Charpter 8

16 6 0
                                    

*OUM MUMTAZ...📝*

*RAYUWAR DARAKHSHAAN*
      
  _chapter 8_

Tin daga wannan ranar sai ya zamana shaan kan kira dina jefi jefi idan ta samu lokaci,wanda daga baya ne ma take jin ashe cewa ita din bama yar garin su bace,amaryar yar uwar su ce,shine suka zo biki tare da yayarta dake aure a abuja.
kuma tin daga wannan lokaci da kadan kadan wani irin shakuwa na ban mamaki ya shiga tsakanin shaan da dina,dikda kuwa sau daya suka taba haduwa a rayuwar su face to face,saidai a pics da suke exchanging a wasu lokutan,chart kam ma ba'a magana,sbd kullum sai sunyi chart nasu cike da tsananin shakuwa,wanda abin yayi tsamari har su daniyah da kuma danish suka san da zaman dina a rayuwar shaan.

sosai aminci ya kullu tsakanin su na ban mamaki,wanda kuma dik wannan abotar da su dina kanyi kwata kwata oum bata labari a matsayinta na mahaifiya da a koda yaushe ake son uwa tana bibiyar rayuwar yayanta akan kari,more especially kuma yaya mata.

kusan koda yaushe kuwa suna online abin su,suna chart nasu,harma da guzurin adding na dina a group din su da suka bude su uku da farko suka zamto aminai guda hudu.

kuma takan zuwa gidan baba akai akai tana gaida sa,wanda kuma kusan dik ranar da taje yakanyi mata kyautar kudi,matar sa kuma harda kayan sawa sabbi take bata,ga kuma shakuwar dake tsakaninta da yaran yayan baban nata da suka kasance yan uku.

bangaren anty batool dikda basa gari daya da shaan,amma kuma basu tabayin lafiyayyen kwanaki uku zuwa hudu basuyi waya ba,kodon sbd *mysha* data kasance diya a wurin shaan.

bangaren zamantakewarta da iyayen ta kam zuwa yanxu zamu iya cewa da sauki,dikda ba wani har can ba,domin ko wani zubin oum idan ta dawo daga wurin aiki da yamma bata sake fita ko ina sai kuma washe gari ba kamar a baya ba,da kullum saita fita da dare ma zuwa gidan kawayen ta,sannan kuma fita zuwa gidan biki ko suna da takeyi a weekend ma dai yanxu dik ta rage su,wanda kuma shaan bata san dalilin hakan ba.

yau ta kama ranar alhamis!

shaan ce zaune a fili na gaban gate nasu akan tabarma,ko kaya ma babu a jikinta,illa wani mini towel da tayi daurin kirji dashi,hannunta rike da wayarta fuskar kuma shimfide da wani irin lallausan murmushi sbd maganar da taga ahsan yau yayi mata ta whatsapp bayan tsawon lokaci da suka kwashe batare da sunyi waya ba.

wanda ba komai ne ya shi yi mata magana ba,sai don wani pic din wata kawarta data daura a status yace "nice pic" amma ita kam shaan da shike bata da bin kwakkwafin irin wannnan maganganun sam bata san inda zancen nasa ya dosa ba,illa ma zallaf farin cikin daya cika mata zuciya.

taga sama wayar tata taga sakon dina ya shigo mata waya,wanda hakan yasata shiga domin ganin abinda ta turo mata,wani short vedio ne da kwata kwatan sa bazai wuce 8 sec ba,wanda ganin wannan vedio din da tayi sosai ya daga mata hankali,dina ce tare da wani saurayinta da a kusan ko yaushe idan suna chart takan bata labarin irin yadda yake son ta,kuma ita din ma tana son shi ba kadan ba,sannan kuma kulawar da take samu daga gare shi,amma kuma koda wasa dai dai da sec daya bata taba sanin har yanxu akoi mata irin haka ba,da kan sakewa da saurayi ya taba mata dik wani sashi na jikinta da sunan photo,domin kuwa illar abin yafi birgewar sa yawa kwarai da gaske.

dina ce tare da saurayin ta zaune kan wani kujera,wanda daga gani nan din cikin parlo ne,suna rungume da junan su,inda bakin saurayin ke kan kuncinta,hannunta na hagu na kan kirjinta,inda dayan hannun kuma ya sakalo sa ta bayan kugunta kamar zasu shige cikin junan su,suna ma junan su wani irin kallo wayar na hannun dina da itace keyi masu vedio din dikda ba kallon camera sukeyi ba!

wani irin tashin hankali ne ya ziyar kwakwawar shaan,harma batasan sanda tayo wurgi da wayar tata ba,jikinta na daurar tsananin rawa sbd ganin wannan abu ba karamin tada mata hankali yayi ba!

haka nan Allah ya daura mata soyayyar dina har can karkashin zuciyarta,amma kuma dikda hakan,har yanxu daya daga cikin su bai taba bama dan uwansa cikakken tarihin rayuwar sa ba! bazata taba so taga rayuwar dina ya lalace ya tafi a haka ba,kamar yadda tata rayuwar taso ta gurbace a yan wasu shekaru da suka gabata.

lalumo wayar tata tayi,da niyyar danna ma dina kira,amma kuma me...? saita tarda wayar tata tayi kwatsa kwatsa,sam babu kyan gani,sbd yadda taci screen gaba daya,gashi kuma ita sakama waya su wani guard ko corver sam baya birgeta,wanda yau kam taji haushi matuka da fashewar wayar tata dikda cikin tsananin damuwar da take ciki nason tayi magana cikin gaggawa da dina akan wannan abinda ta gani.

haka nan har oum ta shigo gidan shan bata motsa daga inda take ba,sannu da zuwa tayi ma oum din fuskarta cike da damuwa bayan sun shiga parlo tace "oum dai am wayata ta fashe gaba daya!" ta kare maganar kamar zata fashe da kuka sbd sanin irin mahimmiyar rawa da waya ke takawa cikin rayuwarta,data barma kanta sani,wanda kuma hakan sirrinta ne,bata bukaci a bayyana ma duniya ba.

"garin yaya akayi hakan ta faru...?" oum ta tambaya da yar guntuwar kulawa akan fuskarta,  "yanzu ne kawai naje mikewa ya fadi akan birji din da akayi cuko dashi" shaan tayi karya da hakan sbd bata so oum tasan asalin dalilin fashewar wayan.

"kema ai baki abu a hankali shirya" oum ta fada a lokacin da take makala babbar android nata a jikin charji.  "oum dan Allah ki bani karamar wayar ki na saka simcard nawa a ciki...?"

shaan tayi maganar cike da marairaicewa,wani irin matsiyacin kallo oum ta jefa mata tace "ai bani nace ki fasa wayar taki ba,tinda ke dama sam bakya abu a hankali" tana gama fadar hakan tayi shigewarta,tabar shaan zaune dake jin haushin kanta da har taje ta fasa wayar tata.

"ke kam ba maa ta hana ki zama babu dankwali bane? da wannan dan iskan towel din...?"  oum ce ke wannan maganar a lokacin da take fitowa bayan ta yi wanka.

batare da shaan tayi magana ba ta wuce dakinta,hannunta rike da wayar tata,inda ta jefa sa cikin wata jikarta,sannan tayi kwanciyarta akan katifarta,tana jinta wata iri kama mara lafiya! inda tunanin ya hade mata goma da ashirin,gana dina,ga ahsan da yayi mata magana yau,ga babu wayan da zata shaidama su danish batta da waya,gashi kuma babu wayar dake debe mata kewa a dik lokacin data kasance ita kadai a gidan batare data bukaci zuwa yawo ba,kamar yadda wasun keyi idan zaman kadaici yayo masu yawa.

tin daga wannan ranar sai kadaicin ya taru yayi ma shaan yawa,tama rasa ta inda zata fara bulloma al'amuranta cikin gaggawa,gashi babi yadda batayi da oum ta bata karamin waya ba,amma oum takiya! inda wani zubin takance mata "ina shi wanda zaki aura din da bazakice ya say maki waya ba...?"

wanda in shaan taji hakan,har cikin zuciyarta take cewa "Allah ya tsare ni da sake karban abin hannun wani da namijin da sunan roko."

ta fada ma abi ma bata da waya yace karta damu zai saya mata zuwa karshen wata,amma shuru har watar ta shide bai saya mata ba,ita kuma yanxu dai tasan da kunya ace taje wajen baba da sunan a saya mata waya,bacin kuma na hannunta dinma data fashe shine ya saya mata ba kowa ba.

ranar data fita zuwa gidan wata kawarta ne ta ari wayar kawar,tare dasa sim nata,first wanda ta fara kira anty batool ce,bacin sun gaisa ne anty batool ke tambayarta shin lafiya kwana biyu wayarta bata shiga?

anan ne ta shaida mata dsame bayani da tayi ma oum,wanda basu rabu a wayar ba,saida anty batool tayi mata alkawalin waya cikin satinnan.

kawayenta na online datake mutunci dasu dik ta kira su,tare da aminanta,wanda dina ce kawai bata kira ba,ta bari akan sai ta sami waya abin nasu zaifi sirri.

bayan sati daya.

*inga chanji kuga chanji,idan kuma kukace ba haka na,saikun ganni bayan wata biyu😉😉😉*

*vote*
*comment*
*share*

RAYUWAR DARAKHSHAANWhere stories live. Discover now