Page 34

74 7 2
                                    

Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
         _(Nefarious Hubby)_

          Written by *NEESHAR.JAY*

          *NEESHARJAY* @wattpad

Page 34



Bayan sati biyu

Su Afeefah an gama exams alhmdllh kuma sun fito da result mai kyau Faty ma ta gyara CO din da take da shi, sosae Afeefah ke jin dadin zaman gidan su yanzu duk da gurin sati daya aka basu saboda zaman gidan da akayi na wata bakwai.
      Ammi ma ta kara wayau har ya fara iya tafiya, lokacin da suka je Bagudo hutu Hajiya tace a barta a nan hakan yasa Bayan sun dawo Afeefah ya kuma dibar wasu kaya ta aika mata ko Ba komai ta dan huta kafin ta dawo duk da ko a gidan ma ba gurin ta take zama ba, sai dai yanzu wahalar skl dazai kara masu yawa tunda a cikin 2months zasu karasa so dole abubuwa zasu hade masu.

•••••••••••••••••💙

Zaune yake cikin shirin sa na fita office tea cup ne a hannun sa yana sipping a hankali yayin da gaba daya idon sa na akan wayar sa da yake  amfani suhail kuma na daga kan dining yana zubama mai aikin su rikici shima shirye yake cikin uniform din sa, sai faman rigima yake ya abincin da ake bashi a baki ma yaki karba gaba daya abunda suke yi akan idon fu'ad amma zaka rantse bai San suna yi ba wannan hali na Siyama na bata mashi rai duk safiyar Allah abunda ke faruwa kenan kullum mai aiki zata hada masu breakfast tayi ma Suhail wanka ta shirya shi yayin da ita kuma tana can tana sharar bacci dan guntun tsaki  yana mikewa tsaye bedroom din sa ya shiga ba jimawa y fito a lokacin suhail ya gama breakfast, hannun sa ya rike suka fita part din mommy.
   A daki ya same ta ta fito daga wanka tana shiryawa, gaisawa suka yi Bayan ya zauna a bakin gado suhail ma ya gaida ta shiru yayi na kusan minti uku yana tunanin ta Ina zai fara gaya mata abunda ya kawo sa , mommy kuma ganin kamar a kwai magana a bakin sa yasa tace "Lpy dai ko?"
Kasa yayi da kai kana yace "mommy dama maganar yarinyar nan ne" duk da ta gane Afeefah yake nufi bai hanata tambayar shi ba "Wace yarinya kenan ko siyama?"

Yace "aa Afeefah"

Tace "ohh ashe kasan sunan ta toh meya faru?"

Kara kasa da kai yayi yace "mommy inaga ya Kamata ayi magana da iyayen ta tunda na gama komai"

Yar karamar dariya mommy tayi tace "toh shikenan duk yanda mukayi zan gaya maka" godiya ya mata ya mike sis fice sai da ya fara ajiye suhail a skl kana ya wuce office.

________Afeefah💕

Hankali kwance take yin komai kamar komai bai faru ba sosae ta mai da hankali akan karatun ta gashi yanzu har sun ci wata daya saura daya. Washe gari Friday ta shirya tsaf zuwa gdan Adda Maryam dan bata jin dadin jikin ta kwana biyu sosae take laulayin sabon cikin da take dashi, Ammi da satin ta daya da dawowa kuwa a gurin Aunty ta barta ita kadai driver yakai gidan.
    Koda taje gidan Yah ukasha na nan shima daga gani ma daga sallahr juma'a ya dawo Bayan sun gaisa yake mata wasa "amarya amarya har kin fara wani kyalli fa"

Dariya kawai tayi dan bata gane me yake nufi ba, Adda Maryam ma dariya tayi Bayan ta zubar da yawun bakinta tace "ai kuwa dai nan da sati hudu dan Abba yace baya so a dauki lokaci tunda dai na gidane basai an tsaya bincike ba"
   Da sauri ta dago kai ta kalli Adda Maryam dake tafawa da ukasha cike da firgici tace "Adda Maryam wai maganar me kuke yi ne?"
Kallonta tayi shekeke kana tace "kaji yar rainin hankali toh duk boye boyen ki dai wannan ta riga ta fito a toh" shiru tayi tana sauraren sautin bugun zuciyar ta  da sauri ta mike kamar wacca aka tsikarama allura hannun Adda Maryam ta kama tare da cewa "Adda kar dai Yah fu'ad kuke magana"

Hararar wasa ta maka mata kana tace "toh dama kin ajiye wanine Bayan shi?" Shiru tayi tare da komawa ta zauna kanta a kasa tama kasa cewa komai gaba daya yinin ranar haka tayi sa sukuku ba abunda tayi sai aikin tunani, Bayan ta koma gd ma dakyar ta samu ta dan karanta wani abu.
  Ranar Sunday da kiran Abba ya riski kunnenta ba karamar razana tayi ba dakyar taja hijab Bayan kusan minti 20 da kiran, a hankali ta tura kofar parlourn ta shiga kamar wacca kwai ya fashewa a ciki bakinta dauke da sallama.
    Abba dake zaune shida yah Ashir ta gaida Bayan ta zauna can gefen kujera. Kallonta yayi dakyau yace "Afeefatu kin San ke ba yarinya bace kina da hankali dan kina iya bambanta tsakanin abu Mara kyau da Mara kyau toh dan haka bazan miki dole ba dan yanzu ke ba yarinya bace ko annabi yace mu zabama masu maza na gari zaurawa kuma a basu zabin su toh dan haka ki gaya min kina son dan uwanki fu'ad ko kuwa?"
     Sosae kalmar zaura ta taba ta abunda take gudu kenan kalmar data fi tsana a duniya yau itace ake kira da ita shiru tayi bata ce komai ba ta dai kuma yin kasa da kanta...........


*Hi lovely 😊 people am back again insha Allah, am done with my exams and it's was a successful one addu'an ku yayi aiki insha Allah Allah ya karba.*
  *By God zan cigaba da maku posting duk da mun kusa gamawa dai*❤️ thanks for your prayers


#TeamAfeefah
#TeamFu'ad
#TeamSulaiman


*Lioness👑*

𝐇𝐚𝐤𝐚 𝐧𝐚𝐚𝐚 𝐦𝐢𝐣𝐢𝐧 𝐲𝐚𝐤𝐞Where stories live. Discover now