2⃣4⃣wani dadi yaji kuwa, yashiga dakinsa yakwanta can dai yaga kwanciyan bazaiyiba yatashi yarinka tsalle akan gado, esha kuwa gun hajiyan hafeez taje bayan ta rusuna sun gaysa, tace hajiya inada magana ne, tace inajinki baby na, tace cikin sanyin jiki, hajiya inaso ahada auren mu dana meena, hajiya dake bata fahimci maganan ba tace awh manemin meenan yafito ne?, ah bakomi indai iyayenta zadu yadda, tace a a hajiya ina nufin dani da ita da hafeez, mikewa tsaye tayi tare da kallon. Esha dakyau, lalle yar nan, bakya kishinshi ne?; tacee a a hajiya tana goge hawayen daya zubo mata sannan tace shiyakeso ,kuma kinga badadi yana sonta itama, hajiya taja tsaki aikin banza, toh inace abdul dinne yazo ya kitsisina miki magana yace kifada? Don yaganki mai hakuri? Za saba masa fa? Ina yake? Wuce ki kiraminshi, tamike jiki a sanyaye taje fanninsa tabuga kofan yana budewa yaganta, yhto kingaya musu? Ta girgiza masa kai, yafito yabiyota abaya isansu falon suka samu hajiya ta gayyato su alhaji kowa yayi jigim ana jiransu, jikinsa yayi sanyi daga ganin yadda hajiyansa ke jefa masa hararar, anan husuma ta tashi su iyayen esha duk da abun yamusu ciwo anma suna kara wa hafeez din a matsayin dansu suka nuna amincewarsu, yayinda iyayensa suka nuna fir basusan maganan ba, ran kowadai abace itadai esha kanta a kasa, fatanta su amince don batason taga ran hafeez yabaci,anan dai magana ta tsaya akan zaaje asamu iyayen meena ayi maganan aure, akace andaga biki kam, murna agun hafeez ba kanta, harda cewa shikam angama masa komi, esha kuwa da kyar tamike, ranan akan sallaya ta kwana, hakama hajiyarta, sanin datayiwa yarta mai xurfin ciki ce sosai,donhaka tasan komi zai iya faruwa, washegari akadau hanyan abj ta jirgi suka bi, aka nufi gydansu meena dama hafeez yasanar da ita zuwansu, anyi saa mahaifinta yananan, nanma aka fara wani rikicin don ummanta ta wanke ido tsunm tace. Bazaayiba, aiwannan cin amana ne, anma inbanda rashin hankali anraba meena da yaron nan taki ko?. Anandai mahaifi kam ya yarda dakomi. Aka bada sadaki, akace rana daya zaayi biki Washegari suka dawo kaduna, anan fa esha take bawa sakeena lbr, sakeena lawan,batace komi ba anma ita tasan meta kudurta aranta, dama zataje abj a satin aikuwa tana zuwa takira meena, anan suka hadu, meena tace inajinki anan sakeena tafara bayani, zan gayamiki tarihin aisha umar dakuma abdulhafeez ahmed ko Allah zaisa kiji tausayinsu kifita rayuwansu,itadai meena tazuba kunne tana sauraro sakeena tafara kaman haka hafeez tun kafin yashiga atbu inda kika tsinceshi tare da esha suka tashi, zuwa makaranta cin abinci, hafeez shine yayan esha,babanta,mamanta akoina don yahutace iyayenta akan komi
YOU ARE READING
ABDULHAFEEZ (2014)
Short Storya hausa novel, so emotional,tragedy,love sacrifice, and patience