💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍
*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦_Story and writing by_
_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_My wattpad momislam2020
My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2Zainabhabibu713 gmail.com
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comhttps://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ
*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
EPISODE 19 &20
Kwanan su biyu basuga juna ba dama shi ba memanta yakeyi ba , a ranar na ukun ne ya shigo da safe yayi wanka yasha bugagiyar shadda sai sheƙi takeyi , Maimunatu najin alamun tafiyar mutum ta miƙe da gudu daga kwanciyar da tayi , to sai kuma ina ?"ta tambayeshi tana girgiza kwan kwaso , sai gidanku ko kinada ja ne ? a'a tace "to ai naga gidan namun ma bakaje ba da kake gayamin baƙar magana , shidai Haisam gani yakeyi yanzu kam kamar an maƙala masa jaraba ne dan yarinyar bata neman kwanciyar hankali kwata kwata , bai ƙarasa shiga ɗakin ba ya yi ficewarsa waje , kan uba inama tsaye har ya wuce ya barni kan uba wlh wanan ɗan taurin kan zanyi magzninsa , barin zo in kira umma taje min gurin boka ko da akwai maganin da zai ragemin wanan rainin haba fitina har ina ?".
Yau ne Afnan ta gama idda ,Abdallah yayi maganar aure , dady ne yace "ka tambayi Afnan ɗin inhar ta 'amince to babu matsala ,kwana biyu tsakani momy tasa aka shiga yiwa Afnan dilka saboda ta ƙara kyau inda zata gigita samari , yanzu idon Afnan yafi dz buɗewa nesa ba kusa ba , ƙarar wayarta ce tasata duba mai kiran , Abdallah ne ,dama yama sani anshafe labarin ɗaukar wayarshi intai ring sai ɗaya ,dole sai tayi sau biyu, aslm mijina katseta yayi da gani a palo dan Allah ki fito yanzu , gyalenta ta ɗaukz tare da ƙara feshe jikinta da humra , isa gurinshi tayi da sallama tace "ranka shida ɗe barka da isowa , ywa gimbiya komai naki birgeni yakeyi dariya tayi masa mai haɗe da fari da ido tace "kaima ai hakanne ,gyara zamanshi yayi yace "kinsan me ? a'a Afnan tace sai ka faɗa , inason a kawo sadaki ne kin amince manya su shiga tsakani ? murmishi tayi tace "haba honey nama ɗauka wata maganar ce nikam tun yaushe na amince karka damu , kai amma godiya nake sosai cewar Abdallah inason komai kar ya ɗauki lokaci nafison in ga amaryata a gidana , dariya Afnan tayi tace "ai ka sameni ma tun yaushe."
Yau duk rabi hirar tasu ta lamari auran ne , Afnan ji takeyi kamar yanzu ne zatayi sabon aure , wani nishaɗi takeji , momy ma sai daɗa zugata takeyi, ana kuma gyarata tun ba'a kawo sadakin ba ma bare ayi maganar aure , yau kwanan Abdallah uku bai zo ba kasancewar ya gayawa Afnan cewar zaiyi tafiya , a yau iyayensa sukazo nema masa auran Afnan tare da dukiyar aure , dubu ɗari da hamsin suka zube gaban su dady , dan su biyu ne shida abokinsa , fatan alkairi sukayi kana sukayi musu sallama , Abdallah na Ibadan yaje gurin wani kaya nashi da aka kawo , sana'ar kayan sawa yakeyi kama daga takalma na mata harma na maza shaddoji da atamfofi da sarƙa da ɗan kunne duk dai , kuɗi a gurinshi ba'a magana , duk kuɗin dadyn Afnan to Abdallah yasha gabansa ."
BAYAN SATI UKU .
Yau kwanan sa ɗaya rabonsa da gidan dan yanzu sai yayi ra'ayi yake shigowa , Maimunatu na kwance zazzaɓi ya rufeta ta koma abin tausayi , jin alamun shigowar mutum yasata daddafa bango ta fito , ganin Haisam zaune da ƴar laptop ɗinsa a gabansa yana sarafata yasata zama gefen shi , ɗago kai yayi ya galla mata harara yace "wane irin iskanci ne zakizo ki zauna min dalla tashi jiki duk tsami , dariyar yaƙe tayi kana tace "ka temaka ka kaini asibiti , kallon kinma rainani yayi mata ya maida hankalinsa ga abinda ke gabansa , kuka tafara shaɓe shaɓe ta miƙe jiri na ɗibarta ta tsuguna a fabansa tace "dan darajar iyayenka dan Allah ka temakeni zan mutu , shi dariya ma tabashi , gani yakeyi kamar langwai take yimasa yace "inna fice naga wanda zaki laƙewa kauce dallah ,haka ya fice ya barta a gurin wani gagarumin amai ne ya taso mata ba shiri tadinga kwarara shi kamar zata amayar da hanjin cikinta , nunfashinta sama sama ta ɗauki ruwan dake kusa da ita a tebur ta sha ai kamar ta kuma kiran aman tacigaba , tashin zuciya ya takura mata wanan wace irin rayuwace ?" cewar Maimunatu jiri na ɗibarta ta ɗauko tsumman rigarta ta naɗe aman ta koma ɗaki bawai dan gurin ya gogu ba sbda wari ma gurin ya ɗauka amma haka ta koma ɗaki ,
TA ɗauki wayarta ta danna lambar mahaifiyarta , cikin sa'a ta ɗaga tare da cewa"Maimuna lafiyarki kuwa ?"naji muryarki wata iri kamar mara lafiya ,cikin ƙarfin hali Maimunatu tace "umma banida lafiya kamar zan mutu ga Haisam ɗin yaƙi kulani , to meye yake damunki cewar umma?"wlh amai ne da zazzaɓi gakuma tashin zuciya ,Alhmdulilah ƴar albarka kinyi ƙoƙari kin haifu Allah ya inganta shiɗin waye da zaiƙi kulaki lallai ma , bari yanzu zan fita gidan barka daganan zan wuce gurin wani malami da aka yimin kwatancensa jiya kwantar da hankalinki zakisha gata shiɗin banza ma , kashe wayar umma tayi zuciyarta fal farinciki yo aisu kakarsu ta yanke saƙa."
Anty Aisha ce ta zauka a gidan misalin ƙarfe huɗu na yamma kai tsaye ɗakin yayan nata ta wuce, yana ganinta ya washe haƙora tare da cewa dama so nakeyi in kiraki a waya yanzu to sai gaki kin iso , sassuta murya Anty tayi kamar munafuka tace "ai gani dama zmfanin ɗan uwa kenan yanzu mai yafaru Alhaji ?"dady ne yace "akan maganar auran Afnan ne, riƙe baki anty tayi tace "yanzu gidan matsiyacin zaka maidata?"a haba ni na isa ai wani sabo Allah ya kawo mata shi wancan ai harya bata takardar ta tun yaushe hidindimun bikinne dai ankawo sadaki ankuma sa rana wata biyu me dame kike ganin ya kamata a siyo banason wancan kayan ɗakin nata so nakeyi a canza mata masu tsadar gaske , cikin fara'a anty tace "dama abinda zance kenan to suɗin wa za'a bawa naga basuyi komai ba , dady ne yace "wa nakeda shi bayan ke kece zaki kwashe ,ai da sauri anty ta sunkuyar da kai tana zubowa Alhaji godiya."Alhaji ne yace "ai ba komai yanzu nawa ne kike ganin zai isa kokuma tare zamuje kasuwar , ai kam dayafi Alhaji ita kuma uwar tata sai ka bata kuɗin siyan kayayyakin abinci kuttt hmmm...
Kumafa kin kawo shawara barinje banki in dawo zuwa gobe sai mu tafi , yana ficewa anty ta wuce saɗaf saɗaf ta fice dan batason su haɗa ido da kowa, tana fita bakin get tayi hamdala da tari abin hawa ta fice , kai tsaye dady ɗakin momy ya wuce , samunta yayi ita da Afnan suna duba wasu turaruka da aka kawo musu daga saudiya, zama dady yayi yace "biki nata ƙaratowa harkun fara shirye shirye ne ?momy ce ta kashewa dady ido ɗaya tace "turarukan Afnan ne ƙawata da zata dawo daga saudiya nabata sautu to shine ta kawomin , kuɗinsu dubu ɗari uku , ok babh matsala amma sai naje bank dan yanzu babu kuɗi a hanuna masu yawwa....✍️.Follow me and vote on wattpad