Page 39

123 11 7
                                    

Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
         _(Nefarious Hubby)_

          Written by *NEESHAR.JAY*

          *NEESHARJAY* @wattpad

Page 39

Washe gari Bayan ta dawo daga sallahr Asuba wanka yayi ya shirya ko kan ta Siyama dake kwance tana bacci bai bi ba ya fice daga gdan yau ko part din mommy bai leka ba.
   Afeefah kuma kamar yanda ta saba Bayan ta gama gyara part dinta tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga atampha ta yafa karamin vail ta wuce part din mommy sosae suka sha fira sai kusan sallahr azahar kana ta koma part dinta Bayan tayi sallah ta bi lafiyar gado sai bacci.
  Fuad kuwa Bayan ya gama aikin da daddy ya saka shi ya dawo gida zuwa jibi zasu koma Abuja gaba daya shiyasa yake so su gama shirun su kafin jibin. A matukar gajiya ya shiga part din Siyama da sallama ciki ciki tana kwance a sofa tana kallo itama a ciki ta amsa sallamar sa tana kara gyara kwanciyar ta zama yayi yana fadin "washh Allah" ko kallon sa bata yi ba hakan kuma ba karamin bata masa rai yayi ba sai kawai ya danne yace "sannu da gida siyama ina Suhail?" Banza ta masa yace "ina Suhail nace maki" nan ma bata kulasa ba tsawar daya daka mata ne ya sakata saurin mikewa zaune tace "yana part din mommy" yace "dama ashe iskanci ne kina jina kika yi shiru". Kasa tayi da kanta yace "bani abinci" turo baki tayi shikuwa ya tsura mata ido a hankali tace "ban girka ba" mamaki ne ya cika sa sai ya furzar da iska ya gyara zaman sa yaci serious "Siyama" ya kira sunan ta tace "na'am" sai da ya kirata sai uku kana yace "so nawa Na kira sunan ki" tace "uku" yace "ki maida hankalin ki jikin ki bana son na miki abunda bazaki ji dadina ba duk abunda kike min tsawon lokacin nan Ina taraki ne wlh duk ranar da kika Kai ni bango sae na hankado ki, naga kina so ki mai dani karamin mutum ko duk wannan haukan banzan na kishi ba abunda zai ma maki a guri na sae zubar da girma Ina mai tabbatar miki daga ranar da kika bari na daina ganin girman ki wallahil'axim bazaki ji dadin zama dani ba bana son abunda zai bata miki rai ya saka ki jin dan na kara aure yasa nake miki haka ke baki San kawai ci bane, a ajiye maganar aurenta dake kaina yar uwata ce ta jini kina tunanin bazan ji haushi ba idan naga kin wulakanta ta Ina mai baki shawara ki zubar da duk wannan makaman yakin naki idan ma shawara ake baki, bawai bazan iya rabuwa dake bane aa kawai Ina tausaya miki ne idan kikayi wasa kina kallo kamwarki zata kwaceni a hannun ki duk iya shekarun sa mukayi tare kin fi kowa sanin halina ni mutum ne mai tsananin son kulawa idan kika yi wasa zaki rasani ne na gaya miki gwanda ma ki daina wannan abun ki dawo hayyacin ki ku zauna Lpy na tabbata idan ba shiga harkar ta kikayi ba bazata miki rashin kunya ba kece babba ki kama girmanki" daga haka ya mike ya fice abunsa ya barta da tunani kala kala a cikin zuciya.
   Part din mommy ya nufa a can yaci abinci Bayan ya gama suka fara fira har Waheedah da Faruk da shigowar su kenan suka isa parlourn, Bayan sun gaisa Fuad ya mike ya fice.

       Washe gari da safe Siyama ta tafi gida a bisa umarnin Fuad akan suje su masu bankwana Afeefah kuma bata fita ba sai kusan 12pm, sosae yan gidan su suka dane ta suna mata oyoyo da nuna jin dadin ganinta ita kuwa sae dariya take, part din Hajja suka fara shiga Bayan sun gaisa ta shiga part din mama daga nan kuma part din Aunty ta shige abunta suna ta fira abunsu, sai Bayan magrib taje part din Abba suka gaisa ya Kara mata nasiha sosae kana ta koma part din aunty. Tana ta yiwa Ammi wasa ita kuma sai dariya takeyi, sae kusan 9 Fuad yazo daukar ta Bayan sunyi wa mutane sallama suka tafi cike da kewar mutanen gida.

Part din mommy suka fara shiga Bayan sun gaisa ya fito tare da Waheedah dan ta taimaka mata ta gyara kayanta kafin fuad din ya shigo, akwati hudu ta koda da kaya ta share ko Ina sukayi mopping sauran bedrooms din ta rufe su Bayan ta ajiye komai inda ya Kamata kusan 11 sae gashi ya kuma shigowa hakan yasa Waheedah yi masu sai dai safe ta fice abunta, ruwan wanka ta fara hada masa kana ta ciro masa kayan bacci ta ajiye, kasa ta sakko yana kwance a sofa ya lumshe idon sa a hankali tace "yah tashi kayi wanka" bude idon sa dake cike da bacci yayi kana ya mike a matukar gajiye ya haye sama, kitchen ta shiga ta hada masa coffee da toasted bread bread guda daya ta daura a tray ya kai masa, a lokacin ya fito yana daure da towel dauke kanta tayi ta ajiye masa ya fice zuwa daki.
Bayan ya kammala yayi shirin kwanciya ya fice zuwa dakin ta basu jima ba bacci ya dauke su.

         Washe gari Bayan Faruk ya kwashi kayan su gaba daya ya kai tasha aka saka a motar kasuwa zuwa Abuja, Afeefah kuma ta kara Kimtsawa haka ma Siyama suka zauna zaman jiran lokacin tafiya, misalin 5pm jirginsu ya daga zuwa Abuja,
Kowa part dinsa ya nufa ganin Fuad ya nufi part din Afeefah duk sai siyama taji ranta a matukar jagule badan shida kansa ya fada mata magana jiya ba da wallah ba abunda zai sakata gyarama yarinyar nan zama kuma tana son Fuad bazata iya rabuwa dashi ba hakan yasa ta shiga hayyacin ta sai dai ta dauki alwashin bazata dinga shiga harkar ta ba ko magana bazata dinga mata ba. Part dinta ta shige ita da suhail ganin gurin da yar kura yasa ta kira mai aikin ta ta sanar mata dawowar ta dan bazata iya aikin ita kadai ba.
      Afeefah kuwa sosae ta yaba da part din nata ba karamin kyau ya mata ba sae hamdala gakewa ubangiji, bedroom din ta fara lekawa sai da ta shiga ko Ina kama ta shiga dakin da taga Fuad ya shiga kaya ta samu yana cirewa toilet taje ta hada masa ruwan wanka ta fita ya shiga, itama dayan bedroom din ta shiga ta ajiye kayanta ta zauna duk da tana son yin wanka sae dae bata Bayan sakawa dan kayansu bae kae ga isowa ba. Ganin zaman ya ishe ta yasa ta fito ta nufi part din mommy kayan girki ta nema ta koma part dinta boiled yam ta dora ta nufi daki dan yin sallah tana cikin yi ne taji ana shigo da kaya Bayan ta idar ta leke taga Fuad ne tsaye sae idi mae gadi dake shigo da kayan daki ta koma Bayan taji fitar su ne ta fito ta shige kitchen aikin ta ta karasa ta gama ta hada komai ta jera a dining kamanta shige daki , zaune ta same sa bakin gado yana danna wayarsa sannu tayi masa ta hau cire kayan ta kallo daya yayi mata ya dauke kai cire kayan tayi ta ajiye su inda ya dace kana ta shige toilet wanka tayi tare da dauro alwala ta fito bata same sa a dakin ba hakan yasa ta saka doguwar riga sabuwa ta bacci cotton kana ta gabatar da sallahr isha.
  Shap shap ta karasa shiryawa ta fito ganin baya parlour yasa ta leka dakin sa ganin yana shafa mai yasa ta karasa shiga ya ciro masa kayan baccin sa ta fesa turare kana ta fice. Abinci ta hada masa Bayan ya fito yayi dinner suka zauna suna kallo sai kusan 10 ta mike zuwa daki dan bacci take ji, Fuad kuwa sai kusan 11 ya shige shima..........

𝐇𝐚𝐤𝐚 𝐧𝐚𝐚𝐚 𝐦𝐢𝐣𝐢𝐧 𝐲𝐚𝐤𝐞Where stories live. Discover now