༺༻🌹༺༻
*🇿UℬAℛ*
*🇭AWAYE𝒩A*
֍
༺༻🌹༺༻
, . - . - , _ , " ;
) ' - . .> ' '(
/ 🌹🌹 '\
| 🌹 🌹🌹 |
\ 🌹 / /
'=(\ /.='
'-;'.-'
')| ,
|| _🍃. -'
,_|| \_,/*Տᴛ⌾ℛℽ & 𝒲ℛⅈᴛᴛℰℕ*
*ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩*©®-Aɴᴀ ᴛᴀʀᴇ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛
(wє ѧяє ṭһє ɞєśṭ ѧṃȏṅɢ ѧʟʟ wяıṭєяś)📚
https://m.facebook.com/Anatarewritersassocian/
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ*_Fadila αlῖϒῠ ϻῠsα (ϻϒ δῖlαlα)❤️ kϵ δῖͷ tα ϻῠsαϻϻαͷͼϵ gαrϵͷῖ._*
*🌹🇵ᴀɢᴇ ☞13➪14*
*𝚠𝚊𝚗𝚎𝚗𝚎 𝙰𝚕𝚑.𝙼𝚊𝚒𝚗𝚊?*
Alh.maina Muhammad shi ne k'ani ga Alh. Aliyu Muhammad, kuma mahaifi ga Lateef (mijin Haseena).
Mutum ne mai dukiyar gaske ba shida matsala ga kowa, sai dai ta wani fannin yana da k'ank'amo kad'an (rashin sakin abun hannu) duk da cewa yaransa mata yana wadata musu ta ko ina musamman ta b'angaren kashe kud'i.
Alh.Maina na zaune a unguwar Shagari quarters, yana da mata guda hud'u, matarsa ta farko ita ce Haj.Lantana, macece mai sauk'in kai ta wanni fannin kuma bata d'aukar raini bare hulak'anci.
Jamila ita ce matarsa ta biyu mace ce masifaffiyar gaske ta bugawa a jarida gata da rashin tarbiyya da fitsara ko da kuwa fad'a suke da Alh.Maina batak'i su danbata a waje ba, duk da dai shi ma ya san wajen da ya aurota babu tarbiyya ko kad'an, auren ne Allah ya nufa aka yi, bayan tsahon wani lokaci su ka sami sab'ani da Alh.Maina ya sake ta.
Daga nan ne kuma ya auro Halima ita ma bata wani juma'a ba ya sake ta ya auro Haj.Hindu, mece ce me kishin tsiya akan komai har akan yara ta wani fannin kuma tana da hak'uri.
Daga kanta ne kuma bai k'ara saki ko auro wata ba, ya ke zaune da matansa guda biyu, Haj.Lantana da Haj.Hindu, kowacce daga cikinsu shi ya kaita saudia, a cikin yaransa kuwa Lateef kawai ya tab'a kaiwa.
Alh.Maina shahararren mai kud'i ne wanda sunansa ya zaga ko ina, yana da kamfanin shinkafa da Taliya nasa na kansa mai suna Maina Group, wannan yasa ya tara dukiya da kadarori wanda suka had'ar da gidaje da filaye da sauran abinda ba a rasa ba.
Alh.Maina yana da yara ashirin da hud'u, Haj.Lantana ta haifa masa yara goma sha uku maza bakwai mata shida, Ibrahim ta fara haifa sannan Lateef, Kamal, Sadiq, Khadija, Ahmad, Hauwa, Hafsat, Zuhra, Zulaihat Mukarram, Aminu, sannan Abida.
Jamila ta haifa masa yara biyu dukka maza Yazid da Bilal.
Sai Haj.Hindu inda ita ma ta haifa masa yara tara maza hud'u mata biyar, Nasira ita ce babba a d'akinta daga ita sai Anwar sannan Ishaq, Rahma tana binsu sai Na'ima, sannan Mus'ab da Husna, Anas da Bilkisu.
Idan aka biyo ta jerin cikin gida kuwa Ibrahim shi ne babba yana da shekaru talatin da tara, sannan Lateef me shekaru talatin da shida, Kamal na da shekaru talatin da biyar, dukkaninsu dai tazarar ba yawa, Sadiq shi yake binsa sannan Khadija, Ahmad, Hauwa, sai Yazid sannan Hafsat me binsa sai kuma Bilal, Zuhra, Zulaihat, Nasira ita take bin ta a cikin gidan, sannan Mukarram, Anwar, Aminu, Isha, Rahma, sannan Na'ima, Abida, Mus'ab, Husnah, sannan Anas da Bilkisu.
Alh.Maina ya aurar da yara goma, guda tara duk na Haj.Lantana ne wanda suka rage mata ba aure a d'akinta zulaihat, Mukarram, Aminu da Abida.
A d'akin Haj.Hindu kuwa ta aurar da Rahma me shekaru ashirin wadda ita ce ta hud'u a yaranta, kasancewar ta samu miji da wuri yasa aka yi mata aure.𑁍𑁍𑁍𑁍𑁍
Auran Lateef da Haseena ya faru ne sakamakon rashin jituwar mahaifansu Alh.Aliyu da Alh.Maina tun daga lokacin rabon gadon iyayensu, wannan yasa sauran 'yan uwansu suka bada shawarar a had'a yaransu aure ko Allah yasa su shirya daga gabar da suke ta tsahon lokaci.
Duk da cewa mahaifiyar Haseena Haj.Asiya ba k'aunar auren take yi ba kamar yadda shima mahaifin nata Alh.Aliyu ba so yake ba, sauran 'yan uwan Haseena duk basa k'aunar wannan had'i da za a yi, haka ma ita kanta Haseenan ba k'aunar auren take ba tun da kuwa tana da saurayin da take so, sai dai kuma abinda Allah ya nufa ba tsumi ba dabara sai ya faru.
B'angaren Lateef ma ba son auren suke ba, har gwara ma Alh.Maina ya yi farin ciki da hakan duk da irin gabar dake tsakaninsa da d'an uwansa duk da dai shi daman ba wai a son ransa hakan ke faruwa ba.
Shi kuwa Lateef sam! bai yi farin ciki da hakan ba tun da kuwa yana da wadda shi ma yake so Naseeba 'yar wajen k'anwar mahaifiyarsa Haj.Batula, ya bi umarnin mahaifinsa ne kawai kamar yadda ya saba yi masa.
Tun Lateef da Haseena basa k'aunar junansu har Allah ya saka musu son junansu tamkar ba had'a su aka yi ba.
A kwana a tashi cikin ikon Allah soyayya ta fara k'arfi tsakaninsu har ta kai da ko waya suke yi basa iya barin junansu in ba dole ba.
Ta haka ne kuma sauran 'yan uwanta wasu daga ciki suka fara sakko da zuciyarsu wajen aminta da auren, musamman yadda mahaifin Lateef yake da dukiya duk da cewa shi aikin da yake yi ba wani aiki ne me kawo kud'i sosai ba malamin makaranta ne na secondary, sai dai rufin asiri.
Tun a baya mahaifinsa ya yi k'ok'ari ya zauna a kamfaninsa amma Lateef yak'i sabida ya fi son aikin gwamnati.
A haka dai aka yi auren Lateef da Haseena, cikin ikon Allah suka yi zamansu lafiya, tamkar ba su ba.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba bayan wannan aure ba a kaiwa Hassena gara ba kasancewar basu sami kud'in da za su had'a mata ba.
Wannan dalili ya k'ara sawa mahaifiyar Lateef da sauran 'yan uwansa tsanar Hasseena a zuk'atansu gami da rashin haihuwar da bata yi, wanda har ta kai da abin ya fara damunta.
Duk inda Haseena ta ji mai maganin haihuwa sai ta nema ko dan ta wuce gori.
Duk sauran 'yan uwan Lateef da aka yi wa aure sun haihu amma ita shuru ba amo ba labari.
Sai da Haseena ta yi wata goma sha takwas tukunna ta samu ciki, har zuwa lokacin data haifi Yesmin.
An yi murna sosai da farin cikin samun k'aruwa, sai dai duk da hakan an gudu ne ba a tsira ba, domin kuwa wannan tambarin na rashin yin gara da ya zama kamar ibada yana goshinta suna kallonta da shi,duk irin son da Lateef yake nuna mata sai da shima ya fara nuna mata gazawarsu.
Haseena ta fuskanci k'alubale iri-iri daga wajen dangin miji har ma da shi kasa mijin, gori ba irin wanda bata sha har zuwa lokacin da Allah ya nufa aka yi mata gara, sabida k'orafin da take yawan kaiwa gidansu.
Kayan da suka kai ba laifi cikin rufin asiri komai ya yi, shinkafa buhu d'aya, sai Taliya katan guda, farin mai da ja galan guda-guda, maggi jaka biyar, da dubulan da alkaki bokiti me 100ltr d'ai-d'ai, sai turmin atampa da shadda yadi goma.
Duk da irin wannan kayan bai sa an daina musgunawa Haseena ba sai dai rage mata da ya yi, take samun fara'a kadan cikin 'yan uwan mijinta, a haka har Allah ubangiji ya sa ta kuma haihuwar Safwan......✍🏻*_YAWAN COMMENT YAWAN TYPING_*
🌹☞ℬıɠ ɠᗅ̨ι *¢ɛ✍🏻* *_2020_*
YOU ARE READING
ZUBAR HAWAYENA
Short StoryLittafi ne me k'unshe da sark'ak'iya kala-kala ta fannin rayuwa da kuma zamantakewar aure.