Page 31

96 9 2
                                    

*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_

Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHARJAY* @wattpad

Page 31

Washe gari da misalin 11 Waheedah ta rata saloon tayi gyaran gashi da bakin lalle da aka mata shima bamai yawa ba sai 2 suka koma gida, gaba ɗaya Afeefah jin kanta take cikin wani farin ciki mara misaltawa da dare ma sai da suka raba dare suna fira kafin suka kwanta.
      A ɓangaren Fu'ad da Siyama kuma bayan Fu'ad ya dawo daga kai su mommy gdan biki da dare kafin su kwanta sai data tada fitina wai akan me zai ɗauki Ammi ganin zata saka masa ciwon kai ya saka shi daka mata tsawa "Enough Siyama nike auren ki bake Ke aure na ba and lemme warn you for the last don't you ever shout at me again am not your son nor your Savant get this, maganar ɗaukar Ammi kuma na ɗauka saboda ina son Yara and kin san da haka amma kika hanani ta hanyar family planning Idan kinji haushin ɗaukar ta da nayi to koyi zuciya ki haifi naki mana sai na ɗauka mtsw"
    Ya juya zai fice har ya kai bakin ƙafa gaya idan ma ya barta a haka bai saka mata baccin ran data saka shi ba dan sosae ransa ya sosu juyowa yayi ya watsa mata wani kallo yace "ki daina wahalar da kanku am advising you that ki rage tsanar da kika yima Afeefah ko badan maganar auren ta da zanyi ba she's my blood" tana kai nan ya fice. Baki wangale ta bisa da kallo har sai da ya rufo mata kofar kana ta zauna daɓas kan gado a hankali maganar Fu'ad ta karshe ke dawo mata.
      '''ki daina wahalar da kanku am advising you that ki rage tsanar da kika yima Afeefah ko badan maganar auren ta da zanyi ba she's my blood''''

Da ƙarfi tace "nooooooo Fu'ad wlh baka isa bazaka taɓa auren wannan yarinyar ba na yarda zan haihu amma bazan bari ka auri Afeefah ba" ta ƙara sa tana fashewa da wani irin kuka kamar an min tsine ta zumɓur ta mike ta nufi part din mommy duk da kuka da dare ne dan kusan Karfe goma koda yake har sun rufe kofar su hakan yasa ta hakura ta dawo bedroom ɗin Fu'ad taje sai dai kofa a rufe hakan yasa ta wuce ɗakin Suhail ta kwanta kusa dashi duk da gadon ba wani babba bane dakyar ta samu bacci ya tafi da ita sai kuka take harda kanta ta fara sara mata.

     Washe gari da safe Fu'ad ya fita sae 12 ya dawo dan flight din Afeefah 1:55 ne and ticket ɗin ta na hannun sa,  jin haya niya ya saka shi shiga cikin gida da sauri Muryar Siyama ce a sama tafi ta kowa tashi "wlh shawara nake baki mommy ki saka baki karasa ta aurar min miji idan ba haka ba wlh zatayi dana sani dan bazan barta ba" mommy dai tayi shiru dan har ta gaji da magana sai ƙoƙarin fahimtar da Siyama take amma inaaa idon ta ya rufe, ga Afeefah tsaye kanta a ƙasa tana hawaye ita bata ma san da wannan maganar ba "toh yaushe ma ya Fu'ad ya taba tsayawa ya ƙare min kallo ballantana har yaga abin so a jiki na kodae tsanar da matar nan kemin yasa take wannan ɗaga jijiyoyin wuya dan karna dawo ohh Allah ga baiwar ka".

Shigowar Fu'ad ne ya saka siyama yin shiru tana huci kamar wacce tayi tseren gudun kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai ya ƙara sa gaban mommy yana tambayar lpy? Bata iya ce masa komai ba sai Faruk ne yace "Yah Wai fa akan kace mata zaka auri Adda Afeefah ne yasa take wannan abun Ni ban ma sani ba ko da gaske take dan ba wanda yasan da wannan zancen" harara ya watsa ma Farouk hakan yasa tayi shiru yana hararar siyama ta gefen ido.

     Waheedah ce ta ƙara sa kusa da Afeefah ta saka hannu ta ƙarbi Ammi dake kuka amma bata kula ba kanta na kasa, waheedah na karɓar Ammi Afeefah ta juya da gudu zuwa ɗaki "wannan wace irin tsana ce haka mai nayi ma wannan matar yau ko iyayen ta na kashe baici ramin irin wannan tsanar ba" kayan ta ta shiga haɗawa ta saka a lodge dinta ta ɗauki mahaifinta da handbag ta jawo sai data saka key ta rufe ɗakin kana ta jawo kayanta zuwa cikin parlourn hannu ta saka ta karɓi Ammi ta sakata a jakar goyon ta kana ta matsa gaban mommy murya a raunane tace "mommy zan tafi sai na dawo" charaf Siyama tace "Umma ta gaida Ashsha kamar ki dawo dan baki da gurin zama".

"Siyama" Fu'ad ya kira sunan ta cikin tsawar data zaburar da mutanen parlourn aiko Ammi ta tsoro ta sai kawai ta fashe da sabon kuka Afeefah ta share hawayen ta tana jijjiga Ammi Fu'ad ya karasa ya karɓe ta kana ya dawo gaban siyama murya a kausashe yace"get lost bf I lose my cool" kallon sa tayi tace "bazan fita ba har sai wannan ta tafi dama na gane cewa yanzu baka sona Fu'ad tunda wannan annobar ta shigo gidan nan hankalin ka ya koma kanta" wani lafiyayyen mari ya watsa mata for the first time in his life, tsabar gigita har da wasu stars Siyama Ke gani kuka ne ya kwace mata ta fice da gudu zuwa part dinta.

  Kallon sa mommy tayi da damuwa tace "me yasa ka mareta Fu'ad me yasa ka mari matar ka" baice komai ba yaja hannunta zuwa bedroom ɗinta a bakin gado ta zauna ya jiye Ammi gefen ta kana ya buɗe fridge ya ɗakko ruwa mai sanyi ya bata ba musu ta karɓa tasha ya zauna kusa da ita yana ɗaukar Ammi.

Ajiyar zuciya mommy ta sauke kana tace "Fu'ad bana son matsala ina ga wannan auren kawai  a barshi Allah ya zaɓa ma Afeefah mijin daya fika dama sabo tausayin da take bani sae nake gani kamar ba wanda zai iya rike min ita ko bayan raina kamar ka Fu'ad amma ba komai zan cigaba da mata addu'a matar ka kuma zafin kishi ne dan haka kaje ka bata hakuri"

Numfashi ya sauke yace "a'a mommy maganar fasa aure kam bata taso ba zan san dai yanda zanyi bari na ajiyeta time na tafiya idan na dawo zamuyi magana"

Mommy tace "toh" a tare suka fito parlourn su Faruk Na zaune suna magana ƙasa ƙasa shida waheedah fa Ashraf da alama dai zancen abinda ya faru suke yi Afeefah kuma tana zaune ta kifa kanta a hannun kujera tana share kwalla. Ganin Fu'ad ya saka suka yi shiru mommy ta karasa kusa da Afeefah ta ɗago ta idon ta har yayi jaaa mommy ta girgiza mata kai tana share mata hawayen dake zubowa tace "kiyi hakuri kinji nasan da wannan" murmushi tayi tace "nifa mommy kukan rabuwa dake nake yi" shafa fuskarta mommy tayi tace "toh ai zaki dawo dan ba jimawa zakiyi ba"
A shagwaɓe tace "ehh mommy na duk da haka Ni dai sai nake ji kamar karna tafi".
   Gaba ɗaya dariya suka saka mata banda Fu'ad da tayi mutuwar tsaye yana kallonta wani abu yake ji tun daga kasan kafar sa har cikin kansa cikin ransa yace "dama akwai mata masu shagwaɓa idan suka girma" dan shi dai siyama bata masa shi yasa abun ya bashi mamaki ji yanda take yi kamar wata karamar yarinya sai kawai ya tsinci kansa da smiling.

Har bakin mota suka rakota mommy ta mata addu'a kana ta shiga mota tana sharar kwalla suka wuce cike da kewar juna. Har suka isa airport ba wanda yace ma wani ci kansa sai Ammi dake wasar ta tana dariya, Afeefah kuma gaba ɗaya tunanin abinda ya faru take yi toh wai ma waya gaya ma siyama cewa Fu'ad na sonta" shine mana" wata zuciyar ta bata amsa idan ba haka ai bazata zo tana masifa ba.
  Fu'ad kuma yana tunanin yanda zai ɓullo wa lamarin yake bazai fasa auren Afeefah ba kodan Siyama dole ya koya mata hankali.  Koda suka isa airport ba jimawa aka fara kiran passengers akan labbansa ya furta "safe trip" yana ma Ammi wasa yanda yayi maganar bazaka taɓa tunanin shi yayi ba smiling kawai tayi tace"thanks" kana ta wuce abunta.

Tafiyar 45mins sukayi daga Abuja zuwa Kebbi dama an san da zuwan ta hakan yasa Faruk Gary da Husna suka tafi ɗauko yar gaban gashin aunty. Tun a airport ta San cewa ta dawo gida sai ta nema Abunda ya faru da safe ta manta saboda ganin yan uwanta da tayi wani abun ma sai da suka isa gida kamar zasu cinye ta ɗan murna kowa sai yana girma da wayon Ammi tayi bayan sun huta suka ci abinci aka ɗora daga inda aka tsaya.

.
.
............🦋

"Sulaima ina so dan Allah ka cire wannan abun daga ranka kalli fa yanda duk ka ƙare ka rungumi ƙaddarar ka ka zauna da matar ka Lpy ina so ka kwantar da hankalin ka ka mance maganar Afeefah dan ta maka nisan da bazata taɓa jin kiran ka ba ballantana ta saurayi ka"

Wani gauron numfashi ya sauke yace "mama damuwa ta shine na nemi yafiyar Afeefah ta yafe min mama wlh idan bata yafe min ba bazan taɓa samun kwanciyar hankalin ba a rayuwata"

Cike da damuwa mama tace "toh Allah yasa ta yafe maka Allah kuma ya kyauta tashi kaci abincin ka sannan kuma kaje gidan su Atika ka ɗauki matar ka ku koma gida"

Yace "toh"

Ina baranda addu'ar ku dan Allah exmas gare Ni ku sakani cikin sallolin ku akan Allah ya bani Sa'ad Love You all❤️

#TeamFu'ad
#TeamAfeefah
#TeamSulaiman



*Lioness👑*

𝐇𝐚𝐤𝐚 𝐧𝐚𝐚𝐚 𝐦𝐢𝐣𝐢𝐧 𝐲𝐚𝐤𝐞Where stories live. Discover now