Chapter 35 & 36

22 3 0
                                    

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
     💍      💍       💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE  NA!!!* .

      💍     💍       💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
   (mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA   SHUGABA*

*(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)*

*ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA*

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

EPISODE 35 & 36

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

    Washe gari safiyar litinin (monday) Maimunatu ta tashi da wani matsanancin ciwon mara da baya , jin shiru har ƙarfe takwas bata fito ba yasa mama nufar ɗakin , jiyo nishin Maimunatu yasa hankalinta mugun tashi ta shigo a guje , ganinta tayi durƙushe tanata juyi idanunta sunyi ja , subhannallah mama tace " tare da kamo mai munatu ta gyara mata tsuguno , yau kam babu magana kuma bata yiwa mama musu , ganin abin ya wuce tunani gashi dai alamun  aihuwar ce amma har yanzu shiru , sake Maimunatu tayi ta wuce ɗakin Haisam dake bacci ..

    Bugun ƙofar takeyi tana ƙwala masa kira , a tsorace ya taso ya buɗe ƙofar yace "lafiya mama?" inafa lafiya maza fito kazo ka ɗauko mashin ɗinka muje asibiti wanan yarinyar inaga aihuwa ce , ai dajin tace aihuwa ce yasashi azamar sauya kaya ya fito da sauri mama ta kwaso kayan yaro , kasancewar ba zaman daɗi sukeyi dashi ba amma yana siyo kayan jarirai , kai tsaye suka nufi asibiti ,da isarsu aka wuce ,da Maimunatu ɗakin aihuwa ..

   Mama da Haisam sun zuba tagumi kawai jira suke suji ance ta aihu ,

  Ɓangaren Maimunatu likitoci ne zagaye a kanta sunata aiki ,itako batasan inda kanta yake ba ,adu'a sukeyi duk wacce ta faɗo musu amma kaf ɗinsu hankalinsu ya fara tashi , tun ƙarfe tara na safe gashi yanzu ƙarfe biyar na yamma , wata likita ce ta fito fuska babu walwala ganin hakan yasa mama miƙewa da sauri Haisam da bai san ko mai ke faruwa shima ya miƙe , hango likitar yayi ta doso gurin su ...

   Tun a zuciyarsa yafara mai maita innalilahi haka mama itama , likitar ce tace "waye mijin Maimunatu a nan ko kai ne ? ta nuna Haisam ,cikin tashin hankali yace " nine ok "kazo office munason ganinka , to Haisam yace "jin ba abinda yake tunani bane yasashi sakin fuskarsa ,

    Da sallama ya shiga ya nemi guri ya zauna likitar da tazo ta kirashi ne takuma cewa malam muna mai baka haƙuri akan rashin matarka , a razane Haisam ya miƙe daga zaman da yayi yace " ban gane ba ?".

   Kina nufin Maimunatu ce ta rasu ? wani doctor dake gefe tunda Haisam ya shigo bai ce komai ba yace " abokina kayi  haƙuri kulli nafsin za'ikatull maut kayi haƙuri adu'arka take buƙata ..

    Da zamuyi maka magana kasa hannu ayi mata aiki to muna tunanin aihuwar da saura   amma Allah da kansa ya ƙarɓi abarsa ."

Mama jin Haisam shiru bai dawo ba yasata neman gurin zama amma tanajin yawan faɗuwar gaba , hangoshi tayi yana share hawaye kamar ƙaramin yaro , a saninta Haisam bai cika zubar da hawaye ba inba babban abu ne ya faru ba , lallai akwai abinda ya faru mama ta faɗa a fili ".

     Yana isowa gurinta yace " mama ta mutu !!zaro ido mama tayi tanajin abin kamar a mafarki ƙarya kakeyi Haisam ,waye ya mutu ?Maimunatu ya bata amsa innalilahi ta bazama cikin asibitin da gudu , binta Haisam yayi yana ƙwala mata kira amma ina sai da tayi ɗakin da gawar Maimunatu take ta bude gawar da aka lulluɓeta da farin mayafi , salati ta dinga rafkawa tana surutai marasa amfani ..

  Ashe tafiya zakiyi kintafi da ciki , tsayawa Haisam yayi a bakin ƙofa idanunsa cike da hawaye yana share wa wani na biyo baya , haka likitocin suka shigo suka samesu suma sun tausaya musu amma dayake lamarin na Allah ne da yafi kowa so ya karɓi abinsa suka cigaba da yiwa su Haisam nasih.

   Haka 'asibitin suka bada mota aka sa gawar Maimunatu  suka nufi gida , tun a hanya Haisam yafara sanar da ƴan uwansu dana Maimunatu , mahaifiyarta ko kuka tasa tana ihu ,

   Kafin su ƙaraso an ɓalle ƙofar gidan mutanen kusa sunata shigowa , da shigarsu aka wuce ta gawar ɗakinta aka ɗibi ruwan ɗumi aka yimata wanka aka karɓo likafani a masallaci , aka suturce ta, kasancewar iyayenta duk sunzo ana fito da gawar ta mahaifiyarta ta miƙe tana ihu wani malami  ne ya fara yimata wa'azi  da ban haƙuri  , kuka kam ansha haka aka kaita makwancin ta rai kenan baƙon duniya.

Gida ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi mama kam hauka ne batayi ba amma tadingi kuka sosai ga cikin babu tadinga mai maitawa a cikinzuciyarta...✍️.

Follow me on wattpad momislam2020

LAMARIN K'ADDARAR AURE NAWhere stories live. Discover now