chapter 21_25

10 2 0
                                    

*ZAFAFA WRITERS FORUM*...

           *Z W F*🏝️

*Typing*✍️

🟣🟣🟣🟣🟣

         *DUNIYAR NAN*
          
                🟣🟣🟣🟣🟣

*Tsarawa da rubutawa*
      
            *Daga*

*LEEMART PINKY*💞💕
     

_dan tsokaci duniyar nan sabon salon littafi ne Wanda komai na rayuwa yakunsa banyi shi dancin zarafin kowa ba duk Wanda yaga wani hali daga rayuwarsa yayi hakuri arashi ne fatana naga nakawo gyara ga al'ummah_

*Daga farkon wannan  littafin har karshen sa sadaukarwa ne ga kungiyar mu ta Zafafa writters forum alkairan Allah yakai maku Allah ya d'aga darajar ku Allah ya tsaftace alkalaminku yakara maku basira da dauka'ka kuyi yanda kukeso da Wannan book din na baku shi kyauta pinky leemart taku ce*💗💗

           Chapter  21_25

*Bismillah'rahamanir'rahim*

______________📝 "wata ranar jumma'a ce da Ja'afar baizai taba mantawa da itaba watau Baffah itace ranar da yaga mutanen garin sunyi dandazo mazansu da matansu manya da yara sunzo suka sakashi agaba akan wai a dole sai yasauka daga kujerar mulki yabawa asalin mutanen garin Baffah kuwa baiyi mamaki ba da jin zancen su dama tun kafin mahaifin shi ya rasu yasanar dashi zuwan Wannan ranar shiyasa baiwani Jin tashin hankali ba da jin zancen su",

Maida dubansa garesu yayi yayi shuru can kuma yayi gyaran murya irin na manya dinan kana yace "touu alhamdulilah yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki Wanda yayini kuma yayi mutanen duniya gaba daya.  dukansu kallon juna suka fara da jin maganar Baffah kana yaci gaba da cewa "iya halaci kunyi Mana a cikin garinnan kuma bamuda bakin gode maku tabbas kun tabbatar Mana da cewa duk wani bafulatani Yana kaunar Dan uwansa fulani wannan maganar haka take mutane da yawa Suna fadar hakan game da rayuwar fulani har hausawanmu sukeyi Mana sherri akan cewa mu fulani jininmu kawai muka sani kuma shi mukeso duk inda bafulatani yaga Dan uwansa tou tabbas sai sun tsaya sun gaisa Koda kuwa basu san juna ba wannan shi ake Kira da mutunta juna tabbas fulani munada wannan halayen kuma nayi farin cikin sosai da irin daga darajar mahaifina da kukayi ku'ka nuna Masa so da kuma kau'na Wanda har yanzu da bashi raye akwai sonshi a zuciyarku tou mu bamuda abun gode maku kuma insha Allahu ni Ja'afar nayi maku alkawarin zai goyi bayanku Akan duk Wanda zaku daura Akan kujerar mulki kuma zamuyi masa biyaya",

Gaba daya mutanen wurin Saida suka zubar da hawaye har wasu daga cikin su suke ganin Basu kyauta ba Suna ganin basuyi Masa adalci ba saboda mahaifinshi shine mutumin da yakawo masu duk wanici gaba acikin wannan garin nasu Amma ba yanda suka iya dole Dan garin yakamata yaci gaba da mulkar garin haka kuwa akayi Baffah ya sauka daga kujerar mulki yabawa asalin Dan garin sosai mutanen garin sukayi mamakin Baffah na ganin Bai wani tayar da hankalinsa haka rayuwa taci gaba da zuwar masu kamar kar a daura mutumin mulki shikenan tattalin arzikin garin yafara ta barbarewa ga kashe kashen da akeyi acikin garin Wanda mutanen garin suke tunanin dasa hannun wannan sarkin da suka daura Amma har yanzu basuda tabbas shiyasa sukaci gaba da bincike

Bangaren Baffah kuwa Yananan zaune da yaransa cikin farin ciki da nuna masu kulawa sosai yake nuna masu gata Balkisu Barkido da kuma Yusuf Modibo haka dai sukaci gaba da rayuwarsu har Yusuf Modibo ya fitar da mata sosai Baffa yayi farin ciki ya ware Masa waje acikin gidansu ya gyara masu ko'ina akayi Masa aure aka kawo Masa matarsa haka sukaci gaba da Zama acikin gidansu ita kuwa Balkisu kullun cikin korar maza take idan sukazo neman ta wanda har Saida Baffah da kansa yayi mata fada sosai gashi kullun cikin masifa take da matar kaninta madibo tun matar najin kunyar ta Bata tanka mata har ta cire kunyar taci gaba da tanka ta idan Suna masifa duk rugarnan ba mai iya yimasu magana su daina idan ba Baffa gashi modibo bayanan Yana birni wajen neman ilimin zamani na gaba da secondry watau jami'a sosai Baffa yakeyi Barkido masifa Akan nuna rashin son da takeyiwa matar kaninta kuma ba tare da tayi mata komai ba haka dai sukaci gaba da rayuwa yau Dadi gobe ciwo.

DUNIYAR NAN labari ne inda yaron gida zaiyiwa mai aikinsu ciki iyayensa suce Where stories live. Discover now