Charpter 9

12 4 1
                                    

*OUM MUMTAZ...📝*

*RAYUWAR DARAKHSHAAN*
      
  _chapter 9_

Waya ce samfarin spark 3 Anty Batool ta aiko mata,wanda hakan yasa ta cika da farin ciki,dikda wayar bata kai waccan wayar tata ba,amma dai falillahi hamdu.

Ranar kam Anty Batool tasha godiya cikin buhu buhu,wanda oum data ga wayar ne ma tasan ashe shaan din ta kira batool,wanda hakan yasa ta k'ira ta,had'i da yi mata godiya.

Sai da tayi ma wayar tata full charji,kamin ta saka sim card's nata akai,inda ta sauke dik wasu app masu amfani a daren wannan daranar ta kuma yi settling nasu kamin ta kwanta baccin ta,wanda washe garin ranar kuwa aka ci sa'a saiga kiran ahsan ya shigo mata waya bacin ta farka a bacci,sun gaisa normally kamar ko wasu masoya,wanda kuma dama shi ahsan din sai jujin sa ya hau kansa ne ma yake neman ta.
Inda yake tambayar ta lafiya kwana biyu ya daina ganin ta online...? Sannan kuma wayar ta bata shiga? Bayani ta masa ta yadda ta fada ma su oum kamin suka sha hirar su,wanda hakan yayi mata dad'i ba kad'an ba.

saida ta kammala dik ayyukan ta kamar ko yaushe bacin oum ta fita zuwa gidan su mmn Anty batool sbd yau basu da office,kwanciyar ta tayi kan katifar ta,inda ta kunna datar ta,ta hau status nata ta rubuta "Alhmdlh"

nan da nan kuma wayan da sukayi viewing na status din da suke mutunci suka fara mata welcome,inda itama dik tabi tayi reply na sakonnin mutane,wanda nasu yazo mata a waiting kuwa tsallake su take,bama ta budewa.

Inda daga cikin sakonnin da suka bude mata har da na dina,wanda hakan ke nuna ma can cewa tana online kenan.

Ba tayi k'asa a gwiwa ba kuwa ta bude,inda ta tarda sakon ta tana tambayar ta "bamuyi kyau bane baki ce komai ba...?"

wani siririn tsaki taja cike da takaicin dina d'in,kamin ta mata reply da fad'in "ashe baki da wayo ban sani ba dina?"

inda dinner ta aiko mata da fad'in "ban gane bani da wayo ba,wani abu ya faru ne??"

"wato ma baki san abinda kikayi ba kike tambaya ta wani abu ne ya faru? A gaskiya kin matikar bani kunya! ban taba tunanin haka din daga gare ki ba!"

"Ha'aa! malama dilla ni ki fito ki fda man abinda ya faru bawai kina man magana kina rufa rufa kamar wata karamar yarinya ba!"

cije baki shaan tayi cike da takaici inda ta mayar mata ansa da fadin "dan Allah mai kika aikata ke da wannan saurayin naki?? yanxu fisabilillahi ace kina diyar musulmai wacce keda hankali da sanin ya kamata tare da ilmin islama gwargwadon iko amma kike tsayawa ki tafka wannan shirmen da d'a namiji!? D'a namiji din ma da bashi da tabbas ki tsaya kina wannan shiriritar dashi! wanda nake da tabbacin idan ke kin tura man wannan vedio din ni kad'ai,shi kuma baki san iya adadin mutanen da zai tura ma ba,tin da su maza wani zubin ba hankali gare su ba?? ko baki san cewa yanxu idan aka bibiya ma shi bawai don soyayya kawai ya tsaya kukayi wannan short vedio din ba,sai don sbd wata manufar sa kamar yadda dab'i ar dik samarin zamani yake??! to wlhi tin wuri kima kanki fada kisan inda ke maki ciwo a matsayinki na diya mace kamin abu yazo ya kwbe maki kiyi dana sani daga baya!! nidai shawarar da zan iya baki kenan a matsayi nah na diya mace kuma matsayin k'awar ki!"

Shaan ta k'arashe typing din,sbd tunano sanadiyyar haka din itama mutuncin ta yaso ya zube a idanun duniya Allah ya taimake ta.

daga ta can bangaren kuwa jikin Dina ne yayi sanyi,a lokacin data gama karanta sak'on Shaan,harma ta rasa mai zata fara ce mata wanda zaisa ta kare kanta,sbd matsananciyar kunyar data rufeta lokaci guda!wanda bata taba expiriencing akoi sa a duniya ba! inda da kyar ta samu damar yi mata karamin typing da fadin "na d'auki shawarar ki k'awar arxiki! kuma insha Allah na daina wannan mummunar dabi'ar,wanda ni kaina nasan ba dai dai nake aikata wa ba! amma kuma sbd rashin mafadi da zai zaunar dani ya sake nutsar dani akan hakan,sai nake ganin kamar ba wani babban aibu bace"

RAYUWAR DARAKHSHAANWhere stories live. Discover now