charpter 4

10 3 0
                                    

*OUM MUMTAZ...📝*

*R . D*
      
  _chapter 4_

Washe gari da safe shaan ta farka daga baccinta wajen 6:00am,wanda sai a lokacin tayo sallar asuba dinta,tana idarwa ta sake komawa baccinta,wararen 7:30 tajiyo mahaifiyarta na kwalo mata kira,wanda hakan ya sata mikewa fuskarta cinkushe babu alamun fara'a sbd yadda baccin nata ya farayi mata dadi gashi kuma an katse mata shi.

dakin mahaifiyar tata ta wuce daga bakin kofa ta tsaya bayan ta daga labulen tace "gani"

"ki hura wuta,kiyi mana dan wake,kuma kiyi sauri sbd ina son fita da wuri yau" oum ta fada idanunta rufe alamun baccin nata nayi mata dadi!

bata ce kala ba ta fito daga dakin xuwa kitchen din nasu,inda ta hura wuta akan makubar ta sannan ta daura ruwan zafi cikin tukunya lamba biyu.

daga nan kuma ta tankado flower a wata roba daidai bayan ta jika kanta ta tankade kuka dai dai da yadda zai isa na yin dan waken,bulugari ta dakko inda cikin kankanin lokaci ta kammala kwaba garin dan waken,wanda dik wannan abubuwan da takeyi fuskarta sam babu fara'a,wanda haka nan yau ta tashi tana jin tsananin bacin rai da bata san mai ya jawo mata ba.

ta na zaune a wurin ra jefa dan waken,tana kuka dashi,saida ta gama shi tsaf kamin ta daura ruwan zafi wanda zasuyi wanka dashi! bata tashi oum ba saida ta tabbatar da cewa tayi sharan gidan nasu tsaf,ta kuma kai masu abincin parlo bayan ta zuba dik wasu abubuwan daya kamata taje dakin mahaifiyar tata tace "na kawo abincin"

daga haka ta fito daga dakin ta dakko wayarta da tun jiya rabon ta dashi ta tarda missed call na daniyah,bata bata lokaci ba wajen bin bayan kiran inda kuwa ta dauka!

"shaan baki hau online bane yau...?" ta juyo muryar daniyah ya doki dodon kunnenta!   "babu sallama babu ina kwana sai tambayar ban hau online ba lafiya...?" shaan ta fada a lokacin datake zama inda abincin nasu yake kuma a daidai lokacin oum ma ta shigo cikin parlon sanye da sleeping dress!

"ki ajiye batun wasa a gefe in gaya maki! dazu da sassafe sir Aasim yace mu fito karfe tara akoi lectures  da zai mana na tsawon awa hudu! kuma yace dik wanda baiyi attending na wannan class din ba tabbas sai ya kayar dashi domin kuwa yace maki sha biyar biyar zai bada kyauta!"

jin wannan batu da daniyah ke mata me ya sata mikewa hadi da katse wayar tata batare datace ma oum da harta fara cin abincin komai ba zuwa dakinta,a gaggauce ta tube kayan jikinta hadi da daura zaninta na atamfa dake matsayin na wankan ta ta wuce zuwa banda ki!

da ruwan sanyi tayo wanka ta fito a gaggauce sbd a lokacin ma takwas da rabi tayi,kuma gashi zuwa makaranta zai dauke ta kimanin mintuna ashirin kamin ta isa!

mai na vaseline ta murza ma fatarta da bata samun wani wadataccen kulawa ta zura wata doguwar rigarta ta material da bata nauyi ta saka hula akanta sannan ta saka wani hijabinta daya kai mata har kasa ta tattaro su laptop nata da dik wasu abubuwan daya kamata ta jefa su cikin babbar jikarta irin wanda akafi sanin yan sec school na anfani dasu ta fito hannunta rike da key da motar ta!

oum da har ta kammala cin abincin nata ne ta kalli shaan dake tsaye ta wajen kanta kan zata wuce makaranta sbd kiransu da akayi na gaggawa...!

"kin gama ayyukan ki ne da kike ta faman rawar jiki dinnan...?" oum ta tambaya tana mai kafe yar tata da ido fuskarta babu walwala! marairaice fuska shaan tayi tace "dan oum ki barni ta nafi idan na dawo zanyi wanke wanken da banyi ba sbd na riga da nayi shara tin dazu!"

harara ta maka mata cikin daure fuska tace "wallahi idan baki je kinyi wanke wanken nan ba yau a gidannan idan ranki yayi million sai ya baci!! in banda shegen son yawo irin naku ma na yaran yanxu zaku wani ce wai an nemo ku a makaranta salon ku tafi makarantar kawai ku zauna hira tsakaninku kunayi ma malamku karya wai sun naime ku ko...?"

RAYUWAR DARAKHSHAANWhere stories live. Discover now