༺༻🌹༺༻
*🇿UℬAℛ*
*🇭AWAYE𝒩A*
֍
༺༻🌹༺༻
, . - . - , _ , " ;
) ' - . .> ' '(
/ 🌹🌹 '\
| 🌹 🌹🌹 |
\ 🌹 / /
'=(\ /.='
'-;'.-'
')| ,
|| _🍃. -'
,_|| \_,/*Տᴛ⌾ℛℽ & 𝒲ℛⅈᴛᴛℰℕ*
*ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩*©®-Aɴᴀ ᴛᴀʀᴇ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛➛
(wє ѧяє ṭһє ɞєśṭ ѧṃȏṅɢ ѧʟʟ wяıṭєяś)📚
https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ*_Fadila αlῖϒῠ ϻῠsα (ϻϒ δῖlαlα)❤️ kϵ δῖͷ tα ϻῠsαϻϻαͷͼϵ gαrϵͷῖ._*
*🌹🇵ᴀɢᴇ ☞7➪8*
Cikin tsoro da fargaba ta fito waje tana sand'a kamar wadda za a kama, duk da irin tsoron da ta ke ji haka ta danne zuciyarta ta k'arasa har bakin k'ofa, ta yi shuru ba tare da ta ce komai ba, jira ta ke ta ji an yi magana amma shuru ba a yi ba.
Wani irin bugu aka sake yi wa k'ofar wanda har sai da ta razana k'afafunta suka matsa daga dai-dai inda ta ke tsaye dan tsananin tsoro da firgici, ji ta yi kamar ta taka a guje ta koma d'aki ko kuma ta rusa ihu jama'a su kawo d'auki.
Amma ina! hakan ba zayyuba dan ko da ace ta yi ihun babu wanda zai iya jiyo muryarta bare ya kaho mata d'auki tunda kuwa katangarsu tana da tsayi sosai.
Da k'arfi cikin isa da tak'ama ta ji an yi magana "Wai ba za ki bud'e k'ofar ba, wanne irin iskanci ki ke ji da shi yau ne?, muddin na shigo za ki gane ko waye ni".
Fidda idanuwanta ta yi waje sosai ya yin da gabanta ya ci gaba da bugawa da sauri-sauri, ta bud'e k'ofar tana bud'ewa ta hau fad'a "Haba Lateef wai mene haka? Sai ka ce wanda bai san me yake ba, ko da ace gidanka ne irin wannan bugun sam! bai kamata ba, bai ydace ba. ko ka manta da cewa tsoro yana iya haifar da komai? kuma in za kai bugun ma ba zakai na hankali ba sai ..." Kafin ta k'arasa maganar da take shirin furtawa Lateef ya sharara mata mari, sai ji kake wani kauu! a kuncinta da sauri ta dafe kuncin da hannunta na dama take hawaye suka fara biyo fuskarta idanuwanta suka yi jahur kamar gauta.
Tana magana muryarta na rawa "ni ka mara Lateef sabida na fad'a maka gaskiya?" A fusace ya ce "An mara d'in ko za ki rama ne?, kuma ina mai sanar miki daga yau sai yau kar ki k'ara kuskuren d'aga mun murya banza mara mutunci wadda bata koyi tarbiyya ba" Yana gama fad'ar hakan ya wuce zuwa d'akinsa.
A tsaye ya bar Haseena ba tare data motsa daga inda take ba, hannunta dafe kan kuncin da Lateef ya sharara wa mari, banda hawayen da ke fitowa daga idanuwanta babu abinda ke sauka kan kuncinta, zuciyarta na zafi da rad'ad'i ta runk'a jan numfashi kad'an-kad'an, ta juma a hakan har na tsawon wasu dak'ik'u daga bisani kuma ta koma d'aki ta kifa kanta kan gado ta hau gurshek'an kuka, tamkar wata k'aramar yarinya.
Shi kuwa Lateef ko da ya shiga d'aki kayansa kawai ya cire ya canja, bai fi minti biyar da
Shiga d'akin ba ya hau kwalawa Haseena kira,shuru ya ji ta yi ba tare da ta amsa ba dan haka ya tashi da kansa ya na dube-duben abincin da zai ci.
Kai tsaye Kitchen ya nufa inda ya runk'a bud'e kwano-kwano na cikin kitchen d'in amma bai ci karo da abinda ya ke son gani ba.
Yana cikin dubawa ya hango wani d'aurin bak'ar leda wanda ni kaina marubuciyar ban san menene cikinsa ba, da sauri ya kai hannu ya janyo ledar fuskarsa cike da mamaki, ya fara k'ok'arin bud'ewa dan ganin abinda ke ciki, ko da ya gama kwance ledar sai ya bud'e ta sosai, gama bud'ewarsa ke da wuya idanuwansa suka yi arba da ........✍🏻*_YAWAN COMMENT YAWAN TYPING_*
🌹☞ℬıɠ ɠᗅ̨ι *¢ɛ✍🏻* *_2021_*

YOU ARE READING
ZUBAR HAWAYENA
Cerita PendekLittafi ne me k'unshe da sark'ak'iya kala-kala ta fannin rayuwa da kuma zamantakewar aure.