Chapter 7 & 8

27 4 0
                                    

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
      💍     💍      💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

         💍     💍     💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_
  
_ZAINAB HABIB_
   _{Mom islam}_

*zai koma na kud'i tunda kuna karantawa amma bakwa sharhi*

*karku manta wlh zan dena post a Watsapp zan koma wattpad yafimin* 👌👌

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

🅿️EPISODE 7 & 8

   Fad'in haka yasa Salma shiru da bakinta , tana gama shan ruwan ta mik'e tace ”sis mukam zamu wuce ,ga wanan kya rage wani abu, no bana so , Afnan tace ”lokacin da ta kamo hanun Sudais tana shirin yin hnyar waje , tsaki Salma taja kana tace ”wlh tunda kikace auran talaka ,hmm ina tausaya miki ko dady , yanzu baya ambaton sunanki , Afnan ce tayi dariyar yak'e wace tafi kuka ciwo ,tace ”ina da Allah tunda kowa na gudu na please in wucewa zakiyi ki fice, karki k'aramin ciwon kai , okay don't worry , nice ma nazo inda kike ,tunda ke ba neman mu kikeyi ba ,wani wawan mari ,Afnan ta wanka wa Salma , Kana tace ”ficemin a gida ,bana neman temakon ku bance kowa ya temaka min ba , rik'e da kumatu , Salma ta fizge hanun Sudais a na Afnan suka wuce a zuciye , komawa kan kujera Afnan tayi ,rik'e da kanta , cikin damuwa da 6acin rai ta sa kuka mai tsuma zuciya , innalilahi wa inna'ilaihir raji'un ta ambata cikin muryar kuka , ya Allah kayimin magananin matsala ta , tun farkon aure na banida kwanciyar hankali , oh Allah ka duba lamurana, ta kwanta tana kuka ,Fatima ce ta shigo ,hanunta rik'e da wani abu a gora kamar zuma , da sallama ta shiga gidan Afnan tace ”matar Haisam na kawo miki wani sirri na musamman , da jajanyen idanunta Afnan ta dubi  Salma, tace ”wa'alaikumus salam , tsoro ne ya kama  Fatima  tace ”yau kuma maiya faru ?"Afnan ce tace ”dan Allah ki tayani da adu'a Fatima ,insha Allah barinje gida cewar Fatima , Afnan ce tace ”mai kika kawo , a'a kibari zuwa gobe mayi magana ,to Afnan tace Fatima ta wuce gida."

   Dare nayi ta yi abubuwan da tasaba , shigowar Haisam  misalin k'arfe 8pm yau ya dawo da wuri , jiki a sanyaye ta mik'e tayi masa oyoyo , ganin yau babu fara'a dakuma barkwancin da tasaba yi masa yasa shi ,k'are mata kallo ,rungumo ta yayi yana murza hanunta da ya rik'e gam , rurin da wayar sa keyi ne yasa shi sakinta , d'aga wayar yayi tare da sallama , jin muryar mama yasa shi k'ara matsawa nesa da Afnan dan yasan labarin gizo baya wuce na k'ok'i , jiyo muryar mama yayi tana cewa ,wlh inhar baka zo yanzu ba to wlh sai nayi mumunan 6ata maka rai , juyawa yayi yaga Afnan bata gurin ,ya rage muryarsa yace ”mama ganinan zuwa, karma kazo wlh zaka gane ta kashe wayar , k'ara sawa bedroom d'in Afnan yayi ,gajinta a zaune tana gyara powder fuskarta yasa shi , sakin fara'a yace ”my lovely barinje in dawo mekikeso ,in taho miki dashi¿" dariya tasa wace kamar ta dole ce tace ”dabino da kwakwa , to karki damu , cikin rawar jiki ya fice, ƙofar gida ya fita ya tada mashin ɗinsa ,kai tsaye gidansu ya nufa ,sallama yayi kana ya shige ɗakin mamanshi ,samunta yayi a zaune tana jijiga ƙafa, yana shiga ta miƙe ,cike da ɓacin rai tace "wato Haisam ban isa in gaya maka magana ba?" yanzu ƙarfe nawa? duba agogo ka gani ,Haisam ne ya kalli agogon hanunsa yace "ƙarfe goma ,to mekake nufi da maganar da muka yi dakai?" Haisam ne yace "kiyi haƙuri mama zanbi umarninki amma kibari zanyi shawara, shawarar banza cewar mama ,to wlh tun wuri kabi umarni na kokuwa na tsi.... innalilahi ya ALLAH mama ki gafarceni karkiyimin baki ,na yarda  zanyi auran ,ywwa Allah yai maka albarka , nariga na gama magana hira zaka fara zuwa , kuma daga yau , a kid'ime ta kalli mama da keta washe hak'ora , dubu d'aya ya mik'a mata kana yasa Kai zai fice , dakatar dashi mama tayi , tace ”to yanzu bari a kirata a waya inyaso sai kaje ko?" shiru yayi bai ce komai ba , mama ce ta ciro wayarta a lalita ta mik'awa ,Haisam kana tace ”lalubo min lambar , Maimuna ,yana dubawa yaga number danna kira yayi ya mik'awa mama, hararar shi mama tayi tace ”nice mai zuwa zancen?" zaka fara nunamin halin naka ko?"cikin ladabi ya k'ar6i wayar , sallama tayi ,jiyayi ance "baby takake yakuma gajiyar aiki ?" muryar Haisam babu alamun fara'a yace ”zankira ki gobe , okay I love you , yana kashe wayar ya mik'awa mama."

LAMARIN K'ADDARAR AURE NAWhere stories live. Discover now