*ZAFAFA WRITERS FORUM*...
*Z W F*🏝️
*Typing*✍️
🟣🟣🟣🟣🟣
*DUNIYAR NAN*
🟣🟣🟣🟣🟣*Tsarawa da rubutawa*
*Daga al'kalamin**LEEMART PINKY*💞💕
_dan tsokaci duniyar nan sabon salon littafi ne Wanda komai na rayuwa yakunsa banyi shi dancin zarafin kowa ba duk Wanda yaga wani hali daga rayuwarsa yayi hakuri arashi ne fatana naga nakawo gyara ga al'ummah_
*Daga farkon wannan littafin har karshen sa sadaukarwa ne ga kungiyar mu ta Zafafa writters forum alkairan Allah yakai maku Allah ya d'aga darajar ku Allah ya tsaftace alkalaminku yakara maku basira da dauka'ka kuyi yanda kukeso da Wannan book din na baku shi kyauta pinky leemart taku ce*💗💗
Chapter 10_15
*Bismillah'rahamanir'rahim*
______________📝 "d'aga hannu baffa yayi yakaiwa Deen mari from no where Deen yaji saukar mari a fuskarsa dafe fuskarsa Deen yayi ya dago da jajayen idanunsa dafe da kuncensa ya zubawa baffa rinanun idanunsa.
Wani kallo baffa yafara jifansa dashi kana yace " kana hauka ne Saifudeen ? Kasan mekake fada kuwa ? touu tun wuri Ina Mai shawartanka da ka canza tunani kasan hukuncin Wanda ya kashe wani kuwa ? ko kasan hukuncin Wanda ya kashe kansa a addinance ? touu duk hukuncinsu daya ne da wanda yakashe kansa da kuma Wanda yakashe wani duk da ganga touu zaishiga wuta kuma zai dauwama a cikin wutar Dan haka ko kanason ka kasance daya daga cikin wayanda Zama zauna acikin wuta nisawa baffa yayi kana yaci gaba da cewa "Dan haka ka gagauta tuba ga ubangijinka sannan idan zaka Fadi magana kafara tauna maganarka kafin ka fadeta",.
Yaci gaba da cewa "wannan wace yarinya ce kake cewa baka so kuma bazaka aura ba ? Kuma metayi maka hakan ?
" Duban baffa deen yayi kana yace "wata bankadadiyar yarinya ce Yar aikin gidanmu itace Abie yakeson ya hadani da ita",
Hankalin Inna da Bappha yayi matuƙar tashi dajin wannan labari
Innawuro ko tanaji yafurta ance zai aure wata taji wani irin haushi da takaici wani ƙululu yazo ƙirjin ta ya tsaya hakanan kawai batasan daliliba hakan ba.
Bappah gyara zama yayi bayan yayi gyaran murya kana yace,"gaskiya Moɗibbo bai kyauta ba,bayi tunani ba,yanzun ka tashi ka koma gida,zanzo in samu maɗibbo dakai na,kome kenan zamuyi magana,ai bai isa don yana mahaifinka ba,yai maka aure da yarinyar da baka so,ko mu nan a ƙauye mundena auren dole balle ku da kuke burni,kana ga karatun boko da arabic,ga uwa uba waye wa".
Nan Bappha ya rinƙa kwantar ma da DEEN hankali da kalamai masu sanyayya zuciya,take Deen yaji damuwar shi ta yaye ,nauyin dake zuciyar shi kaso casa'in da tara cikin ɗari babu shi.
Shiya sa tun farko ya yanke hukuncin zuwa wajan Bappha tunda Abie ya bijiro da rigimar sai ya auri house girl din gidan su,yasan ba wanda zai hana sai Bappha.
Daya tashi tafiya kana ya dubi Innawuro dake zaune gefe ta zuba mai lulu eyes dinta ko ƙyaftawa batayi yai murmushi yace,"Innawuro ɗauko kayanki mutafi tare".
Tsalle da ihun daɗi ta buga ta faɗa ɗakin su da gudu.
Murmushi yayi ya girgiza kai.
Take yanayin INNAH ya canza tayi kicin-kicin da rai ta haɗe fuska kana tace,"ba inda zataje Saifudeeni,idan ta tafi wazai ri'ka tayani aikin gida ,kuma niba isasar lafiyayya ce dani ba".
YOU ARE READING
DUNIYAR NAN labari ne inda yaron gida zaiyiwa mai aikinsu ciki iyayensa suce
Short StoryDUNIYAR NAN labari ne da ya shafi rayuwar da akeyi a Yanzu an dauki rayukan mutane tamkar na dabobi yaran masu kudi suna wulakanta ya'yan talakawa akwai 'kalubale sosai acikin sa inda fulani zasu gwada zallar ikonsu Akan rayukansu da kuma na dabobi...