Chapter 5-6

30 7 0
                                    

༺༻🌹༺༻
     *🇿​UℬAℛ*
  *🇭​AWAYE𝒩A*
              ֍
༺༻🌹༺༻        
     , . - . - , _ ,   "  ;
    ) ' - . .> ' '(
   /   🌹🌹    '\    
   |  🌹  🌹🌹  |
    \     🌹  /    /
        '=(\ /.='
          '-;'.-'
            ')|     ,
              || _🍃. -'
           ,_|| \_,/

*Տᴛ⌾ℛℽ & 𝒲ℛⅈᴛᴛℰℕ*
            *ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
         ❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩

*©®-Aɴᴀ ᴛᴀʀᴇ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛
(wє ѧяє ṭһє ɞєśṭ ѧṃȏṅɢ ѧʟʟ wяıṭєяś)📚
https://m.facebook.com/Anatarewritersassocian/
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ

*_Fadila αlῖϒῠ ϻῠsα (ϻϒ δῖlαlα)❤️ kϵ δῖͷ tα ϻῠsαϻϻαͷͼϵ α gαrϵͷῖ._*

_Hαjjῖϒα ϻαrϒαϻ sαkαtαrῖϒα ϻαtsϴ ͷαͷ δαb δα ͷῖ, dan ͷα sαͷ kῖͷα tαrϵ δα ͷῖ α kϴδα ϒαῠshϵ._

*🌹ℙᴀɢᴇ ☞5-6*

    Har magriba ta yi shuru ba a kawo su Yesmin ba, ta gyara guraren da ta san ba a gyare su ke ba, sannan ta d'auro alwalar magriba ta yi sallah a falo, tana idarwa ta shiga d'aki ta cire doguwar rigar da ke jikinta tun yamma, ta d'ebo wasu kayan daban marasa nauyi riga da wando ta saka, kalar shigar sun yi mata kyau sosai, lemon green ce rigar sai kuma bak'in wando da bak'in d'an kwali da ta d'aura, rigar ta d'an kama jikinta kad'an.
     Tana gama kimtsawa ta haye gado ta kwanta ya yin da wayarta ke hannunta, duk ta k'agu lokacin hawa whtsapp ya yi, kuma  ta k'agu da dawowar su Yesmin sabida ta samu su yi bacci da wuri, dan ba ta son  ta zauna daga baya kuma ta tashi, tafi son ta kammala komai kafin lokaci ya cika.
    Tana cikin tunane-tunane na abubuwan da ke faruwa da ita ta ji yo isowar su Zulaihat da sauri ta mik'e ta fita dan bud'e musu k'ofa.
     Ko da ta bud'e gaisawa kawai su ka yi da su Zulaihat ba tare da sun shigo cikin gidan ba, tun daga bakin k'ofa su ka mik'a wa Haseena Safwan da Yessmin sannan su ka juya, ba yadda ba ta yi su shiga ba amma su ka k'i sabida dare ya yi, ta kama hannun Yesmin, Safwan kuma ta ruk'e shi dan har ya fara bacci.
     Sai da ta rufe k'ofar sannan su ka wuce zuwa falo tun kan su k'ara falo Yesmin ta fara magana "Mummy muka je gidan Aunty Hafsat (K'anwar mahaifin su Yesmin)" Haseena na murmushi ta ce "Tun yaushe ku ka je?" su na tafe su na hira har su ka isa falo inda Yesmin ta ke ci gaba da magana "tun safe muka tafi bayan da Abbah ya kaimu, Uncle Ahmad da su Aunty Zulaihat su ka ce a tafi da mu tun da gidan ba kowa sai su Hajjiya".
   Ba wani saurarenta Haseena ta ke sosai ba, abubuwan da su ke damunta a zuciya su kad'ai su ke yi mata kaikawo a cikin zuciyar, wanda kuma a zahiri sai ka rantse da Allah tana fahimtar abinda Yesmin ta ke fad'a.
    Guntun ajjiyar zuciya Haseena ta ja sa'ilin da ta ke tashin Safwan daga baccin da ya fara. "Tashi ka ci abinci bari na kawo muku, Yesmin je ki cire kayan ki, ki zo ku ci abinci.
     Yesmin ce ta ce "Mummy mun ci abinci a gidan Aunty Hafsa" kad'a kai Haseena ta yi tare da saukar da murya k'asa "amma dai ai za ku k'ara ko? ba na son ku kwana da yunwa, in kun san za ku ci ki fad'a na zubo muku" a shagwab'ance Yesmin ta ce "Ni dai bacci na ke ji na k'oshi" Safwan kuwa a hankali ya ce "Ni dai zan ci" Haseena ta ce "yauwa yaron kirki bari na zuba maka ka ci ka kyale ta" kamar Yesmin za ta yi kuka ta ce "Ni Mummy ba yarinyar kirki ba ce?" Haseena ta yi dariya kad'an "kema yarinyar kirki ce ki je ki cire kayanki kin ji yarinyar arzik'i" daga nan Yesmin ta yi dariya ta shiga d'aki a guje dan canja kayanta.
      Kad'an Haseena ta zubowa Safwan abinci dan ta san da wuya ya iya ci tun da kuwa Yesmin ta ce sun ci.
     Cikin minti talatin ta gama shirya su ta sa kowannensu ya yi sallar ishaa ya kwanta, sannan ita ma ta yi sallar ta hau gado ta kishingid'a ta na jiran cikar lokaci.
    Har zuwa lokacin Lateef bai dawo ba wanda in da sabo shi ma hakan ta saba gani daga gare shi dan haka ma sam! ba ta damu da rashin dawowar sa ba.
     Takwas da minti goma ta kunna datar ta nan sak'onni suka runk'a dropping rututu tamkar saukar ruwan sama, tsayawa ta yi cak! ta na jiran su gama shigowa ta duba wanda ta hau dominsa.
     Gama shigowar su ke da wuya ta ga wata number d'auke da sak'o an bar mata danna kan number ta yi dan duba sak'on da ke ciki ta na k'ok'arin bud'ewa kenan ta ji yo ana buga gidan ranta a b'ace ta k'ara gyara kwanciyarta, dan ba ta san tashi, a zuciyarta ta san ba zai wuce Lateef ba, dan haka ta yi buris kamar ba ta ji bugun da ake ba, ta ci gaba da abinda ta ke.
     Bud'e message d'in ta yi nan ta ga an rubuta "Ar u online?" da sauri ta rubuta "Yes", wani bugu me k'arfi ta ji yo ana yi wanda hakan ya tsayar mata da tunaninta gaba d'aya, dan ya razanar da ita sosai har sai da hantar cikinta ta kad'a.
     A firgita ta ajjiye wayar cikin tsoro ta mik'e ta na k'ok'arin fita dan tambayar wanda ya ke bugawa, sau biyu ta na tambayar ko waye? amma shuru ba tare da an ba ta amsar tambayar da ta ke ba, ganin ba a amsa ba ya sa ta fara tunanin ko ba gidan ake bugawa ba, a sanyaye ta koma cikin d'aki ta haye gado ta kwanta ta ja wayar ta in da ta kuma bud'e number da ake mata magana ta rubuta "Sai dai ban gane number ba" tun kan ayi mata reply ta k'ara ji yo wani mahaukacin bugun wanda saura kad'an ta rafka zagi tana fad'in "wai waye ya ke wannan bugun ne?" Da k'arfi take maganar.
     Kasancewar ta na daga can cikin d'aki ya sa ko da mutum a tsakiyar gidan ya ke ba zai ji yo maganar da ta ke ba, ta na k'ok'arin fitowa ana ci gaba da bugawa abinda ya ke k'ara ba ta mamaki idan har wani na ta ne ai zai kirata a waya, haka kuma idan Lateef ne shi ma ai zai kirata a waya kamar yadda ya saba idan ya kai dare, sai dai babu kiran da ya shigo wayar ta, shiyasa ma firgici da tsoro su ka fara ziyartar zuciyarta.
    Ta ya ma zai wannan mugun bugun kamar me shirin b'alla k'ofar? ta fad'a a zuciyar ta bayan ta iso dab da wajen k'ofar duk da cewa ba ta k'arasa bakin k'ofar ba.
     Sai da ta kuma tambayar ko waye? nan ma ba a bata amsa ba dan haka ta k'ara firgita sosai, me ya ke shirin faruwa da ita? zuciyarta ta fara yi mata sak'e-sak'e iri-iri, babu wani abu na mafita da ya zo mata cikin zuciya sai tunanin Yesmin da Safwan da ya ke zuwar mata, cikin sauri ta ke katse muggan tunanin da ke zuwar mata, wani abun da ya k'ara zuwar mata cikin ranta shi ne ta ya ake yin shuru da bugawar da zarar ta fito? ya yin kuma da ta koma sai a ci gaba da bugun kamar ana kallonta, nan ta fara dube-dube ko za ta ga ta inda ake kallonta, amma sam! ba ta gani ba take tsoro ya k'ara zuwar mata cikin zuciya, da sauri ta koma falo, dan tsoro ba ta iya tsayawa a falo ba ta  wuce can cikin d'aki daman su Safwan ma na ciki, zaman ta ke da wuya ta kuma ji yo wani sabon bugun, a gigice ta mik'e tsaye, gabanta na fad'uwa ya yin da ta ke ji yo wani sauti daban wanda ba ta iya tantance abin da ake fad'a, kuma ba ta gane sautin muryar da ke maganar.

*_YAWAN COMMENT YAWAN TYPING_*





🌹☞ℬıɠ ɠᗅ̨ι *¢ɛ✍🏻* *_2021_*

ZUBAR HAWAYENAWhere stories live. Discover now