Page 37

100 10 1
                                    

Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
         _(Nefarious Hubby)_

          Written by *NEESHAR.JAY*

          *NEESHARJAY* @wattpad

Page 37

Ganin kallon da yake mata ne yasa ta marairaice idanun ta da suka chanza kala zuwa ja sbd tsabar kukan da tayi jiya da dare ko bacci bata yi ita kanta bata taba sanin tana tsakanin kishin mijinta ba sai a daren jiya sai a jiyan ne ta tabbatar da son da take yiwa Fuad is unconditionally and incomparable, kasa tayi da kanta tana matso kwalla ita kanta bata San daliin zuwan ta kawai tsintar kafafun tayi suna tafiya kuma bata tsaya ko Ina ba sai nan, jin tayi shiru ne yasa shi cewa "idan baki da abin cewa zanje in kwanta bacci nake yi kika tado ni" dago idon ta tayi ta kallesa jin abunda ya fada wato ma haka zai ce mata samun kanta tayi da yin karyar da ita kanta sai da mamaki ya kashe ta "dama zan tambaya ne me zan dafa maku na breakfast?" Mutuwar tsaye yayi yana kallon ta da tsantsar mamaki sae kawae yayi smiling yace "anything you can or feel like doing" kanta kawai ta gyada tana nadamar abunda ta furta ta juya ta tafi, sai da yaga ya shiga part dinta kana ya koma ciki yana jin jina kishi irin na mata.

     Afeefah kuwa ganin baya cikin dakin koda ta fito tayi tunanin ko yaje dakin sa ne daya dawo daga duba kofa sae kawai ta zauna daga ita sai towel  bakin mirror tana shafa mai, Fuad kuwa wayar ta ya dauka dake parlour ya duba time 9:12am tsaki yayi ya dan kara murya kadan Kamata haura sama. Bedroom din ta ya fara shiga ya hangota tsaye tana duba kayan da zata saka cikin wardrobe, jin motsin bude kofa yasa ta juyo da sauri ganin sa tsaye yana kallonta yasa tayi kasa dakai gaba daya kunya ta rufe ta dan tabe baki yayi ya juya ya koma dakin sa wanka  yayi ya shirya cikin wani tissue yard sky blue color sae bakar hular daya saka da wristwatch dinsa na Rolex, ya fito sai baza kamshi yake yi, dakin ta ya leka yaga bata ciki sae kamshin turaren dake tashi lumshe idon sa yayi ya rufe kofar ya sauko kasa.
  A dining area ya hangota tana shirya breakfast, guri ya nema ya zauna zaman couch din parlour ya zauna yana duba wayar sa Bayan ta gama ta dago tana kallon sa a hankali ta furta "Masha Allah" Sulaiman ne ya fado mata a rai da sauri ta yakice tunanin sa tana astagfurullah a ranta "ya Fuad ga breakfast din" ba tare da ya dago ba yace "ok".
  Sae kusan 3mins after ya mike ya Kara sa dining ya zauna, Tea ta fara hada masa kana ta dora masa toasted bread biyu da kwai a gefe kana itama ta zauna ta hada nata. Shiru gurin har suka gama ya mike ya fice, tattara kayan tayi ta kai kitchen ta dawo ta kwanta a parlour tana mota ita kadai "kawai ayiwa mutum wani gidan sama tsabar wahala ni gsky bazan iya dinga hawa da saukar nan ba idan na sauko to sai dare ko kuwa wani abu amma kam bazan iya ba wlh mutum yayi ta fama da ciwon kafa da baya tun bai tsufa ba mtsw" haka ta karaci mitar ta har ta gaji tayi shiru, daga nan bacci ya fara fisgarta ganin haka yasa ta mike ta shige nan bedroom din kasa ta kwanta abunta sai bacci.

    Knocking din kofar data ji ne yasa ta mike tana karanto addu'a dakyar ta mike dan baccin bawai ya ishe ta bane toilet ya shiga ta wanko fuskarta kana ta fito, dankwalin ta ta ware tana rufe jikin ta dashi ta karasa ta bude kofar yan gidan su ta gani tsaye da sauri ta basu hanya tana washe baki Waheedah kam sae dariya take, Bayan sun zauna suka shiga gaisawa ta shiga ta dauko masu ruwa da drinks duk da basu da sanyi ta ajiye, nan fa suka baje hajar firar su sai kusan 12:30 suka dora abincin rana, rice and stew sukayi sai salad da suka hada da zubo Bayan sun gama suka zuba suka ci Fuad kuwa aka zuba masa nasa a kula. Part din mommy suka je can suka shiririce har kusan 4:30 basu yi sallah ba ana ta fira.

Fuad kuwa koda ya fito part din siyama ya fara shiga suhail kawai ya samu a parlourn sai takalma da aka shigo dasu da alamu dai baki tayi, da gudu yaron ya karasa gurin sa shi kuma ya duka ya masa peak a kumatu, dariya yaron yayi yace "Daddy Ina kwana" yace "Lpy suhail Ina mommy?"
Cike da yarinta yace "mommy tayi baki kuma tace kar kowa ya shiga shi yasa tace na tsaya a nan" da mamaki yace "Kai kadai?" Yace "Ehh daddy aunty Faty bata nan" mai aikin su.
Shiru yayi baice komai ba ya juya suka fice da suhail, part din mommy suka shiga gaba dayan su suna a parlour sae wasu baki da akayi Bayan sun gaisa suka masa Fatan alkairi da addu'an zaman lpy, kallon mommy yayi yace "daddy fah?"
Tace "yana sama bai fito ba"

𝐇𝐚𝐤𝐚 𝐧𝐚𝐚𝐚 𝐦𝐢𝐣𝐢𝐧 𝐲𝐚𝐤𝐞Where stories live. Discover now