Page 28

99 11 0
                                    

*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
         _(Nefarious Hubby)_

          Written by *NEESHAR.JAY*

          *NEESHEJAY* @wattpad

Page28

*Aslm Alkm sisters masu karanta book din nan ta wattpad Ina bai baki hakuri sbd koda nayi posting basa gani wattpad dina ya samu matsala and am still working on it so plss da wannan handle din zaki iya cigaba da samun littafin nan dama wanda zanyi nan gaba ga handle din nan *neesharjay* wannan shine sabon handle dina ku nuna min kauna ta hanyar following, liking da kuma commenting plsss. Also wadan da basu fara ba kuma suna so su karanta to ku duba ta wannan handle din *neeshejay* a nan zaku samu farkon sa da kuma sauran littafan dana rubuta a baya nagode*

Komawar Afeefah Abuja yasa damuwar ta fara gushe dan tana samun kulawa sosae gurin mommy da yan uwanta a kullum suna kokarin sun kata farin ciki shi yasa kullum suke tare da ita, komai take so ana mata ba abunda ta nema ta rasa gaba daya yanzu ta kara zama wata silent killer ko fira akeyi smiling ko dariya ne kawai nata sai wacca ya zama dole tayi magana take yi ba abunda ke damunta yanzu sai tausayin yar ta akullum ta kalle ta sai ta zubar da hayawe tana gaba daya ba haka ta tsara zaman gidan mijinta ba sai dai ba yanda ta iya da wannan kaddarar data riga fata. Matsala daya take fuskan ya a gidan kuma ba a gurin kowa bane sai Siyama matar Fu'ad tun abun na damunta har ya koma sai dai kawai tayi smiling amma har ta karaci zancen ta ko kallonta batayi hakan kuma ba karamin bata tan Siyama yake yi ba dama tun farko bata son Afeefah bata kaunar ta gaba daya jininsu bai zo daya ba gashi yanzu ta dawo gidan da zama duk da ba part din su daya ba kuma ita ba fita takeyi ba amma kishi take da ita haka kawai. Aikin banza ita Afeefah bata ma San tanayi ba bata saka abun a ranta ballantana ya dame ta.

Zaune suke gaba daya a parloun kasa kayan sa mommy tayi order ne suka iso katuwar jakar kayan dangin lace materials atampha da abaya ne kala kala kuma masu tsada Afeefah ta kalla tace "Zoki fara zaba tunda kece babba" tasowa tayi da niyar zuwa bakin kayan Siyama tace "Haba mommy tun da nice matar babban yayan su aini ya Kamata na fara dauka koya kace noor" ko kallon ta baiba ballantana ta saka ran zai amsa mata bata fuska tayi ta karasa kusa dashi tace "Haba wayar ka tafini ke nan fine" riko hannun ta yayi yace "sorry am going through an important conversation with my frnd ne me kika ce" bata fuska tayi tace "dama mommy ce tace wai waccan ta fara daukar kayan Bayan tasan kuma nice babba" mikewa yayi ya karasa gurin mommy ya duka ash material da wata atampha mai green and yellow sai lace mai manyan flowers pink and purple da abaya brown ya zabar mata kana ya mike yace "mommy wannan muka dauka" bata ce masa komai ba ta maida kallonta gun Afeefah tace "dauka kinji" smiling tayi ta fara dauka material peach sai atampha red dama shine best colour dinta ko lace red and golden ta dauka sai abaya royal blue tayi ma mommy godiya sosae kana ta mike su Waheedah suka dauka nasu cike da takaicin abunda Siyama tayi godiya sukayi suma suka fice daki.

Mommy kuma shiru tayi ta gani ko Siyama zata mata godiya amma shiru dama ba wannan bane karon farko daya fara mata kyauta bata godewa sai dai kawai ta karba kamar gadon babanta. Siyama kuma gani tayi gaba daya kayan da Afeefah ta dauka sunfi nata kyau sosae ranta ya soyu koda fu'ad ya mika mata kayan karba kawai tayi ta fice daga parlourn.

Bayan kwana biyu mommy na zaune kan bed rike da Ammi yayin da Afeefah ke gyara mata wardrobe dinta suna fira sama sama shigowar sa ya saka kirjin Afeefah dokawa da sauri kasa tayi da kanta Bayan ta saka kayan dake cikin hannunta ta nufi kofa mommy tace "Lpy kardai guduwa zakiyi" murmushi tayi tace "aa mommy na gama ne Ina so na hada mana dan waken kafin ki fito" mommy tace "toh shikenan" shi dai bai ce komai ba ya shiga faman dannar wayarsa sai data fita ne mommy ta ajiye Ammi ta shiga toilet daukar yarinyar yayi yana mata wasa har cikin ransa yake sonta ji yake inama yarinyar sa ce wani bacin rai ya ziyarce sa tunawa da bakar akidar Siyama ta rashin son haihuwa fito wa mommy tayi ta gansa zaune yana ma Ammi wasa har cikin ranta taji wani sanyi itama tana son yara amma ba yanda ya iya. Zaunawa tayi tace "ya dai fu'ad" dago da idonsa yayi yace "Ba komai mommy" kallon Ammi dake dariya tayi tace "hmmm yara abun so ne ga kowa Amma ban San meyasa wasu basa so ba yanzu fa akan wannan yarinyar ne mijinta ya muzgunata mata dan shi a nashi ra'ayin ba haihuwa" mamakin abun ya bashi dama a maza za'a samu masu wannan a kidar ne?" Nan mommy ta kwashe gaba daya abunda ya faru ta gaya masa sosae tausayin Afeefah ya masa dirar makiya furzar da iska mai zafi yayi yace "Allah ya saka mata" mommy tace "Ameen".

Parlour suka fito sukayi a lokacin har Afeefah ta gama hada dan wakenta daya ji kayan alatu kallo daya zaka masa ya shiga ranka, sama ta hau don kiran su Waheedah a tare suka sakko Bayan sun zauna mommy ta kalli fu'ad tace "a zubo maka ne" yatsine fuska yayi yace "aa nikam bazan iya ci ba" haka kawai Afeefah bata ji dadin yanda ya kalli abunda ta girki ba aiko a baki baiyi dadi ba a ido yayi kyau tunanin ta ne ya katse lokacin da mommy tace "Waheedah dauko tray sai muci gaba daya" mikewa tayi ta tafi lichen Afeefah kuma taje dining ta dakko Watermelon drink din data hada dazun ta dawo nan suka fara cin abuncin su suna fira shigowar Farouk rike da hannun Husna ne ya karade parloun da gudu tayi kan mommy ta fada kanta tace "I miss you so much mommy" mommy tace "same dear ya hanya" Husna tace "Lpy" fu'ad dake kallonta yace ke dallah ki daga ta idan kika karya mata kafa fa" mikewa tayi ta karasa gurinsa tayi hugging tace "Haba mana big bros" Ashraff ne ya shigo janye da trolley din su ya karasa cikin parlourn ya duka ya gaida mommy ta amsa tana tambayar sa ya hanya yace "Lpy" gurin fu'ad ya Kara ya duka ya gaida shi nan ya gaida kowa na parlourn sai a lokacin Husna ta kula da Afeefah da gudu tayi kanta tana "laaaaa Adda Afeefah yaushe kika zo?" Tace "na jima Autan mommy ya hanya" tace "Lpy me kuke ci haka nima zanci" mommy tace "toh dauko plate a kitchen" da gudu ta tafi dama Husna badai kiriniya ba duk da ta girma dan yanzu shekaran ta 12 amma bata ji har yanzu. Faruk kam zama yayi ya saka hannu yace "ni kam a nan zanci" duka Waheedah ta kai masa dan a kusa da ita ya zauna tace "tankon mata kawai" yace "Ehh din naji" dariya sukayi gaba daya Husna ta dawo da plate dinta Afeefah ta zuba mata kallon Ashraff tayi tace "kai baza kaci bane" yace "aa sai an jima bana jin yunwa ita ma Husna din hadama ce kawai irin nata amma nasan bata jin yunwa" cuno baki gaba tayi tace "yah ka ganshi ko" yace "kyale sa zoki zauna" kadan ya rage ta zauna kan Ammi da sauri fu'ad ya dauke ta ya watsa ma Husna harara yace "wai ke yaushe ne zakiyi hankali?" Kasa tayi da kanta tace "yah nifa ban kula bane" tsaki kawai yayi ya fara rarrashin Ammin dake kokarin fara kuka dama bacci take hakan yasa ya ajiyeta. Kallo daya Afeefah tayi masu ta dauke kai ganin kukan nata zai fara karfi yasa mommy kallon Afeefah tace "ke zoki karbe ta ki bata nono" kunya ce ta rufeta taji kamar kasa ta tsage ta shige Haba ya mommy zata ce ta bata nono gaban fu'ad kasa tayi da kanta bata motsa ba mommy tace "ikon Allah kema kunyar dan Fari zaki fara toh wlh bari na gaya miki an wuce wannan zamani da ake cutar da yara Kinga fu'ad gashi nan ni har a gaban surukata basa nono nake" dauke kai Fu'ad yayi yasha mur ganin mommy nason saka yara su raina sa ai kuwa mai zasu idan ba dariya ba sai dai kowa yana tsoron yayi ta fito fili. Mikewa tayi taje dining sum sum kamar munafuka haka ta karasa gaban sa ta saka hannu zata karbi Ammi hanun fu'ad ya taba nata da sauri suka dago a tare idon sa a cikin ya shine ya fara basarwa tareda dauke kai itama ta karbeta tayi hanyar daki mommy tace "ina kuma zaki je" jiyowa tayi kanta a kasa tace "mommy na koshi dama" tace "toh yayi". Husna kuwa matsawa tayi gurin Fu'ad tace "yah babyn aunty Siyama ne?" Yace "no" dan wake daya ta dauka takai bakin sa yace "bazan ci ba" tace "lallai Yaa kayi missing wlh da dadi sosae bude baki na saka ma" bude bakin yayi ta bashi ya lumshe ido da gaskiyar ta kam da dadi a tare suka cinye na plate dinta harda Kari. Lol

Vote
Comment
Share

*Lioness👑*

𝐇𝐚𝐤𝐚 𝐧𝐚𝐚𝐚 𝐦𝐢𝐣𝐢𝐧 𝐲𝐚𝐤𝐞Where stories live. Discover now