Part 38

108 8 2
                                    

Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_

Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHARJAY* @wattpad

Page 38

Mutuwar tsaye siyama tayi a gurin saboda shock din da ya Kamata bata tabbatar cewa da gaske ne ba'a mafarki ba sai da yayi tsaki ya fice wani irin kuka ne ya kwace mata ta zauna a gurin tana rugar kuka kamar wacca akayi wa mutuwa sosae ba zafin marin bane ya dameta daga hannun da yayi ne ya mareta a gaban kishiya idan ta tuna hakan sai ta kuma fashewa da wani matsanancin kuka, har Suhail ya dawo daga part din mommy tana zaune a gurin shigowar sa ne yasa ta sauke wata katuwar ajiyar zuciya ta sauke tare da mikewa ta shige daki shi kuwa ya bita yana mitar zaije gurin su Deedat  bata kulasa ba ta shige toilet ta wanke fuskar ta ta fito gaban mirror taje ta gyara fuskarta kana ta bude wardrobe dinta ta dauki vail dinta da handbag taja hannun Suhail suka fice daga gidan. Direct gidan su ta nufa tana zuwa ta fashe da kuka cike da tsoro mamanta ke kallonta tana tambayar Lpy sai data saka mata tsawa kana ta dawo cikin hayyacinta ya share hawaye ta koma sauke ajiyar zuciya kana ta fara magana "mama wlh tunda akayi auren nan wulakanci iri iri Fuad kemin yau harda daga hannu ya mareni" ta karasa tana fashewa da wani kukan, kallon ta maman take yi kana ta sauke numfashi mai aikin su ta kira tace taje da suhail ta daga masa noodles Bayan tafiyar su ne ta kalli siyama dakyar ttace "Siyama dago ki kalleni" dagowa tayi ta kalli mama taga fuskarta ba alamun wasa dama tasan maman ta bata daukar iskanci yaro, "nasan mijin ki bazai mare ki a banza ba tsawon shekarar da kuka dauka kuna zaman aure, kullum shine ke hakuri dake kin San nasan wannan toh bari kiji idan ma zugar kawayenta ko na yan uwanki kike dauka kinyi a banza dansu suna can gdan mazajen su suna zaman lpy amma ke kina nan kin daga hankalin ki mutum nawa ne akayi wa kishiya kuma suke zaune Lpy baka jin kansu, kece babba kece zaki jagoranci gdan ki tunda ke kika San yanda kika fara tafiyar da tsarin sa, kishiyar ki ba buduwar wa bace idan kika yi wasa sai dai ki dinga hango Fuad daga nesa, shi aure dan hakuri ne dama duk wanda yace maki yau yana zaman lpy 100% a gidan sa karya yake maki siyama ba wanda yake zama ba tareda yayi hakuri ba kuma kece mace dole kece zakiyi hakuri da duk abunda ya faru toh amma ke ki godewa Allah mijin ki na sonki ba abunda ya rageki dashi kiji tsoron Allah kiyi masa biyayya dan wlh idan ba haka ba Allah bazai barki da hakkin sa ba a matsayina na uwa nake baki wannan sharawa Allah na gani na fita hakkin ki tashi kije Allah baku zaman lpy".
  Ai mutuwar zaune Siyama tayi a gurin tana kallon mama tace "Ehh tashi kuje nasan baima San kin fito ba kuma idan ya dawo ki bashi hakuri wannan umarni ne ba shawara ba" mikewa tayi jiki ba kwari mama ta kwala kiran Suhail ya fito suka tafi.
  Bata koma gida ba ta wuce gdan babbar yayar su itama dae shawarar data bata kenan dan tana da kishiya ba yanda ta iya sai hakuri ta koma gda.

.
    .
.

Afeefah POV

Koda taga reply dinsa smiling kawai tayi tana mamakin kanta sae guraren 12 ta daura girkin rana kafin ya dawo, Bayan ta gama ta haura sama tayi sallah tare da kwanciya sai bacci.
    Kiran sallahr la'asar ne ya tada ta daga baccin da take yi dakyar ta sauka a gadon ta shiga toilet sai data fara watsa ruwa kana ta dauro alwala ta fito sallah ta fara gabatarwa Bayan ta idar ta zauna bakin mirror ta fara shafa mai sai ga kiran Waheedah ya shigo wayar ta Bayan sun gaisa take sanar da ita Ammi nata kuka kana kiran mommy sae da taji kwalla ta taru mata a ido tace "toh Waheedah ya zanyi insha Allah dai Zan shigo zuwa jibi bani ita" tace "toh" mika ma Ammi wayar tayi Bayan ta saka wayar a handsfree jin muyar mommyn ta tana kiran sunan ta yasa ta saki dariya tana kallon wayar "Ammi na karki damu kinji mommy's love zanzo kinji" kana ta maida alakar wayar fa Waheedah "toh aunty wahee sai munyi waya bari na saka kaya" sallama sukayi ta shirya cikin doguwar riga ta wani material mai taushi bata yi kwalliya ba kwalli kawai ta shafa bako powder ta sauka kasa.
  

Fuad hidimar gaban sa ya cigaba kamar komai bai faru ba sai yanzu ne yake ganin amfanin mata biyu idan wannan ta bata ma wannan zata faranta ma, sae da yayi sallar la'asar kana ya shigo gda a matukar gajiye, key dinsa ya saka ya bude kofar ya shiga da sallama dauke a bakin sa ciki ciki, baiyi tunanin tana parlourn ba sai ji yayi ta amsa masa tana mikewa zaune daga kwancen da take, samun kansa yayi da sakar mata lallausan murmushi  itama ta mayar masa tana yin kasa da kanta, karasa shigowa yayi sai ta mike tana sannu da zuwa ya amsa yana zama yace "washhh" tace "sannu" kitchen taje ta dakko plate da cup ta dawo dining ta bude fridge ta dakko ruwa da drink ta kawo masa Bayan ta zuba masa a cup ta mika masa harda hannun ta ya hada daya zo karba da sauri ta dago kanta shi kuwa ya basar yana shan ruwan sa sae da ya gama kana ya mike sakale da hannun ta suka haura sama, zaunar da ita yayi bakin bed ya hau cire kayan sa hakan yasa ta mike ta shiga toilet dan hada masa ruwan wanka, zata fito kenan sai gashi ya shigo matsa masa tayi ya wuce sai taga ya juya ya rufe kofar da sauri tayi kasa da kanta lokacin daya fara kiciniyar cire mata rigar jikinta bayanda ta iya dole ta hakura sukayi wankan daya zama shiriri ta suka fito Bayan sun shirya suka sauka kasa, a tare suka ci abinci da suka kammala ya mike ya koma parlour ita kuma ta shiga tattara kayan da sukayi amfani dashi ta dawo parlour zata zauna ya miko May hannu hakan yasa ta karasa gurinsa ya jawo ta ta fado jikinsa tana karamar kara, Jan kumatunta yayi yace "kin cika raki" turo baki tayi ba shiri taji bakin sa cikin nata.
    Sanin da tayi ba part dinta yake ba sae ya saka bata wahalar da kanta ba gurin girka abincin dare Bayan ta idar da sallahr isha tayi shirin bacci ta kwanta abunta. Sama sama ta fara jin motsin mutum a kanta dan baccin ta baiyi nisa ba bude idonta tayi ta gansa zaune yana mata addu'an bacci lumshe ido tayi ta kuma budewa ya mata kiss a goshi ya mike zai fice, sai taji kewa ya kamata rabon data kwana ita kadai tun tana gidan Sulaiman, riko hannun sa tayi ya dawo ya zauna sai ta mike zaune tayi masa peck ta rungumesa cikin muryar wanda ya fara bacci tace "Allah ya tsare min kai da tsarewar sa daga wannan daren zuwa wayewar gari Allah ya baka kariya daga sharrin mutum da aljani" sae data sake sa kana tace "Allah tashe mu Lpy" jiki a sanyaye ya amsa mata da Ameen ya mike ya fice Bayan ya kashe mata wuta. Kwalla taji sun taru mata a ido tana jin jina wannnan kaddararta ta ita dae bazata taba auren mijin ita kadae ba sae dae mijin wata, kewar yarta ne ya fado mata a haka dae har bacci ya tafi da ita.

Fuad kuwa cike da farin ciki ya karasa part din siyama sae da ya rufe ko ina kana ya kashe wutar parlour ya fara leka dakin Suhail ya hangosa yana ta bacci abinsa addu'a ya masa ya fito kana ya shiga dakin Siyama, itama dai harta kwanta da kayan ta a jikin ta bata cire ko sarka ba chatting ma take yi hankali kwance, koda ya shigo ko sallamar sa bata amsa ba bata nuna taji shigowar mutum ba shima sai bai bi ta kanta ba ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin kayan baccinsa,
  Sae da ya kwanta ne yace "Siyama bazaki tashi kiyi shirin kwanciya ba" tabe baki tayi tace "wane shiri kuma zanyi Bayan wanda nayi" yace "ai naga baki saka kayan bacci bane ko a haka kike nufin zaki kwanta" "Ehh a haka nake ra'ayin kwanciya yau ko kana da matsala da hakan ne" baice mata komai ba ya juya yana jinjina kalar wannan banzan kishin na mata............

Follow
Vote
Comment

*Lioness👑*

𝐇𝐚𝐤𝐚 𝐧𝐚𝐚𝐚 𝐦𝐢𝐣𝐢𝐧 𝐲𝐚𝐤𝐞Where stories live. Discover now