Charpter 26_30

32 3 1
                                    

*OUM MUMTAZ...✍🏽✍🏽*

*RAYUWAR DARAKHSHAAN*
      
  _chapter 26-30_

A wannan ranar hankali na idan yayi million to kuwa tabbas ya lalace dikda bansan mai ake kira da ainahin wani abu wai shi kishi ba!

Abin kuma dake kuma bani takaici ashe wai Abi da Oum dik suna da labarin auren nasa amma suka ki fada man da bansan manufar su tayin hakan ba!! Abin kuma da har yau idan na tuno yakan bataman rai Oum a matsayin ta na uwa tasan kuma cewa gidan da ake shirin kaini din bani kadai bace amma kuma ace common dan gyara ko kuma wasu magunguna irin na mata ballantana azo kan turaruka bazata iya hada man su ba?

A lokacin ne na kira Qaseem ina kuka sosai ina tambayar sa mai yasa zai man haka amma sai ya bani hakuri dik yabi ya kalallame ni kan wallahi shima ba son matar da aka aura masa yake ba auren dole mahaifiyar sa tayi masa.

Wacce na kwana da sanin daman tin can bata kauna ta sbd Mmn Musa data same ta har gida kan ta raba danta dani wai karna bata mata shi tin a wancan lokacin da nayi mata rashin kunya.

Don haka sai nima naji dan dama dama tinda shida bakin sa yace man auren dole akayi masa bai son ta kamar yadda yake so na,daurin aure kawai akayi inda bayan sallar la'asar wato karfe hudu muka kama hanyar garin su Qaseem da ba samu wani nasiha ko kuma addu'oi daga iyayena ba ballantana yayu na tinda dama ni banda wani shakuwa tsakani na dasu! Sai Anty batool yar gidan Umma halima data zo daga can Gombe wacce a lokacin tana da yarinyarta guda daya! Wani set na foodplask mai guda uku tare da tea plast sai kular nan da ake zuba ruwan zafi dasu cups dai plate wanda ake sayar su  dunkule dinnan tare da wani tukunya mai guda uku a ciki matsayin gudummawarta!

Ai kuwa sosai naji dadin wannan kyautar tata! Inda muna isa kuwa kuw aka wuce dani gidan surukai na dana tadda wani tashin hankali ma acan daya girmi tunani na!

Domin kuwa surukata mahaifiyar Qaseem muka tarda mutane zagaye da ita ana ta faman bata hakuri sakamon kukan da takeyi,inda take furta kalmomi na tsana karara kaina,wanda tayi mana korar wulakanci muka don haka sai su Umma suka fito dani din dikda bamu san ainahin abinda ya faru ba amma mun san ba lafiya ba.

Zaunar dani Umma tayi inda ta soma man nasiha dana gaza samun sa daga wajen wacce ya cancanta...

Haka nan dai gidan babu laifi amma hakan bai sani ganin irin local na kayan da aka man ba tinda dai naje gidan yayu na dik naga abinda aka masu wanda hakan yasani kullatar Oum da Abi har cikin zuciyata na kuma tabbatar ma kaina tabbas basu kaunar tawa...!

Da shike ba wasu kawaye ne dani na azo a gani ba sai ya zamana wasu daga cikin dangin mu ne suka zauna man,wanda kuma kaf cikin su nice yarinya... ni dama already nasan Qaseem bashi da gidan kansa na hayane yace zai kama mana muyi rayuwar mu kamin Allah ya hore masa,sa shike gidan irin mai plate guda uku ne sai ya kama guda biyun,daya nawa daya na matar tasa da yace an aura masa mai suna Ummikulsum...

A ranar itama aka kawo ta da naga tsantsar abin al'ajabi nida nawa family din sbd dik dangin su Qaseem din suna daga bangaren ta sai faman zuba mana habaici suke kamar su doke mu daga nan amma cikin mu babu wanda yace masu qala sbd gargadin da Umma tayi mana kamin ta tafi kamar ta sani...

Can wajen karfe goma na dare kowa ya watse bayan anyi su sayan baki kamar yadda akeyi inda a lokacin ma abokan nasa 5k suka bama kawaye nah...da shike dama ba wasu reasonable mutane bane akoi sauran yarinta dake yawo akan su,sbd shi kansa Qaseem din a lokacin bai wuce 26yrs ba...

Abin da ya masifar bani haushi a farko shine daya ce wai inzo muje plate na Ummiqulsum sbd yana so ya hade mu yayi mana nasiha... (hakan na nufin itace uwar gida kenan...) badon naso ba,sai don banson na fara yi masa musu tin daga ranar na bisa zuwa nata plat din,sosai kuwa naga kokarin iyayen ta sbd yadda aka kawata mata nata part din,a parlo muka same ta zaune kan kujera ta 2seater tana nannade cikin lafaya ga wani irin sihirtaccen kamshin dake tashi a inda take,inda ni kuma nake sanye da doguwar riga ta shadda tare da lullubin gyale... ga wani irin kwaliyan dake kan fuskata sam sam kamar ba amarya ba ...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 24, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RAYUWAR DARAKHSHAANWhere stories live. Discover now