༺༻🌹༺༻
*🇿UℬAℛ*
*🇭AWAYE𝒩A*
֍
༺༻🌹༺༻
, . - . - , _ , " ;
) ' - . .> ' '(
/ 🌹🌹 '\
| 🌹 🌹🌹 |
\ 🌹 / /
'=(\ /.='
'-;'.-'
')| ,
|| _🍃. -'
,_|| \_,/*Տᴛ⌾ℛℽ & 𝒲ℛⅈᴛᴛℰℕ*
*ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩*©®-Aɴᴀ ᴛᴀʀᴇ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛
(wє ѧяє ṭһє ɞєśṭ ѧṃȏṅɢ ѧʟʟ wяıṭєяś)📚
https://m.facebook.com/Anatarewritersassocian/
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ*_Fadila αlῖϒῠ ϻῠsα (ϻϒ δῖlαlα)❤️ kϵ δῖͷ tα ϻῠsαϻϻαͷͼϵ gαrϵͷῖ._*
*ɑƒաɑղ ʍɑƘɑɾɑղԵɑ wαnnαn líttαfí вíѕα ѕhuru dα kukα jí hαkαn чα fαru nє вíѕα rαѕhín lαfíчαr dα nαчí, ínѕhα αllαh zαn cí gαвα.*
*🌹🇵ᴀɢᴇ ☞9➪10*
Idanuwansa suka yi arba da daddawa da kuka, guntun tsaki ya ja, gami da guntun ajjiyar zuciya, da sauri ya matsar da su gefe guda, dan tsananin takaici ko iya d'aure ledar bai yi ba.
Haka ya ci gaba da dube-dubensa kamar wanda ya yi wata ajjiya cikin kitchen d'in, can ya janyo wata kular abinci ya hau bud'ewa, indomie'n da Haseena ta ajjiyewa su Yesmin ce wadda ba su iya ci ba, ya k'ara jan guntun tsaki ya mayar ya rufe, takaici ne da damuwa ya cika masa zuciya babu abinda yake rayawa a ransa face ba ta da mutunci ko abincin ma bata yi masa ba, ji ya yi kamar ya koma d'akin ya same ta, sai wata zuciyar ta hana shi, ya d'auki kular abincin ya tafi da ita d'akinsa dan yunwa yake ji, gashi dare na yi ya san ba lallai ya samo abinda yake son ci ba.
Can kuwa Haseena na kwance kan gado banda kuka ba abinda take yi, ringing d'in wayarta da ta ji yo ya sata saurin d'agowa, tuni ta manta ma da abinda take yi da wayar sabida abinda Lateef ya yi mata sai a lokacin ta iya tunawa.
Ta yi banza da wayar kamar ba ta ji k'arar da take ba, haka wayar ta ci gaba da ruri har sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan ta kai hannu ta d'auki wayar, number da aka kiranta da rana ce, ba shiri ta d'aga wayar ta kai kunne, sallama ta fara yi kafin d'aya b'angaren ayi magana.
Shuru ta fara yi tana sauraron mai magana dan ba ta san me za a ce ba, duk da abinda Lateef ya yi mata haka ta danne zuciyarta tana sauraron mai magana, ya yin da aka ci gaba da yi mata magana "na ga kamar baki gane me yi miki magana a whtsapp d'in ba, kuma na miki reply amma shuru baki yi responding ba"
Abinda yake damunta shi kawai yake damunta a rai dan haka ba ta iya wata kwakkwarar magana ba face ba da hak'uri da kuma tambayar mai maganar.
Cikin mamaki ya runk'a yi mata magana "Ya salam, yanzu har kin manta me magana?, ya naji muryarki kamar akwai alamar damuwa ne?" Sake danne zuciyarta ta yi "babu komai, ba wai ina nufin ban gane ka bane, a'a kawai dai a whtsapp d'in ne nake ganin wata number daban" murmushi ya yi sosai har sai da ta ji yo alamar murmushin, ya ce "in ba damuwa mu koma online d'in mu k'arasa magana, kar fa ki ji tsoro ni ne ba wani ba da number nake whtsapp shi yasa za ki ga kamar ba ni ba".
"Toh" kawai ta iya cewa da shi, daga bisani kuma ta katse wayar ta hau online.
Mamaki ta yi irin yawan tulin sak'onnin da ya bar mata, da kuma irin bayanan da ta karanta wanda ya ke nuni da nuna damuwa da kuma kulawa gareta.
Dr. Haneef kenan mutumin da 'yan mata suke rubibi sabida tsananin kyansa, kwalliyarsa, dukiyarsa da kuma iliminsa da duk wani tsari wanda ake son a ga d'a namiji da shi Dr.Haneef duk ya had'a.
Dr.Haneef mutum ne da yake da d'inbin masoya a cikin makarantar, haka kuma ko a hanya mata suka ganshi sai sun ji sun yaba da irin tsarinsa, mutum ne me farin jinin mutane, hatta wasu mata masu aure ji suke tamkar ya zama miji a gare su, Dr.Haneef shi ne number d'aya a kaf! malaman da ke koyarwa na cikin makarantar da d'alibai ke so.
Sai dai duk wad'an nan abubuwa da ya had'a su, ba dai ka ganshi da wata mace da sunan soyayya ba, baya sauraron kowacce yarinya da ke cikin makarantar, muddin ka ganshi da mace to akwai abinda ya kawo ta wajensa na game da karatu kuma tana kammalawa an wuce wajen ba dai da sunan soyayya ba, dan ba ya kallon kowa da sunan hakan.
Dr.Haneef ba shida aure kuma duk kanin karatunsa ya yi shi ne a k'asar waje.
Duk da cewa akwai wata yarinya guda d'aya Mufeeda wadda ta mace a sonsa, kuma ba ta jin kunyar sanar masa da abinda take ji akansa cikin zuciyarta ko da kuwa a gaban mutane ne, duk da irin wulak'ancin da yake nuna mata na cewar baya sonta amma ita sam! hakan ba ya tab'a damunta dan bata damuwa, sai ya zamana ma tamkar k'ara zigata yake.
Gaba d'aya 'yan ajin su Haseena sun san komai game da son da Mufeeda ta ke wa Dr.Haneef da kuma irin k'in sauraronta da ya ke yi, wanda har wasu mazan ajin su kan tsokani Mufeeda kan tana wahalar da kanta akan wanda bai damu da sonta ba, amma ita ko a jikinta zuciyarta tuni ta yar kare ya d'auka, ko kuwa tsananin son da take masa ne yasa bata iya ganin kowa face shi? oho.
Mufeeda macece mai kyau ga ta fara da gashi bata rasa komai ba ga duk abinda ake buk'atar gani jikin 'ya mace Mufeeda duk ta had'a sai dai ita kanta tana yawan tambayar kanta mai ta rasa da shi ba ya sonta?.
Duk da irin son da Mufeeda takewa Dr.Haneef ita ma ba wai dan ta rasa masoya bane hasalima tana da wanda shi ma ya mace a sonta amma bata sauraronsa face Dr.Haneef, duk wani salon wulak'anci da Dr.Haneef yake nunawa Mufeeda itama ta iya ninkin baninkin d'insa tunda takan gwadawa wad'anda suke sonta fiye da wanda ake gwada mata, kuma akan Dr.Haneef ji take zata iya karawa da kowa. Hausawa na cewa 'son maso wani k'oshin wahala'
Da sauri Haseena ta katse tunanin da take akan Dr.Haneef, bayan da wani sak'on nasa ya kuma shigowa wayarta.
Jikin Haseena ne ya yi sanyi dan kalamansa suna nuni da kamar sonta ya ke, take ta fara zance da zuciyarta, shin bai san ni wacece ba?, ko kuwa me yake nufi da ni?, idan kuwa haka ne toh ta ya zan iya magance wannan matsalar da ta kunno kaina?, ko dai na yi blocking dinsa na hutawa kaina? kai idan na yi haka zan iya janyowa kaina babbar matsalar da ba zan iya maganaceta ba wajen karatuna, ko da yake ai ba furta min ya yi ba ni nake ganin hakan, ta runk'a fad'ar hakan a ranta.
Shuru ta yi tana karanta duk wani sak'o da yake turo mata, wani d'an emoji ta dubo mai alamar murmushi kawai ta dire, tare da rubuta cewa "idan babu damuwa ko za mu iya barin tattaunawar zuwa gobe in Allah ya kaimu? dan bacci nake ji sosai" ya amince da hakan ta kashe datar wayar.
Tuni ta ji ta manta da damuwar Lateef wannan tunanin ya zamar mata sabon al'amarin da ba zai iya barinta rintsawa ba, sai a lokacin ta kuma wani tunanin kan wanda yake kiranta a mota da cikin aji kenan ba kowa bane face Dr.Haneef? ta tambayi zuciyarta tunda kuwa number whtsapp d'insa ita ce number da aka rink'a kiranta da ita.
Dogon ajjiyar zuciya ta ja ya yin da ta d'ago kanta tana mamakin irin kalaman da Dr.Haneef ya rink'a furta mata, take ta yi ido hud'u da Lateef a tsaye bakin k'ofar d'akin yana kallonta.....✍🏻*_YAWAN COMMENT YAWAN TYPING_*
🌹☞ℬıɠ ɠᗅ̨ι *¢ɛ✍🏻* *_2021_*
YOU ARE READING
ZUBAR HAWAYENA
Cerita PendekLittafi ne me k'unshe da sark'ak'iya kala-kala ta fannin rayuwa da kuma zamantakewar aure.