CHAPTER 1_5

133 5 5
                                    

_typing✍️_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®️🏝️

🏝️ *ZAFAFA WRITTERS FORUM*....✍️

*_Z• W• F•🏝_*

🟣🟣🟣🟣🟣

*DUNIYAR NAN*

🟣🟣🟣🟣🟣

*Tsarawa da rubutawa*

*Daga alkalamin*

*LEEMART PINKY*💞💕

_Ɗan tsokaci duniyar nan sabon salon littafi ne Wanda komai na rayuwa yakunsa banyi shi dancin zarafin kowa ba duk Wanda yaga wani hali daga rayuwarsa yayi hakuri arashi ne fatana naga nakawo gyara ga al'ummah_

*Daga farkon wannan littafin har karshen sa sadaukarwa ne ga kungiyar mu ta Zafafa writters forum alkairan Allah yakai maku Allah ya d'aga darajar ku Allah ya tsaftace alkalaminku yakara maku basira da dauka'ka kuyi yanda kukeso da Wannan book din na baku shi kyauta pinky leemart taku ce*💗💗

Chapter 1_5

*Bismillah'rahamanir'rahim*

______________📝 "Rugar bubu ardo" ruga ce data Tara manyan fulani makiyaya Allah yayi'wa garin baiwar arzikin kiwo Allah ya albarkaci garin da kayan more rayuwa kala_kala kai zakace ba rugar fulani bace Allah yayi'wa mutanen garin Kyau mazan su da matansu kyawawane zaka dauka larabawane ga fari ga gashi ga tarin arziki na gani na fad'a Masha Allah",

Wata tsohuwa na hango a bakin wata bukkar zana a zaune tana Shan fura wata budurwa da bazata wuce kimanin shekara ashirin ba tana a gefenta sai famar zuba takeyimata.

Budurwar ce naji tacewa tsohuwar "INNAH yanzu shikenan bazamu sake ganin Kawu modibo ba? Shikenan sun shige burni bazamu Kara ganinsu ba shida yaransa gaba daya ni gaskiya INNAH bazan yarda ba sai naje burni wajen Kawu inganshi",

Wani kallo tsohuwar tabi wannan yarinyar dashi kana ta nisa tace

"Kinga Innawuro ki kiyayeni da maganar modibo anan bani ba modibo tunda har ya zabi farin cikin matarshi bisa ga ni Yar uwarshi Dan haka na yanke zumuntar dake tsakanin mu.

Waro ido waje wace aka Kira da Innawuro tayi kana tace "haba INNAH wannan wace irin magana ce kikeyi Dan Allah? kiyi hakuri wallahi nasan Kawu bayayi hakan bane Dan ya kuntata maki bane sai dan yanayin aikinsa Amma nasan har yanzu muna a zuciyarsa musamman ma baffa da kullun sai yayi maganar sa Yana addu'ar Allah yasadasu kafin ya mutu.

Murmushi INNAH tayi tace yaro_yarone.

Maida dubanta INNAH tayi ga Innawuro kana tace;

"Innawuro bakisan waye madibo ba modibo mutum ne wanda ba ruwansa da lamarin kowa indai har matarshi zata samu farincikin bashida abunda yake so da kau'na a koda yaushe irin yaga wannan matar tashi tana dariya tana farinciki touu ko miye zai iyayi maka idan har kana Saka matarshi a farin ciki mutanen Rugar nan da yawansu sunci kyaututuka daga madibo saboda matar sa matarsa mutunce Mai yawan son wasa da dariya kuma tana son arika Bata labarai irin wayanda suka shude touu mutanen gari dayawa sun san hakan tun kafin ta auri modibo shine fa da sukayi aure yakanje yana nemo irin tsofafinnan nada wayanda sukasan tarihin "da" suna zuwa gidansa suna Bata labarin idan na dariya ne tayi dariya idan na Kuka nema haka nisawa tsohuwar tayi kana taci gaba da cewa
"Idan suka gama Bata labarin haka zakiga modibo ya dibi dukiya Mai yawa yabawa mutanen sukuwa suyita murna har suna rokon gobe su dawo ta dalilin hakan akwai wayanda sukayi kudi da kudin modibo da yake Basu bazan taba mantawa ba akwai wata kyautar da modibo yataba yiwa wani kad'o da yazo daga burni shine matar sa tace tanason a nemo mata Wannan bakon dayazo daga burni tanason zai bata labarin burni aikuwa ingaya maki da yazo yabata zokiga irin kyautar da madibo yayi'wa mutunen wace duk wani dake Rugar nan Saida yashiga mamaki irin tarin dukiya ta modibo da bayajin wuyar fitar da ita saboda wani Dan karamin dalili nashi",

DUNIYAR NAN labari ne inda yaron gida zaiyiwa mai aikinsu ciki iyayensa suce Where stories live. Discover now