Page 36

85 6 1
                                    

Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_

Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHARJAY* @wattpad

Page 36

A tsaye ya samu siyama tana ta faman kai komo da alama ko sallamar da yayi bata ji ba gyaran murya yayi hakan yasa ta jiyo da sauri ta nufeshi ta fada jikinsa tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka mai taba zuciya sosae yake jin kukan nata har cikin ransa tunda aka fara maganar auren nan yana kula da duk wani take taken ta amma ya share, tausayi ta bashi ya rungumota jikinsa har suka zauna baice mata komai ba tana lafe dai a jikinsa. Sai da tayi mai isarta kana ta tsagaita cikin sheshsheka ta fara magana "Fu'ad Wlh ina kishin ka zuciyata baza ta iya daukar abunda zai faru a daren yau ba bazan iya ba Fu'ad ka tausaya mun dan Allah bana jin zan iya sharing dinka da kowa".
    Shiru baice mata komai ba, kuma badan bashi da abunda zaice ba sai dan maganar bata masa kama data masu hankali ba, dago idonta tayi ta kallesa taga nashi idon a lumshe suke sai ta kuma lafewa tana sauke ajiyar zuciya, ita kadai tasan yanda zuciyar ta ke tsalle taba barazanar fasa kirjinta ta fito, tana tsakanin kishin mijinta tabi duk shawarar da yan uwanta da abokanai suka bata amma ba wanda yayi aiki bata San me zatayi ba, dama haka kishi yake? Kuma mamanta ta yarda aka kara mata kishiya? Duk wannan tambayar tana yinsu ne a cikin ranta.
   "Ina suhail?" Taji tambayar sa ta daki kunnen ta a dakile tace "yayi bacci" daga haka sukayi shiru har kusan 11 saura daga ta yayi daga jikinsa daki ya kaita sae daya tabbatar ta saka kayan baci ta kwanta ya mata addu'a yana ajiye mata dayar ledar daya shigo da ita "sai da safe" fitowa ne kawai zuciyar ta bata yi ba jin abunda yace kuka ta fashe masa yana jinta amma ya share ta ya wuce. A nan ta durkushe tana kara fashewa da wani sabon kuka.

........................✨

Duk a takure take kasancewar bata shiryama baccin ba ya fisgeta, ganin ba kowa a parlour ya saka shi yin addu'a ya rufe kofar parlourn sai da ya leka ko Ina na kasa kana ya haura sama, dakin sa ya fara shiga ya rage kayan jikin sa ya fada toilet yayi wanka ya fito spray kawai ya fesa ya saka jallabiya ya fito, da sallama a bakin sa ya tura kofar dakinta ya shiga can kan gado ya hangota kwance tana bacci duk ta takure, samun kansa yayi da sakin murmushi ganin yanda take baccin a hankali ya karasa gurin gadon ya zauna a hankali sai da ya gama kare mata kallo kana ya dagota a  hankali zuwa jikinsa rungumeta yayi yana ajiyar zuciya tare da godewa Allah, shi dai yasan ba son yarinyar nan yake ba amma dai yana tausayinta. Afeefah kuwa lafewa tayi a jikinsa ta kara gyara kwanciya tare da cigaba da baccin ta hankali kwance, (su Afeefah an samu jikin Mayan maza lol!)
Gyalen dake jikinta ya fara cirewa hakan yasa ta dan motsa cire sa yayi gaba daya ya ajiye ya mike tsaye da ita har toilet a bakin sink ya tsaya da ita ya deba ruwa ya shafa mata fuska bude idonta dake cike da bacci tayi ta zuba masa su, da sauri ta janye jikinta ganin wanda ke tsaye kusa da ita gaba daya kunya ta kamata kasa tayi da kai, kallonta yayi na second 2 ya dauke kai "kiyi alwala ki fito Ina jiran ki" kanta kawai ta daga masa. Wata katuwar ajiyar zuciya ya sauke Bayan ya fice kusan 10mins sai gashi ta fito a lokacin har ya gaji da jiranta ya shimfida sallaya yana danna wayarsa. Akwatin ta ta bude ta dakko sabon hijab dinta ta saka sai kuma tayi tsaye, shi mamaki ma take bashi ji yanda take yi kamar wacca bata taba aure ba dan tabe baki yayi ya mike tsaya ya hau sallaya hakan yasa itama ta tsaya a Bayan sa ya jasu sallah Rama's biyu kamar yanda manzon Allah ya umurta. Bayan sun idar ya masu addu'a mai tsawo wacca rabi gaba daya Afeefah gyangyadi kawai take zubawa ganin haka ya tsagaita. Ledan daya shigo dashi ya sauka ya dakko tare da plate koda ya dawo harta kwanta a gado "Amma yarinyar nan kasa ce wlh" ya fada a zuciyar sa ajiye ledan yayi ya tashe ta saboda baccin dake idonta yasa tace "ya fu'ad a koshe nake" bai matsa mata ba ya bude furar daya siyo yasha kadan sai kunun aya daya ji kwakwa da dabino yasha sosae nan da nan wata kasala ta saukar masa, ajiye kayan yayi a bedside ya kashe wuta sae bedside lamp kawai daya bari a kunne shima na gefe daya hakan yasa dakin yayi so dimmm. Gadon ya haye yana jawo ta ga jikinsa, ita kuwa abu biyu ya rufe ta na farko tsantsar kunyar yayan ta na biyu kuma bacci a hankali ta fara jin ya cire mata hijab sosae gabanta ke faduwa bata kara tsorata ba sai da taji tafiya tayi nisa kuka ne kawai batayi ba a wannan daren.
    Da asuba shi ya fara tashi daga ta yayi daga jikin sa ya daura kanta a pillow sai da ya mata light kiss a goshi kana ya sakko daga gadon toilet ya shiga kusan 30mins sai gashi ya fito tada ta yayi dan an fara tada ikama dakyar ta bude ido yace "tashi kiyi sallah" Kai ta daga masa yace "karfa ki kwanta tashi" daga haka ya fice, ita kuwa kunya ce ta hanata mikewa sai da ya fita ta zuro kafafunta dakyar ta mike zuwa toilet sae data fara gasa jikinta tayi wanka ya dauro alwala ta fito raka'atanul fajir ta fara yi kana ta gabatar da sallar asuba har ya dawo tana zaune a gurin tana azkar zama yayi bakin gado yana kallon ta sai daya gama kana ta gaidashi ya amsa ya Kara da "ya kwanan amarci" a kunya ce tace "alhmdllh" kanta a kasa.
   Kwantawa yayi tare da rufe ido yace "zoki jamin blanket" turus tayi tana kallon sa a ranta tace "lallai ma ya fu'ad din nan" mikewa tayi ta karasa gaban gadon ta saka hannu zata rufe shi ya jawo ta ta fada kansa kanta ya dan bugu da fuskar gadon "auch" ta fada tana shafa gurin dariya yayi kasa kasa yace "silky girl" turo baki tayi tare da kauda kanta gefe kuruciyar ta zalla ta fito smiling kawai yayi ya gyara mata kwanciyar ta a jikinsa ya rufa masu blanket bawai dan tana jin bacci ba kawai dai ta kwanta ne. Sabo da zuwa skl kwana biyun nan ne yasa bata iya baccin safe yanzu sai da yayi bacci kana ta mike a hankali ta dauke kayan daya ajiye jiya ta fice kitchen da su, sai yanzu ne ma take kallon tsarin gdan yanda yake sosae  ya mata kyau sosae breakfast ta dora Tea da sai bread din da tayi toasting da kwai data soya.
  Ganin fashion bulbs din da aka saka mata irin masu  white stones din nan ne wanda ake sakawa a maimakon fan, da yake irin shi ne a parlourn gdan su sai tayi connecting din Bluetooth speaker din ta kunna karatun qur'an ta rage murya sosae, sama ta haura cikin sanda ta shiga toilet ta fara wanka kenan taji ana knocking kofa sharewa tayi ta cigaba da wankan ta.
    Fuad kuwa dakyar ya iya bude idon sa ganin bata kusa dashi ne ya saka shi mikewa ya nufi toilet bude kofar yayi ya ganta tana wanka ita kuwa kwala ihu tayi tana durkushewa gurin tsaki yayi ya fice zuwa kasa, koda ya bude kofar Siyama ya gani tsaye cikin doguwar riga ta atampha dan kwalinta kuwa ta daura sa ne a kanta ta rufe kirjinta dashi. Kallon mamaki yake binta dashi ganin haka yasa tace..........



#TeamFuad
#TeamAfeefah
#TeamSiyama

*Lioness👑*

𝐇𝐚𝐤𝐚 𝐧𝐚𝐚𝐚 𝐦𝐢𝐣𝐢𝐧 𝐲𝐚𝐤𝐞Where stories live. Discover now