21_25

23 4 0
                                    

*OUM MUMTAZ...✍🏽✍🏽*

*RAYUWAR DARAKHSHAAN*
      
  _chapter 21-25_

"Umma ina kwana ...?" na fada cike da dauki,maimakon ta ansa man cikin fari ciki a dik lokacin da muka soma waya sai akasin hakan ya biyo baya,domin kuwa rufe ni tayi da fada sosai kamar zata fito ta cikin wayar ta jibge ni kan wai ita batasan sanda na koyi rashin kunya ba dai har zan ma wacce ke mat'sayin mahaifiya a waje na ba!

Da shike a lokacin nima da wayo na sai banyi shiru ba tiryan tiryan na kora mata jawabin abinda ya faru,wanda a yanayin yadda naji muryarta na tabbatar data gamsu da bayanai na,amma hakan bai sata kyale ni ba sosai ta nuna man illar rashin kunyar da nake kokarin daura ma kaina kamin muka shiga hirar mu kamar babu gobe...!

Yaran kakata su su hudu ne,akoi namiji guda daya daya kasance shine babba yana da yara a kalla kusan guda goma tare da matan sa guda uku! Sai kuma HALIMATU wacce muke kira da Umma,ita kuma yaran ta guda uku ne,akoi namiji babba,sai maibi masa mace ce wato ANTY BATOOL,sai kuma k'aramin su da shima ya kasance namiji (wanda nace maku ya bata 1k tasa kati lokacin daya kawo Oun gida...).

Sai kuma Oum da ke da yara guda Uku,YUSIF,Aadab da kuma ni shaan...! Sai kuma Mmn Musa da ke da yara wajen guda biyar,musa ne babba sai kuma sauran kannen sa da dikkan su mata ne...!

Muna gama hirar tamu kuwa mukayi sallama inda na fad'a harkoki na gadan gadan,bamu jima da zama a wajen ba saiga kiran Oum ya shigo,wanda Kaka ce ta d'auka sannan ta mik'o man bayan sun gaisa "zanci kutumar b...'ubanki fa shaan,wato kinga na tura ki can din shine kika samu lasisin yin iya shege son ranki ko? Hmm to wallahi tallahi ki had'a kayanki gobe da sassafe akoi Idriss zai zo damaturu nasa yaje ya dauko ki,idan kuma kinki zuwa zaki sha mamaki nah...!"

Ai kuwa a daren na hada kayana dikda ban so ba,sannan kuma muka hadu da Qaseem a gidan wata yar uwar su aka barmu a parlo,a lokacin ne kuma shima ya fito man tasa zalamar a fili sai na gagara hana shi,a lokacin na riga dana gama sanin mai ake kira da shawa tinda tin ina kankanuwa ta na rayu ne akan turbar hakan...! Sai ma hadin kai din danake bashi a wannan lokacin,munyi iya shege kam iya shege amma bamu ketare zuwa asalin wajen ba,inda ya dauki kyauta dubu biyu ya bani da tinda nake a rayuwa babu wanda ya taba bani a hannu na halak malak...!

Sosai na nuna masa jin dadina kuwa,da shike banda waya sai ya rubuta man number nasa akan wata papper ya bani muka rabu cike da kewar juna...!

Washe gari kuwa da sassafe saiga Idriss din yazo muka kama hanyar garin mu cike da kewar Kakata...! Ai kuwa da shike ranar sunday ne a gida muka sami Oum,daga shiga na ko zama ban samu zarafin yi ba ta kamani da zagi ta uwa ta uba kan dalilin da yasa nayima kanwarta rashin kunya! Wanda hakan yasa raina yayi masifaffen b'aci,haka taci gaba da zagi na da wasun ma ban taba sanin akoi su ba!

"to kina ta zagin uwata kuma dai gashi naga kece uwar tawa yaya mat'sayin zagin da kike man kenan...?" ta kat'se mata zagin da take zuba man a fusace,da ya sata fashewa da kuka wai yar data tsuguna ta haifa yau gashi Allah ya kawo randa ta zage ta...! wanda ta fara auna man maganganu cikin muryar kuka "insha Allahu yadda kika sani zubar da hawaye a rayuwa kema sai kin samu wanda zasu saka ki zubar da hawaye koman daren dadewa!😭😭 idan kuma anyi duniya don manzon Allah sai kin gani a kwaryar cin tuwon ki wallahi😭😭😭" daga nan ta barni a wajen nima na fashe da kuka daga baya kuma naji zuciyata na bushewa,a raina na raya koma mai zata man tayi indai akace nasan banyi laifi ba aka dage nayi to koman girman mutum saina karyata shi...!

Daga wannan lokacin sai ya zamana idan dai Oum ta fita,nima ficewa nake inje gidan kawaye na dake da waya insha wayata da saurayina Qaseem...! A tsakankanin wannan lokutan nayi samarika da dama da babu abinda ke rudar su sai surar jiki na ni kuma in barsu suyi ta luguda man jiki na idan sun gama su bani kudi,wanda dashi nake kashe wasu bukatu na,na yau da gobe tinda ko nace a gida bani ba bani din ake ba!

Ana cikin haka Abi da Oum suka sama man makaranta inda a lokacin nake SS1! Inda acan makarantar ma sosai nake da samari kamar me...? Wanda a wannan lokacin sosai idanuna suka sake budewa da sanin dik wani lungu da sako dake jikin da namiji! Amma kuma abinda na gagara yi shine na basu kaina,wanda na riga da kudirta a raina koman rintsi wannan din mallaki Qaseeem ne,domin kuwa soyayyar da nake masa a lokacin ta zarce misali akan sa ina jin da kowa ma zan iya batawa!

A haka rayuwata ta ci gaba da gangarawa cikin rashin sanin darajar kaina da kuma mai daura ni akan ga abinda ya dace nayi ga kuma wanda bai dace ba,soyayyar uwa da uba kam dama ban taso a cikin ta ba,ballantana na yan uwana! kuma dik wannan budirin da ake dangin abin mu na sane amma babu wanda yayi yunkurin daura shi akan yadda yakama shima ya zama jajirtacce!

I was 16yrs na kammala secondary school nawa a watan june july...! Wanda kuma zuwa wannan lokacin Qaseem da babu kalar iya shegen da bamuyi dashi ba ya gama hure man kunne a gidan mu na tada borin ni aure nake so ! Haka kuwa akayi lokaci guda na tada masu borin ni aure nake so bazan ci gaba da makarantar ba! Ai kuwa babu wanda ya hanani,ABI yace ince ma Qaseem din ya turo magabatansa! Inda cikin kankanin lokaci akayi komai aka kammala aka saka aure watanni hudu masu zuwa!

A yadda na sani dai muddin aka sama yarinya ranar aure abinda uwa ke farayi shine naima a yarda maganin sanyi follow by irin gyaran da ake ma dik wata amarya amma banda ni! Domin kuwa babu abinda aka man da sunan gyaran jiki ballantana akaiga koyar dani yan wasu dabarun daya kamata ayima ko wacce yarinya ballantana ni yar kimanin shekaru 16 da iyakaci na sec sch...!

Inda Abi dai ya kokarta ya man set amma ba kamar yadda yayi ma Aadab da yarshi dayar ba sbd already a lokacin an riga da anyi auren su...!

Nidai gani nan ne kawai dik abinda aka man saidai ince nagode,wanda kuma a lokacin sosai nayi laushi,a raina ina raya cewa anya kuwa abi da oum sune suka haife ni? idan ma sune suka haife ni mai nayi masu har haka da zafi da basu nuna man kauna kamar yadda  suke nuna ma sauran yan uwana? idan ban manta ba lokacin da za'ayi auren su Aadab har gida aka kawo ma Oum ita gyara ciki da waje tasha su tare da dinkuna na alfarma!

Lokacin da auren yazo nayi sa ne cikin tsananin kunci fiye kima! babu wani program da akayi,gashi ni bansan ana wani karbar kudi a hannun miji ba irin nasu turaren wuta da dai sauran su!

Hmm wani tashin hankalin daya man karar t'saye ya kuma kusan zautar dani shine labarin ashe wai bani kadai bace aka daura ma aure tare da Qaseem ba a wannan ranar!😭😭😭😭


*Ku nuna man k'auna ta hanyar sayan littafina na 💖MOMTAZ💖,alan kud'i k'alilan naira d'ari biyu 200 ta wannan asusun bankin 0562758097 fatima adamu fate GT bank,tare da shaidar biya ta wannan number 09076427357,ga way'anda basu da account number kuma sai ku d'auki hoton kati MTN ko AIRTEL naira d'ari biyu 200 ku turo man ta number na dake sama💖💖💖daga nan ni kuma sai na sank'ama ku cikin paid group😍😍😍😍*

*vote*
*comment*
*share*

RAYUWAR DARAKHSHAANWhere stories live. Discover now