End

115 6 2
                                    

Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_

Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHARJAY* @wattpad

Page 40

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya abubuwa da yawa sun sauya ciki kuwa harda samun dai dai tuwa tsakanin Afeefah da Siyama duk da ba wani magana suke ba hakan kuwa ba karamin kwantar da hankalin Fuad yayi ba.
     
Bayan wata 6
    Lokaci baya jiran mutum sai dai kai ka jirasa, gaba dayansu suna kebbi sunzo sallah babba gdan duk ya harmutse da hayaniyar yan kawo lefen Faty kaya Masha Allah sae son barka anyi komai cikin mutunta juna, Bayan yan kawo lafe sun tafi gdan ya rage hayaniya yara suna ta wasan su, jin kamshin abincin da aka shigo dashi ne part  din Hajja ya hautsina cikin Afeefah da gudu ta shige toilet din parlour sai kowa ya bita da ido, jin kakin aman da take yi ne ya saka Adda Maryam bin bayanta gaba daya ta galabaita sae amai take kamar zata fito da kayan cikinta da taimakon Adda Maryam ta gyara Bayan ta gama aman suka fito wadan ke parlourn we jera mata Sannu suke yi Adda Hadeexa ce tace "dama baki da Lpy?"
  Girgiza kanta tayi tace "aa wlh Adda warin abincin nan ne ya haye min kai" dariya tayi tace "a lallai Toh Allah ya raba Lpy"
    Adda Maryam tace "dama ni Ina ganinta nasan wlh ciki ne da ita dan gaba daya ta sauya" zaro ido waje Afeefah tayi tace "ciki kuma?" Dariya suka kwashe da ita da sauri ta mike sai daki Adda Maryam tabi bayanta tace "dama baki San kina da cikin bane" cike da kunya tace. "Ehh Adda" "ta shi mijin naki ya sani" tace "aa".
Wayar ta Adda Maryam ta karba ta dannawa Fuad kira ring biyu ya dauka jin muryar bata Afeefah bace ya saka shi gaida ta duk da bai San ko waye ba sai data gaya masa "Congratulations kanin mu your wife is pregnant sae dae bamu San ko wata nawa bane idan kazo sai kuje asibiti".
   Da sauri ya mike yan fadin "what Adda Maryam da gaske kike yi kuwa" dariya tayi tace "Allah da gaske Kai dai sai ka zo" daga haka ta kashe wayar.
     Mommy dake zaune tana kallon sa tace "Lpy dai ko naga kanata zabga murmushi ko aljannah aka kiraka aka gaya ma an maka albishir da ita" dariya yayi yace "aa mommy Bari dai Ina zuwa" bai tsaya jiran me zata ce ba ya fice daga gdan bai tsaya ko Ina ba sai gdan su Afeefah. Kiran wayarta yayi Bayan yayi picking yace "fito muje Ina waje" tace "toh" kamar zatayi kuka dan ba yanzu taso komawa ba, haka ta masu sallama ta tafi Adda Maryam na mata dariya, a waje yayi parking motar dan haka tana shiga yayi reverse sae da suka fara hanya tace "ina wuni" "Lpy ya gajiya" "alhmdllh" Ba wanda ya kuma cewa kala cikin su ita ta jinginar da kanta a seat din motar shi kuma hankalin sa na kan driving din da yake yi.

    Asibiti ya nufa Kai tsaye, Bayan sun isa ya dan taba ta dan har ya fara bacci ganin yayi parking ya sakata kallon sa sai kuma taga asibiti suke kallon tuhuma ta Bisho dashi kawai ya Basra ya bude motar ya fice, dole itama ta fito ya rufe motar tareda zagayawa gefen ta ya kama hannun ta, marairace masa tayi tace "nifa Lpy na qalau Allah kuwa" bai kulata ba har suka je office din dr Saudat, cikin sakin fuska suka gaisa ta basu guri suka zauna nan Fu'ad ya gaya mata abunda ya kawo sa da mamaki Afeefah ke binsa da kallo har ya kai karshe.
      Tambayoyi dr Saudat ta dan yima Afeefah kana ta kira wata nurse aka deba jininta dan ayi test. Tashin farko result ya nuna ciki ne a jikinta na wata biyu da sati daya. Hamdala ya shiga yiwa ubangiji da nuna tsantsar godiyar sa da Allah yayi masa badan yafi kowa ba ba kuma dan shi din wani ne ba harda kyauta yayi wa dr, ita kuwa Afeefah kunya ce ta kamata sai kasa tayi da kanta tana smiling, wai yau itace ake farin ciki dan ta samu ciki farin cikin ma daga mijinta Sulaiman ne ya fado mata arai lumshe ido tayi tana shafa cikin ta cikin wani irin yanayi. Hanunta ya kama suka fice daga office din Bayan sunyi wa dr Saudat sallama, Kai tsaye gida suka wuce cike da farin ciki baiyi Parking ko Ina ba sai part din mommy, ganin yanda suka shigo fuskar sa dauke da fara'a ita kuma Affeha kanta a kasa sai abun ya bata mamaki, su Waheedah ma dake zaune da kallo  suka bisu guri ya samu ya zauna a kujera Afeefah kuma ta rakube jikin kujera kanta kasa ta gaida mommy ta amsa "ni dai kun daure mun Kai wannan annashuwa haka da nake gani zaman fuskar ku haka" mommy ta fada.

𝐇𝐚𝐤𝐚 𝐧𝐚𝐚𝐚 𝐦𝐢𝐣𝐢𝐧 𝐲𝐚𝐤𝐞Where stories live. Discover now