*OUM MUMTAZ...📝*
*R . D*
_chapter 7_Washe gari kuwa tin wajen 6:30am oum ta tashi shaan kan ta daura abinci da wuri sbd abi zai tafi makaranta yana da lecture by 8:00 o'clock am.
wanda hakan yasa sai ture turen baki takeyi na katse mata baccinta da akayi dikda dama kusan koda wani lokaci muddin abi na nan toh kuwa tabbas tashin wurwuri takeyi domin shirya masa abinda zai karya dashi kamin ya wuce wurin aiki. wanda kuma ita a nata tunanin gani take kamar ai ba ita bace ya cancanci ace ke ma abi girki a dik lokacin da yake nan domin kuwa akoi wata kawarta dake layin su itama babanta mata biyu ke gare sa,sannan kuma suma ba gida daya ya hade su ba,amma kuma dik ranar da kwanan gidan su ne mamar tasu ce take shirya masa dik wasu abinda ya kamata a fannin girke girke da dama sauran abubuwa.amma kuma indai yana gidan dayar matar tasa to su kawar tata ce ke girkin su ba tare da mamar tasu ta sa masu hannu ba.
saida ta kammata bayan ta shirya masa komai takai masa dakin sa,sannan tayi gyare gyaren gidan kama daga kan shara har zuwa kan wanke wanke,sannan kuma ta cika masu ruwan gidan nasu da pompon dake cikin ko wanne gida dake unguwar.
wanka ta shiga tayi bayan ta fito ta tarda harma abin nata ya wuce jami'ar da yake koyar wa ta poly,sai kuma oum dake kwance a parlo tana baccin ta hankali kwance alamun ba yanxu zata wuce wurin aikinta ba kasancewar yau juma'a ce.
saida taci abincinta tsaf kamin ta sake bin lafiyar katifarta bayan sunyi waya da danish ya kuma shaida mata bata da wani lecture din sai karfe biyu wato bayan sallar juma'a bacci yayi awon gaba da ita.
A lokacin da ta tashi a bacci wuraren dayama harda wani abu wanda tayi mamakin irin baccin da tasha yau din. kuma ma wani abin mmk babu kowa a gidan haka nan yake a bude alamun oum ma ta fice batare data shaida mata ba ballantana ta rufe gidan sbd tsaro.
a gurguje ta shiga wanka,wanda ta jiyo sallamar daniyah wanda hakan ya sata karashe wankan nata ta fito daure da zanin atamfarta fuskarta shimfide da farin ciki dikda rashin karfin jikin nata tace "maraba da zuwa kawar arziki! sannu da zuwa"
shaan ta fada a lokacin da take zama bakin katifar tata da daniyah ke zaune cikin shirin fita makaranta. tana daddanna wayarta.
itama da annashuwa tace "yawwa sannu manyan mata ya gajiyarki ta jiya...?"
"lafiya qlaou wlhi"
"ina oum dasu abi tare da sauran yan gidan ku din can" "dik lafiyarsu qlaou yasu anty da kuma kanwa ta...?"
"suma dik suna lafiya,kuma ma anty tace in gaisar mata da oum gashi kuma banji motsin ta ba bacin kuma yau friday tin 12 suke tashi a wurin aikin nasu"
"kuji ki da wata tambayar kina nuna wa kamar baki san komai ba ke kam" shaan ta fada a lokacin datake dan daure face alamun taji babu dadi har cikin ranta.
ringing din da wayar shaan ne ya dauka ya katse ma daniyah maganar dake neman fitowa daga bakinta,sunan wacce ya fito ne yasa ta daukar wayar da fara'arta tace "barka da juma'a antyn mu ina wuni...?"
daga ta can bamgaren kuwa cikin wata kamilalliyar murya naji an ansa mata da "lafiya qlaou kanwata ykk yasu mamanki da sauran yan uwanki...?"
"dik lafiyar su qlaou,ina yaran mu dasu _ya Bassam_ ...?"
"dik lafiyar su qlaou yau an kawo ma aminiya ziyara kenan...?" aka fada daga ta can bangaren.
"eh wlhi zamu wuce makaranta ne ma,ga nan shaan din" ta fada a lokacin da take karama shaan dake zuge zip na rigarta wayar a kunnen ta.
"ina wuni _Anty Batool_ ya su yaya da kuma yaran...?" "lafiya qlaou kanwata yasu anty bahira (oum) dakuma su abi...?"
"lafiyan su qlaou ina su _khairat_...?" "dik suna nan qlaou gasu nan ma ku gaisa kamin ki wuce makarantar kar na sa kuyi latti"