Charpter 6

11 4 0
                                    

*OUM MUMTAZ...📝*

*R . D*
      
  _chapter 6_

A gefen sa ta zauna inda su triples keta faman buga game da wayar ta.  "ina wuni baba" shaan ta fada ma kamilallen dattijon da a kalla zai kai irin shekaru 70 dinnan,  "lafiya qlaou mamana! kina lafiya...?" ya fada yana mai dan shafa mata kanta fuskarsa da murmushi.

sunkuyar da kanta shaan tayi cikin murmushi mai kyau tace "lafiya qlaou baba! ya kafar taka...?"    "da sauki mamana kafa kam gata nan ne sai godiyar Allah."

"Allah ya kara maka lafiya tare da  tsawon rai mai amfani baban mu." shaan ta fada fuskarta da wadataccen murmushi sosai sbd yadda take matikar sakewa dashi bata tabayi da wayanda suka kawo ta duniya,badon komai ba sai don sbd yadda ya tsaya tsayin daka akanta shekaru uku zuwa hudu da suka gabata ya karba mata yancinta a hannun mutumin da abaya take ganin bazata taba iya rayuwa batare dashi ba.

wanda ta tabbata badon shi ba da a halin yanxu wannan karatun da takeyi ma sam bazatayi shi ba zai zaman jiran gawar shanu.

cike da jin dadi baban ya ansa mata da "ameeen ameeen mamana ta kaina! Allah yayi ma rayuwar ku albarka tare da yan uwan naki baki daya"

"ameen ameen,baba zan wuce gidan su daniyah ne ma kamin ma wuce gida kar dare tayi man" ta fada a lokacin da take mikewa tsaye.

miko mata kudi kimanin dubu takwas baba yayi tace "toh sai kin zagayo ki gaida man iyayen naki,kuma kice ma _Abul hassan_ ina naiman sa idan yazo gidan"

"insha Allah baba" ta fada a lokacin da take gyara zaman mayafinta dake silale mata bayan ta anshi kudin da dik bayan kwana uku sai ya bata sbd shan mai ma motar ta da shine ya saya mata.

saida ta koma wurin ummy wato matar baba tare dasu Aadila tayi mata sallama inda itama ta bata kyautar dubu biyu tare da wata riga doguwa ta ready mate sannan ta wuce zuwa inda tayi parking na motar bayan ta anshi wayar ta inda ta fice daga gidan zuciyarta wasai su Aadil na daga mata hannu alamun bye bye.

batayi tafiya mai tsawo ba ta iso kofar gidan su daniyah,inda ta fito daga motar ta fada gidan nasu da sallama a bakinta ta shiga inda ta tarda mahaifiyar daniyah da suke kira da anty tare da daniyah sai kuma wata kanwarta a kofar kitchen alamun girki sukeyi.

da fara'a kuwa sosai anty da malika (kanwar daniyah) suka karbe ta idan ka dauke daniyah dake ta faman daddauke kai irin har yanxu fushi nake dake dinnan.

"ina wuni anty na same ku lafiya...?"   "lafiya qlaou yar nan! ina maman naki da kuma wurin  su _Aadab_ da sauran yan gidan naku...?"

"dik lafiyan su qlaou wlhi! Aadab kam na kwan biyu ban leka gidan nata bama"

"ai kuwa dai ya kamata kina ziyartar yar uwar taki akai akai kinji ko...?"   "insha Allah!"

sosai ta sake da anty din suka sha hirar su kamar wasa sa'anni inda daga karshe ma daniyah ta bar kumbure kumburen da takeyi suka sha hirar su kamar babu gobe!

sai da suka kammala abincin su inda anty ta diba mata a kula kamin sukayi sallama ta komo gida fuskarta da wadataccen farin ciki ba kamar yadda ta fita cikin kunci ba. a bude ta tarda gidan wanda hakan ya shaida mata da cewa babanta ya dawo gida.

saida ta shigar da motar ta kamin ta dakko laidar da rigarta ke ciki inda tayi sallama a mashigar parlon,badon an koya mata a gidan su ba,saidan fa'idar yin sallamar da ta jiyo a bakin anty(mmn daniyah).

dattijo ne sosai da a kalla zai kai irin 60yrs dinnan fuskarsa dik farin gashi ya kewaye,idanunsa sanye suke cikin glass na medicated sbd matsalar idanu da yake dashi,inda kuma gabansa kan wani table na roba cike yake da takardu na student da yake making.

"ina wuni abi" shaan ta fada a lokacin da take idasa zama daga ta bakin kofar da zai sadata da cikin gidan. abi dake binta da kallo tin dazu ya dan sake fuska kadan yace "lafiya qlaou,daga ina kike...?"

"naje gidan baba ne" shaan ta basa ansa a takaice!  jinjina kai abi yayi alamun gamsuwa,kamin shaan ta daura da fadin "ina su Aalee da sauran mutanen gida...?"

"dik lafiyar su qlaou" abi ya bata ansa a lokacin da yake gyara gilashin idanunsa bayan ya maida hankalin sa akan abinda yake yi.

wanda hakan yasa shaan mikewa daga zaunen da take ta idasa shigewa cikin gidan tana jin takaici da abi bai tambaye ta lafiyarta ba da tayi kwana biyu bata sanya shi a ido ba sbd yana gidan dayar matar tasa da suke kira da ummu.

a gurguje ta fada kitchen sbd jin an fara kiraye kirayen sallar magiriba ta daura masu jolouf na shinkafa. sannan taje ta gabatar da sallah,wanda zuwa lokacin abi ma ya tafi masallaci. oum ce ta dawo gidan a lokacin kamar koda yaushe.

itam ma sallah ta gabatar kamin ta bukacin shaan data kawo mata abinci batare da ta tambaya shin "abin naku ya iso? ya kika wuni...?" ko kuma wani abu makamancin haka ba daya dace ace uwa tayi a dik lokacin data dawo daga wani wuri,wala Allah unguwa taje ko kuma tafiya tayi.

saida ta kammala abincin kamin ta zubo ma oum a plate,bayan ta zubama baba a flast sannan ta daura masa akan karamin plate da kuma cokali a gefe.

saida ta ci nata a daki bayan tayi sallar isha'i kamin ta fito bayan ta sakala chajar wayarta zuwa parlo da zuwa lokacin abi ma ya dawo daga masallaci harma yana cin abincin,oum kuma na gefen sa itama kamar koda yaishe wayar ta ce a hannun ta tana ta faman dannawa.

tin kamin ta zauna oum tace "jeki dakko man plate da wuka,sannan kuma ki bude fridge zaki ga kankana da ayaba kizo sa su"

bata ce komai ba kuwa ta fice zuwa kitchen inda ta kawo mata! oum da kanta ta yanka kankanar data kasance rabin kwallo ce. sai kuma ayaba din data miko ma shaan guda daya tare da yankar kankana guda daya,sai kuma ta ajiye na cikin plate din tsakaninta da abi.

shaan kuwa Allah yayo ta ne mai masifaffen son ayaba kamar me...? yau koda ace bakunta taje gidan mutane akayi mata tayin ayaba bata taba iya tsallakewa sbd yadda yake mata dadi. dan hakane ma yanxu data cinye na hannunta tace "oum ki karamin dan Allah"

harara kuwa oum ta watsa mata kamin tace "wato ke kwata kwata a rayuwarki baki da godiyar Allah ko...? ina nan nan da nace ki dakko plate din tsabagen ki nuna ma duniya kin raina ni baki kulani ba sbd gani kike kamar kinyi ci baya ne idan har kika ansa man toh...?"

har shaan zatayi mgn abi ya daga mata hannu alamun tayi shiru,sannan ya miko mata ayaba guda daya amma fir shaan taki karba wanda karshe ma bar masu parlon tayi tana mai sakin wani marayan kuka cikin zuciyarta.

wanda daga karshe ma bacci ne yayi gaba da ita batare da ta sake biyewa ta kan wayar tata ba datake da burin ci gaba da rubuta labarin rayuwarta wato "diary"

_zan ajiye post na littafin nan idan banga chanji ba yau_

*vote*
*comment*
*share*

RAYUWAR DARAKHSHAANWhere stories live. Discover now