*ZAFAFA WRITERS FORUM*...
*Z W F*🏝️
*Typing*✍️
🟣🟣🟣🟣🟣
*DUNIYAR NAN*
🟣🟣🟣🟣🟣*Tsarawa da rubutawa*
*Daga al'kalamin**LEEMART PINKY*💞💕
_dan tsokaci duniyar nan sabon salon littafi ne Wanda komai na rayuwa yakunsa banyi shi dancin zarafin kowa ba duk Wanda yaga wani hali daga rayuwarsa yayi hakuri arashi ne fatana naga nakawo gyara ga al'ummah_
*Daga farkon wannan littafin har karshen sa sadaukarwa ne ga kungiyar mu ta Zafafa writters forum alkairan Allah yakai maku Allah ya d'aga darajar ku Allah ya tsaftace alkalaminku yakara maku basira da dauka'ka kuyi yanda kukeso da Wannan book din na baku shi kyauta pinky leemart taku ce*💗💗
Chapter 5_10
*Bismillah'rahamanir'rahim*
______________📝 "d'aga hannu sa Deen yayi kana kuma sai yasauke kamar mai wani tunani ganin nayi yafara dube_dube Kamar wani marar gaskiya sai Kuma yayi gyaran murya yace.",
"Assalamu alaikum" yakara yin sallamar yaji shuru daga hannunsa yayi yafara bubuga Yar kofar da sukayiwa bukarsu daga INNAH har baffa bamai kama wani ita Barkido ba ama maganar ta saboda katifa ta d'aga tashiga kasan gadon karfe irin na Fulanin na Mai rumfa ta boye
Tura kofar dak'in Deen yafara aikuwa INNAH ta saki fitsari a tsaye jikinta sai mazari yakeyi tana cewa "shikenan mukan kwanan mu yazo karshe wayyo baffa kashe mu za'ayi innalilahi'wa'inna'ilaihir'raju'unnn tsawa baffa ya daka ma'ta kana yaji wani karfi ya ziyarci zuciyarsa dakewa yayi ya dumfari kofar yace",
"Waye nan?"
Deen kuwa saurin cewa yayi "nine"
"Kaine wa?",
"nine Saifudeen baffa kubude"
Aikuwa baffa yanajin hakan dagashi har INNAH da Innawuro rigangan fitowa daga d'aki sukeyi har suna Shan tuntube baffa Yana bude dak'in ya rungume Deen farinciki darshe a zuciyarsa INNAH kuwa sai famar washe hakora takeyi baffa ne yace"
"Saifudeen nake gani a zahiri ko mafalki nakeyi?",
Murmushi deen yayi kana yace uhumm "ba mafalki kakeyi ba baffa nine Saifudeen ne baffa nasameku lafiya?" Lafiya kalau saifu ya kabaro mutanen gida?
Shuru Deen yayi na Dan wani lokaci take yanayin fuskarsa ta chanza kallo daya zakayi Masa ka gane Yana cikin damuwa kallon sa baffa yayi kana yace "lafiya kuwa Saifudeen meyake damunka?
Murmushi deen yayi ya maida dubansa ga INNAH da har Yanzu shi take kallo har 'kasa yakai ya gaidata ta karba sai murna takeyi tanayi Masa wasar d'a da uwa Innawuro kuwa tuni ta shagala da kallon Deen yagama tafiya da imaninta shigarsa ta Yan birni ta bala'in burgeta tsawa INNAH ta daka mata kana ta dawo hayacinta INNAH ce tace " kikawo Masa tabarma da ruwa kin tsaya kina kallonsa kamar kin samu tv" sunkuyar da kan'ta 'kasa Innawuro tayi har ga Allah ta tsani irin wannan abun da INNAH keyi mata gaidashi tayi kana ta wuce daki Dan dauko Masa abun Zama.
Murmushi Deen yayi kana ya dubi baffa yace baffa wai Innawuro ce ta girma hakan?",
"itace kuwa Saifudeen kaga ta Kara girma koh ? bakamar yanda ka santa ba touu Deen Baku zuwa wajen mutane kojin d'uriyarku ba ayi"
Murmushi INNAH tayi tace "baffa kenan ai shi ba laifinsa bane laifin iyayensa ne idan suka ce yazo ai dole yazo ai kowa yabar gida gidama yabarshi",
", Murmushi Deen yayi kana yace "Allah ba haka bane Gwago ni bana 'kasar ne yanzu hakan iyakana wata shida da dawowa daga londom shekarata biyar acan",
Zaro ido waje Innawuro tayi da fitowarta Kenan daga daki ta shimfida Masa tabarma kana tace "London Dan Allah Yaya idan zaka koma kaje dani wallahi duk duniya ba kasar danake son zuwa kamar London tunda wani malaminmu da yake zuwa koyar damu yaki da jahilci kullun yazo sai yabamu labarin london da irin haduwar kasar yanda yake bamu labarin Kai zakace ba a duniya bane wallahi Kuma Yaya bakaga shigarshi ba shima irin shigarka yakeyi ta Yan gayu",
Harara INNAH ta watsa mata kana tace "touu Fadi ba atambayeka ba kinsan Allah Innawuro idan Baki raba kanki da wanann surutun ba sai na Saba maki",
Sunkuyar da kan'ta 'kasa Innawuro tayi har ga Allah taji kunyar abunnan da INNAH tayi mata agaban Deen Amma babu yanda zatayi tunda mahaifiyar tace", kasa da kan'ta tayi tace Allah yabaki hakuri INNAH.
"Ameeen"
Baffa kuwa nisawa yayi yace Barkido ake rika hakuri da yara kinji? tace touu baffa",
Murmushi Deen yayi kana yace "Innawuro kema insha Allah zakije london dinnan Dan naga kinason garin sosai"
"Dan Allah Yaya dagaske kakeyi gyada mata kansa yayi alamar ehhh", tace yawwa Yayana nagode",
Baffa ne ya katse masu surutun da sukeyi ta hanyar cewa "Saifudeen kai kuwa Mai yakawo ka wannan garin a Yanzu Mai cike da barazanar rayukan mutane ? Nayi mamakin ganinka a Yanzu saboda wannan garin Yana daya daga cikin garuruwan da akeyi masu barazana da rayukansu Idan yau ba ashigo akayi kashe kashe ba touu gobe za a shigo akashe Mana Yan uwanmu fulani akwashe masu dabobinsu munaji muna gani ba yanda muka iya Yanzu hakan Yan bindigar basuyi awa daya ba da suka gama kashe_ kashensu a kauyen dake kusa damu suka tafi",
Zaro ido waje Deen yayi subuhanallah innalilahi'wa'inna'ilaihir'raju'unn itace kalmar da kawai yaketa nanatawa dube_dube yafara kana yace "kuma baffa shine kuke zaune a cikin garin har yanzu ?
"Maida dubansa baffa yayi ga Deen kana yace "touu ya muka iya Saifudeen idan muka bar garin Ina zamuje kada ka manta nan ne garinmu na gado da muka gada tun kakanni idan bazaka manta ba mahaifinmu shine sarkin garinnan da ya mutune akayi Mana juyin mulki sarauta tabar gidanmu saboda yanzu ba mulkin gaskiya akeyi ba Amma da hakanne da yanzu nine zan gadi sarautar Rugar buba ardo ai buba ardon ma sunan mahaifinmu ne",.
Kaga kuwa har yanzu mu Yan sarauta ne kasarnan kasarmu ce inaji a jikina kujerar mulkin ma tayi kusan dawowa gidanmu",
Kaga kuwa babu damar mugudu mubar garin da naso muyi hakan Amma kuma sai zuciyata takasa amince wada hakan",
Gyara Zama Deen yayi saboda dama shi mutum ne wanda yakeson Jin labaran da suka shude harde 'kafarsa yayi ya gyara zamansa kana yace "inajinka baffa cigaba",
Murmushi baffa yayi kana yace uhumm "Saifudeen labarin da tsawo yake Amma Yanzu ka Sanar damu make tafe dakaine Dan kayi sauri kabar garinnan kada ayi mutuwar kasko",
atake yanayin Deen ya chanza Dan labarinnan da sukeyi da baffa har yasa ya manta damuwar sa wasu hawaye ne suka Fara fita daga idanunsa daga baffa har Barkido da Innawuro hankalinsu ya matukar tashi ganin Yana Kuka balam ma Innawuro da keji kamar ta daura hannu akai ta fasa ihu da tafara ganin hawaye na sauka daga idanun yayan nata",
Baffa ne yace "subuhanallah meke faruwa Saifudeen?",
d'ago da jajayen idanunsa Deen yayi da suka rine kamar Jan barkono kana yace " Dan Allah baffa kace Masa kada ya aura Mani ita wallahi baffa bana sonta wasu hawaye masu dumi kebin fuskar Deen kana yaci gaba da cewa wallahi kaddara ce baffa Amma bazan iya auranta ba ba kalar macen da nakeso bace idan aka aura Mani ita wallahi zan kashe ta Kona kashe kaina",
Waro Ido waje baffa yayi kana yace kai................
Comment dinku Yana mani kadan kodai na dakatar da typing dinne ?*It's me leemart pinkyy*
Commmet
Vote
Shere🙏🙏
YOU ARE READING
DUNIYAR NAN labari ne inda yaron gida zaiyiwa mai aikinsu ciki iyayensa suce
ContoDUNIYAR NAN labari ne da ya shafi rayuwar da akeyi a Yanzu an dauki rayukan mutane tamkar na dabobi yaran masu kudi suna wulakanta ya'yan talakawa akwai 'kalubale sosai acikin sa inda fulani zasu gwada zallar ikonsu Akan rayukansu da kuma na dabobi...