Chapter 3-4

45 10 2
                                    

༺༻🌹༺༻
     *🇿​UℬAℛ*
  *🇭​AWAYE𝒩A*
              ֍
༺༻🌹༺༻        
     , . - . - , _ ,   "  ;
    ) ' - . .> ' '(
   /   🌹🌹    '\    
   |  🌹  🌹🌹  |
    \     🌹  /    /
        '=(\ /.='
          '-;'.-'
            ')|     ,
              || _🍃. -'
           ,_|| \_,/

*Տᴛ⌾ℛℽ & 𝒲ℛⅈᴛᴛℰℕ*
            *ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
         ❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩

*©®-Aɴᴀ ᴛᴀʀᴇ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛
(wє ѧяє ṭһє ɞєśṭ ѧṃȏṅɢ ѧʟʟ wяıṭєяś)📚
https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ

*INA BAWA MAKARANTA WANNAN LITTAFI HAQURI BISA SHURU NA RASHIN CI GABANSA DA AKA JI HAR NA TSAHON LOKACI, HAKAN YA FARU NE BISA WASU DALILAI KUMA IN SHA ALLAH A YANZU NE LITTAFIN ZAI D'ORA DAGA IN DA YA TSAYA, ZAI KUMA RUNQA ZUWA KO DA YAUSHE BA TARE DA YA TSAYA BA IN SHA ALLAH.*

_FATAN ALKHAIRI GARE KI *MY SAFNA ALIYU JAWABI❤️*._

TARE DA KU:
➪aтĸ
➪нaj. мaryaм ѕaĸaтarιya
➪мυнaммad ĸareeм
➪nazιғι yarιмa
➪тeeмaн dιмple

*🌹ℙᴀɢᴇ ☞3-4*

    Wata sanyayyiyar murya ce wadda ita kanta ba za ta iya tantance inda ta san muryar ba, shuru ta yi tana sauraro, yayin da shi kuma me maganar ya ke ci gaba da watso mata dad'ad'an kalamai masu ratsa zuciya.
   Mamaki ne ya runk'a kamata ji take tamkar ba ita ya yi niyyar kira ba kuskuren number ya yi, sai dai kuma sunanta da ya ambata kad'ai shi zai sa ta dad'a tabbatarwa da zuciyarta cewa ita d'in ya yi niyyar kira, dan haka ta yi gaggawar katse wayar.
       Tana cikin nazari da tunanin wanda ya kirata musamman irin kalaman da ya ke furta mata d'aya su ke da kalaman soyayya irin na saurayi da budurwa, wani guntun tsaki ta ja a dai-dai lokacin da kiran ya k'ara shigowa a karo na gaba, katsewa ta kuma yi ba tare da ta amsa kiran wayar ba, ci gaba da kira aka yi da sauri ta latsa wayar ta kai kunne cike da tsoro ta ce "sai dai har yanzu ban gane me maganar ba, anya kuwa ni ake nema?" Dariya ya yi daga can b'angaren "ki na mamakin hakan ne? , ki ma daina mamaki idan ma har ki na yi.
     Ina so mu runk'a gaisawa idan babu damuwa" shuru ta yi ta na mamakin abin da ya ke faruwa da ita, ba ta iya ba shi amsar komai ba ta kuma katse wayar, kashe wayar ta yi gaba d'aya ta yadda ko da ya kuma kira ba zai samu damar samun shigowar kiran ba.
    Har aka kaita in da za ta sauka cikin unguwar Mariri ba ta daina tunani kan wanda ya kirata ba.
      Tana sauka ta wuce gidan Hajjiya da niyyar d'auko su Yesmeen, ko da shigar ta sai ta ci karo da Haj.Lantana ta na wanke shinkafa, da sauri ta tsuguna ta gaida ita wata muguwar harara ta kai mata wadda ita kanta bata san dalilin faruwar hakan ba, ta amsa kad'an kamar ba ta son amsawa, sai dai kuma in da sabo Haseena ta saba ganin hakan lokaci-lokaci, jin kamar ba ta amsa ba ya sa Haseena k'ara gaida ita a karo na biyu, a fusace Haj.Lantana ta ce "sau nawa ki ke so na amsa 'yar malam da amsawa d'aya ba ta isa ba?" Jikin Haseena ne ya yi sanyi a hankali ta ce "Yi hak'uri Hajjiya ban ji bane" ta k'ara kai mata wata hararar a karo na biyu, kan Haseena a k'asa ta mik'e ta bar wajen.
     Haseena ba ta zame ko ina ba ta wuce d'akin Haj.Hindu kishiyar Haj.Lantana dan gaida ita, ta yi sa'a tana cikin d'akin dan haka ta shiga da sallama fuskarta cike da walwala, ita ma ta amsa ba tare da wata damuwa ko b'acin rai ba, har k'asa Haseena ta tsuguna ta gaida Haj.Hindu ta amsa mata cikin walwala, sannan Haseena ta tambayeta ko su Yesmin suna nan?, tana murmushi ta bata amsa da sun fita da su Zulaihat (K'annan mahaifin su) in sun dawo za su kai su, daga nan Haseena ta yi sallama ta bar d'akin dan duk jikinta a gajiye ya ke abinda tafi buk'ata a  yanzu bai wuce na ta ganta a gida ba.
        Tana k'ok'arin k'arasa fita ta jiyo Haj.Lantana ta koma d'aki dan haka sai ta koma zuwa d'akin na ta dan yi mata sallama ko da ta shiga ta yi mata sallama nan ma bata amsa yadda ya kamata ba, tun da kuwa a ciki ta amsa mata hakan ya k'ara saka Haseena cikin damuwa duk da ta san halinta.
                 𑁍𑁍𑁍𑁍𑁍
     Haseena na komawa gida kaya kawai ta cire ta shiga toilet dan watsa ruwa, bayan ta gama ne kuma ta d'auro alwalar la'asar ta yi sallah sannan ta fara k'ok'arin had'a abinci.
     Shigarta kitchen ke da wuya ta jiyo shigowar motar Lad'eef, gabanta ne ya yi mugun fad'uwa dan ba ta yi tsammanin dawowarsa a lokacin ba, da sauri ta d'ora ruwan taliya dan tasan ya na son Taliya, kuma tafi saurin dahuwa duk da ita ba wani cin ta take sosai ba.
     Ba ta yi aune ba ta jiyo shigowarsa, ta hanyar k'ofar kitchen d'in ya wuce fuskarsa babu alamar ko walwala, a ranta ta ce ko waya b'ata masa rai kuma? oho! kamar ya ji abinda ta fad'a har ya yi gaba sai kuma ya dawo da baya ya kalleta a fusace da sauri ta yi k'asa da idanuwanta ta na had'a kayan miya, jikinta a sanyaye ta ce "Sannu da zuwa fatan ka dawo lafiya?" Ko amsa mata bai yi ba kamar me niyyar cewa wani abu, sai kuma ya fasa furta abinda zai fad'a ya wuce, tana kallonsa ya shige zuwa d'akinsa tab'e baki kad'an ta yi ta ci gaba da aikin ta, kayan miya ta janyo wanda ta tanada gudun kada ta dawo ba ta da su, dan hakan ta ci gaba da aikinta.
      Ya na shiga d'aki ya hau kwala mata kira sam Haseena ba ta jiyo kiran da Lateef ya ke mata ba dan haka ba ta amsa ba, kanta a sunkuye tana had'o kayan miyan da ta ajjiye, sai ganinsa ta yi tsaye a gabanta yana wuci kamar wanda ya had'iyi wuta "Wato ke ba za ki sake halayyarki ba ko? kin d'auki girman kai kin d'orawa kanki, har wa ce ke, har me ki ke da shi da ki ke nuna ke wata ce?, toh ki sani duk wani take - taken iskancin da ki ke ji da shi ni na hauraki na zartaki wallahi raga miki kawai nake".
     Mamaki ne ya cikawa Haseena zuciya fuskarta cike da mamaki ta runk'a kallonsa ya na fad'a mata maganganu masu zafi da d'aci, ran Haseena ya yi matuk'ar b'aci amma duk da haka ta danne zuciyarta ta saukar da murya k'asa ta ce "yanzu me kuma na yi Lateef, me ka ke so ka ce? kullum kai ba ka son zaman lafiya, yanzu dan Allah me ne laifina kuma wanne girman kai na ke nunawa?, na tafi makaranta ban samu na dawo ba sai yanzu ko abinci ban ci ba tun safe, k'ok'arina na had'a muku abinda za ku ci amma hakan bai yi maka ba?" wani mugun zagi ya yi mata wanda ita kanta ba ta tab'a tsammanin zai iya aikata hakan gareta ba, ba shiri ta ce "Haba Lateef ban cancanci hakan daga gareka ba, ka sani duk wani zagi da za kai mun ni nasan mutuncin iyaye na, kuma na san darajar aure ba zan tab'a ramawa ko kuma na ce zan fad'a maka maganar da za ka ji zafinta irin wadda ka ke fad'a mun ba" ransa ne ya k'ara b'aci dan shi ba ya son yana magana ta na yi ko kuma in ya yi ta ce za ta mayar masa, a wajensa wannan raini ne babba matsayinsa na mijinta dan haka ya k'ara fusata cikin zafi ya runk'a jefa mata muggan kalamai "Ashe ba ki da mutunci, baki san mutunci ba?, har yanzu ke dak'ik'iya ce tun da baki san menene darajar miji ba sai dai ki fad'e shi a baki, banza mara hankali" Daga nan ya fice zuwa falo ya barta tsaye cikin kitchen zuciyarta na tafasa.
      Tun lokacin da ya ke maganary tsayawa ta yi ta na kallonsa ta kasa ce masa komai sabida tsananin takaicin da ya tsaya mata a zuciya, na yau har ita Lateef ya ke zagi kamar wadda aka bawa sadakarta, wasu kwalla masu zafi da rad'ad'i ne su ka fara kwaranyowa kan kuncinta.
     Kuka ta runk'a yi dan ta rasa me ya sa ya ke mata hakan, tunane-tunane ne su ka yi ta zuwar mata cewar me ya sa ya ke mata haka, ko dai ba ta da abinda d'a namiji ya ke so ne tare da ita? idan har babu me ya sa maza da yawa su ke tsaida ita a duk lokacin da ta fita, har su ke tunanin ma ba mai aure ba ce, duk da irin manyan hijaban da ta ke sakawa?, toh ma ai abin dubawar tun asali ba haka ya ke mata ba yanzu ne ya ke fito da wad'annan abubuwa na rashin kyautawa, ko dai wani abu ne ya faru wanda ita kanta ba ta san da shi ba?, haka zuciyarta ta yi ta raya mata.
       Sabon kuka ne ya k'ara zuwar mata dai-dai lokacin da Lateef ya fito ya na shirin fita kallonta ya yi a cikin kitchen ta na gurshek'an kuka tamkar wata k'aramar yarinya bai ji tausayin ganinta a hakan ba sai ma cewa da ya yi "Ki na nufin baki gama girki ba? Kafin na dawo ki tabbatar kin ajjiyen abinci na dak'ik'iya kawai" ya shige ya fita, kallon mara tausayi ta runk'a yi masa yayin da ta k'ara fashewa da sabon kuka.
      Da kyar ta iya dakatar da kukan da take, wata zuciyar ta ce kar ta ci gaba da aikin wata zuciyar kuma ta ce mata ta yi hak'uri ta k'arasa aikin da ta ke wata rana sai labari, fasa d'ora girkin ta yi, ta rage ruwan ta maida shi ruwan indomie dai-dai cikinsu ita da yaranta.
      Ranta a b'ace ta had'a girkinta ta zuba kifi ta yi jajjagen kayan miya duk ta zuba da kayan k'amshi yana dawuwa ta juye a flast ta zuba na ta a plate ta ci ta ajjiyewa su Yesmin sauran.
       Komawa d'aki ta yi ba tare da ta  zauna a falo ba, ta d'auko wayarta daga cikin jakarta dan ta manta a kashe wayar ta ke sai a lokacin ma ta tuna, dan haka ta d'auko ta kunna.
      Ta na kunna wayar sak'o ya shigo ta yi saurin dubawa, number ce wadda aka kirata a hanya, dan haka gabanta ya yi mugun fad'uwa musamman ganin irin kalaman da akai amfani da su a cikin sak'on.
      Shuru ta yi zuciyarta na ta sak'e-sak'e iri-iri na ko dai ta saurari me wannan sak'on? sai wata zuciyar ta hanata.
      Tana cikin wannan tunani ta ga an kira wayar sai dai yanzun ma wata number ce daban ba irin wadda aka kirata ba, a zuciyarta ta ce toh yau kuma bak'in lambobi ne su ke kira na?, ko waye kuma oho! da sauri ta danna wayar ta kai kunne dan har ta kusa tsinkewa sallama ta fara yi ya yin da aka amsa sallamar daga can d'aya b'agaren, a hankali ta ce "sai dai ban gane me magana ba dan Allah wa ke magana?
      Murmushi ta ji ya yi "kwantar da hankalinki idan har ki ka tsaya ki ka saurare ni zan miki bayani ni ba cutar da ke na kira na yi ba, akwai mahimmin dalilin da ya sa na kiraki sai dai na ga kamar da k'yar ki ka d'aga wayar, ko ki na tsoro ne?" Gyad'a kai ta yi da sauri tamakar ya na ganinta ta ce "a'a ba haka bane, ina sauraronka" guntun ajjiyar zuciya ya ja kafin ya ci gaba da magana "ya kamata ki saki jikinki na san ba ki gane ko waye ba, da farko dai sunana Dr.Haneef"
     Sosai ta fidda idanuwanta dan ta razana da jin sunansa, gabanta ne ya yanke ya fad'i ras! dan ba ta tab'a tsammanin ganin kiransa ba.
     Nan ta ke ta fara tunanin ta yadda aka yi har ya sami number ta, a ina ya samu? Haka ta ci gaba da tambayar zuciyarta tambayar da ita kanta ba ta da amsarta, ta yi shuru ta na tunani  ta kasa cewa komai, jin shurun da ta yi ya sa ya k'ara magana "kina mamaki ne, ko  dai ba Haseena Aliyu na kira ba?" a sanyaye ta ce "ni ce, ina fatan ba wani abu ne ya faru ba, ko akwai wata matsala ne?" murmushi ya yi kafin ya ce "Idan kin ba ni damar yi miki bayanin koma mene zan miki ta whtsapp".
        Shuru ta yi na d'an dak'ik'u gabanta ban da fad'uwa babu abin da ya ke a hankali ta ce "Shikkenan na amince" ya ce "amma kamar wanne time zan iya samun ki a whtsapp d'in, kuma da wanne number ki ke yi?" a sanyaye ta kuma magana "a kowanne  time za ka iya samuna muddin dare ne, kamar after 8pm zuwa sama, ina yi da wannan number da ka kira" daga nan su ka yi sallama da alk'awarin za su had'u domin ya fad'a mata abin da ya ke faruwa.
     Har yanzu zuciyar Haseena ta kasa nutsuwa sabida tunani, ba ta san ta yadda akai har Dr.Haneef ya samu number ta ba,  nan dai zuciyarta ta shiga zulumi da wasi-wasi gami da tunanin abinda zai je ya zo ta kasa fahimtar komai, wa ya ba shi number ta? abinda zuciyarta ta runk'a raya mata kenan.

*_YAWAN COMMENT YAWAN TYPING_*





🌹☞ℬıɠ ɠᗅ̨ι *¢ɛ✍🏻* *_2021_*

ZUBAR HAWAYENAWhere stories live. Discover now