauka kuma saura 30min nehb jirginsu ya sauka xanje dauka ta nehh kamar yarda dad y umarta
Momy tace ohhh kuma kasan na manta idan banda ka tunamin
Salim yace kai mom sisi din guda ita kadai ce fa dani kumaa sai a manta da ita ai mom ni yarda nakeji a yanzu ma baxan taba san wata mace makaman cin san da nakewa kanwata ba
Har ran momy taji dadin kalaman salim kuma tasan hakan ba wai bata sani ba shiyisa a ko wani lokaci take gdy ga ubangiji daya bata da kamar salim domin tsantsar hankalinsa da sanin ya kamatansa kalon sa tayi kallo mai bayyana tsantsar so da kauna na mahaifiya kafin tace tom son a dawo lpy amma sai naji kamar sadiq yace zai dauko ta fa
Da sauri salim yace haba ya isa mom ai ni zan dauko ta nifahh mom ban wani yarda da sadiq ba sosae sabida irin abinda yakeyi wa hanan hakan yana bayyana akwai wani abu da yakeso amma dai koma meye yau zai fadamin najishi
Yana kaiwa nan ya fita da sauri tare da yi wa mom sallama
Ita kam kallon sa kawai tayi dan tasan ba abinda zata ce masa ya tsaya yanxu dan hankalin sa gaba daya yayi airport domin dauko tilon kanwarsa
Salim kam yana isa bangaren sa bai tsaya wata wata ba ya dauko wayar sa number sadiq ya dannawa kira bugu biyu ya daga ko gaisawabasuyi ba salim ya soma fadin sadiq na fada ma kada kaje airport din nan dan ni zanje dauko ta yanxu na fada ma
Dariya sadiq yayi yana fadin haba bro ya kake haka nehh nifahh yanxu haka ba ina katsina road na kusa airport ka jira mu a gida kawai
Wani huci salim ya fitar tare da fadin sadiq sadiq bana son bacin rai plz kar ka je kaji abokina plz plx wlh ni nake son na fara kalle kanwata kuma na daukota da kaina kamar yarda na kaita da kaina
Shuru sadiq yayi yana tunani kafin yace uhmmm tom shikenan kazo ka sameni a kofar airport din amma ka taho da driver din da zai komar da motana gida
Salim yace ok baka da matsala ganin bani 15min abokina dan allah ka jirani kaji
Sadiq yace ai nace zan jiraka ko
Salim yace ehh ehh ka fada tom gani nan yanzu yana kaiwa nan ya katse wayan tare da fadawa ban daki shaf shaf ya watsa ruwa wata Orange din shadda ya saka sannan ya kawo hila kalar kayan ya saka kafin ya kawo agogo kirar Apple ya saka takalmi yasaka shima mai kalar orange kafin ya dauki mukullin motar sa
Sauri sauri gudu gudu ya fito ya nufi parking space matar sa ya dauka kirar kamfanin focus wadda itama kuma ta kasance baka ba karamin kyau motar ta masa ba driver ya kira bai masa bayanin inda xasu ba kawai ya wullah motar tunka fin su karaso mai gadi ya wangale masa get ya fice d gudun tsiya kamar xai tashi sama...........
Im sorry my fans ina mai kara baku hkr akan daukar lokacin da nake ban typing da wuri hakan ya faru nehh sakamakon rashin lokaci ayyuka sunyi yawa amma insha allah yanxu mun dawo gadan gadan domin faranta muku da nishadantar daku a kullum da ko yaushe ku dai ku kasance dani kuma ku kasamce masu comment da sharyi akai akai ni kuma bazan gaji da danno muku wannan daddadan lbr ba
Plx
Vote
Comments
And
SharedBy oum now and old
YOU ARE READING
FADEELAH KO SAMHA
RomanceLABARIN FADEELAH KO SAMHA LBR NEHH AKAN WANI SAURAYI DAYA FADA TARKON WASU TSALA TSALAN YAN MATA GUDA BIYU DAYA DAI HAIFANTA SUN KASANCE BASU DA KOMAI SAI RUFIN ASIRIN UBANGIJI DAYA KUWA IYAYEN TA MASU HALI NEHH SHIKUMA SAURAYIN YA KASANCE SHIMA MAI...