Chapter 15 & 16

25 3 0
                                    

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
      💍     💍      💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

         💍     💍     💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_
  
_ZAINAB HABIB_
   _{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 15 & 16

     Haka dai suka dinga hirarsu Anty ce ta shigo ta samesu a palo cewa tayi" aa saukar yaushe ?"Salma ce tace"Anty ban jima ba , gaisawa sukayi hira ta ɓarke tsakaninsu , wanda duk rabin hurar ta Anty Afnan ce , hakan ya sata ƙin kulasu dan inda abinda ta tsana bai wuce hirar Haisam ba ,sai yamma Salma ta fara shirin tafiya , momy ta bata turaruka da su zuma , kirane ya shigo wayarta , ganin number mijin yasata cewa "to drivern mu ya ƙaraso ,bata samu haɗuwa da dady ba hakan yasata tafiya tace "a gaishe shi, momy ce ta ƙwalawa Afnan  kira kasancewar ta koma ɗakinta , amsawa tayi ta fito , momy ce tace "zo kiyi wanka kiyi kwaliya dan Allah ji tsara kwaliyar  maiya faru momy ?" sai kin tambayeni ko kina ganin zan cutar dake ne ? a'a Afnan tace " ta shige toilet  tafara wanka da sabulun da momy ta bata mai ƙamshi , tana fitowa ta tarar da momy a ɗakinta da kaya a hannu  tana gama kwaliya tace "momy wanan kayan zan sa?"cikin fara'a momy tace "eh man ƴar albarka  karɓa Afnan tayi tasa momy ta miƙo mata sarƙa da ɗankunne da war waro , kana ta miƙa mata turare mai ƙamshi , feshe ko ina na jikinta tayi ta juyo tace "momy nayi kyau?".

   "Sosai ma my daughter  kinyi kyau  , yanzu kinsan abinda nakeso dake? a'a Afnan tace "to baƙo zakiyi daga Kano zai zo nan Abuja so ina san ki tarbeshi da mutunci yaron abokin dadynku ne  insha Allah Afnan tace "in ya iso zai kiraki a waya oky momy , jekisa a gyara ɗakin saukar baƙi , ficewa Afnan tayi dan isarda saƙon momy ,turare mai ƙamshi aka sanya a ɗakin , ƙarar wayar Afnan ce ta dawo da ita daga duniyar tunani sbda tana tunanin to shi waye kuma mezai kawoshi , inko soyayya ce hmm , amsa kiran tayi tare da sallama a bakinta , wa/alaikis salam barka taji ance daga ɗayan ɓangaren gimbiyar mata kuma sarauniya , gani gurin parking ɗin mota oky Afnan tace "tana shirin miƙewa , da fitarta ta hango wani kya kyawan saurayi lol to koma dai bazawari ne ,nidai ya yimin kama da saurayi , yana hangota ya haɗiyi wani miyau tare da magana a zuciyarsa , shin wanan bazawara ce ?"anya nifa naga kamar budurwa , ga tsayi ga kyau komai na jikinta mai ɗaukar hankali kai masha Allah ,kona aureta bazan haɗata da matata ba 🤭wai dama yanada mata ?"fans kuzo muji , sallamar da Afnan tayi ne yasashi daɗa ƙare mata kallo ,yana amsa sallamar yace "gimbiya sarautar mata kuma mata a gurin  Abdallah , waro ido Afnan tayi tace "wanan kirari haka ?.

    To zomu shiga gida ƙin jerawa yayi da ita tana gaba yana baya ,yana kallon yanayin takunta , jinjinawa yakeyi a zuciyarsa inhar yasami Afnan to yasami farinciki gashi ya riƙe sunanta gam ,  suna shiga ya zauna a ƙayataciyar kujerar da ta ƙarawa ɗakin kyau , nesa dashi Afnan ta zauna tunani ne ya faɗo mata ashefa tanada aure zata tsaya hira innalilahi to yanzu yazanyi ?"momy fa na sane wlh , Abdallah ne yace "gimbiya bamu gaisa ba lokacinne ta ƙare masa kallo ba wani yaro bane dan zai kai shekara talatin da biyar ko fima amma kasancewar nera ta zauna sai ta ɓoye shekarun nasa , murmishi tayi tace "ina yini lpy dafatan nasami mazauni a zuciyarki , tsintar kanta tayi da cewa insha Allah, ganin abin takeyi kamar almara wai itace a gaban wani harda tsara kwaliya ba mijinta ba kai ina!!, Abdallah ya lura hankalinta baya gurinshi dan tun ɗazu yake magana batasan yana yiba amma hakan bai ɓata masa rai ba ,sbda tunda ya ganta yaji zuciyarsa ta amince da auren ta kuma dukiya ko nawa take buƙata zai kashe dan yaga ya sameta."

   To Afnan barin shiga mu gaisa da dady yacemin yana hanya ɗazu da alama yama ƙaraso , to kawai Afnan tace "ta miƙe jiki babu ƙwari tayi bedroom ɗin momy , momy na ganinta ta faɗaɗa fara'arta tana cewa my daughter ya kukayi , zama gefen gadon momy Afnan tayi tace "mun gaisa yace "bari yaje gurin dady su gaisa , oh amma babu wata matsala ko ?"eh Afnan tace " momy kinsan fa da aure na nake kula wani , haɗe rai momy tayi tace "to ai Haisam ya sakeki yau kwana biyar kenan gama takardar , cikin ƙaguwa da ganin takardar , sbda gani takeyi momy kamar wasa take yimata ,  miƙa mata takardar momy tayi , Afnan ce ta nutsu ta fara karantawa .

ASLAMU ALAIKUM
NI HAISAM NA SAKI AFNAN SAKI BIYU,
   
  Maimai tawa tadin gayi a zuciyar ta ya sakeni ?" Haisam ya iya sakina ? kalonta momy tayi tace "Afnan inason ki kwantar da hankalinki yanzu kina fita idda zaki yi auranki , namiji ba ɗan goyo bane ,yakamata kisani daga lokacin da yayi sabon aure shikenan kin zamo abin wula ƙantawa ,yanzu kinga aya a auranki da Haisam ko , fashewa da kuka Afnan tayi tana juya takardar tana kuka , yayi kyau zan cireka a zuciyata in huta tunda ba sona kakeyi ba , taɓe baki momy tayi tace" "dama menene abin so a gurin talaka kina soyayya ai , no momy inason sa maiyasa yayimin haka ?" shigowar dady ne yasata tsagaita maganar tare da kukan , kallon fuskar Afnan yayi cikin tuhuma yace "mai yasami Afnan nakejin maganarta tun daga ƙofar ɗaki , momy ce tace "wai dan na miƙa mata takardar sakin da Haisam yayi mata shine take kuka , samun kujera dady yayi a can gefe ya zauna , yace "wato Afnan har yanzu bakisan talaka ba ko ?" idan zaki yarda da zaɓi na na zaɓa miki Abdallah a matsayin miji , ɗago kai Afnan tayi saboda tariga ta yanke shawarar bin umarnin iyayenta , tunda Haisam yayi mata haka bazata ƙara yimusu gardama ba."

   Momy ce ta karɓe da amma yanada mata ɗago kai Afnan takuma yi a karo na biyu mata kuma!!eh cewar dady hakan bazai sa Abdallah ya wukaƙan taki ba , momy ce tace " karki watsa mana ƙasa a ido daughter,to Afnan tace "na karɓi zaɓinku momy insha Allah bazakuyi kuka dani ba , cikin farin ciki dady ya miƙe yana cewa"Allah yayi miki albarka yanzu mai kike buƙata wanda bakida shi ?babu komai dady ,to kitashi ki raka Abdallah zai tafi ,Afanan ce tace "to dady, mayafinta ta ɗauka ta fice samunsa tayi a gaban motarsa a tsaye da alamu ita yake jira , ganinta yasashi faɗaɗa fara'arsa yace "gimbiya barka da fitowa , mumishi Afnan tayi tace "sannu ba wata hira sukayi mai tsayi ba yace "zai tafi aiyuka sunyi masa yawa amma zuwa gobe zai dawo , buɗe mota yayi ya ciro kuɗi masu yawa ƴan ɗari biyar biyar ya miƙa mata , ƙin karɓa tayi tace ..✍️.

KUYI HAƘURI PAGE ƊIN BABU YAWA

LAMARIN K'ADDARAR AURE NAWhere stories live. Discover now